BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
KAI TSAYE, Kotu ta soke takarar gwamna da Pantami ke yi a Gombe
Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 24/09/2026
Zazzafan martani da shugaban Iran ya yi wa Amurka a taron UNGA
Ya kuma jaddada cewa duk wata yarjejeniya da za a yi dole ta ƙunshi kawo ƙarshen shingen da Amurka ta ƙaƙaba wa jiragen ruwa da tashoshin jiragen ruwa na Iran.
Me wasiƙar da El-Rufai ya rubuta wa abokansa ta ƙunsa?
Sai dai tsohon gwamnan bai ambaci sunayen mutanen da yake magana a game da su ba, inda ya bayyana abin da ya faru a matsayin darasin rayuwa.
Hukumomin gwamnati 5 da suka fi tasiri a tsarin zaɓen Najeriya
A Najeriya, gudanar da ingantaccen zaɓe ba aiki ne da ya rataya a wuyan hukuma guda ɗaya ba, domin akwai hukumomi da dama da ke haɗa ƙarfi da ƙarfe don tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zaɓe cikin lumana da adalci.
Hanyoyi 5 da ake gane bunƙasa ko raguwar ƙarfin tattalin arziƙin Najeriya
Babban Bankin Najeriya ne ya bayyana hakan, inda ya ce ayanzu dai matsin lambar da ake fuskanta a ƙasar a kasuwar canjin kuɗaɗen waje ya ragu matuƙa, yayin da ajiyar kuɗin waje ta ƙasar ta ƙaru zuwa dala biliyan 55.25.
Ta yaya Saudiyya za ta kare Makka da Madina daga hare-hare?
Ma'aikatar Tsaron Saudiyya ta ce rundunar kariyar sararin samaniya da ke amfani da waɗannan makamai na da alhakin "kare wurare masu tsarki da kuma dakile barazanar hare-haren sama da ka iya kai musu."
Shugaban Iran ya yi kausasan kalamai ga Amurka a taron UNGA
Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 23/09/2026
Xi Jinping: Ɗan sarauta da ya rasa komai amma ya zama shugaban China mafi ƙarfi
Iyalan Xi Jinping sun sha wahala sosai a lokacin Juyin Juya Hali , wani yaƙin neman sauyi da ya faru a China tsakanin shekarun 1966 zuwa 1976.
Hanyoyi 4 da za ku gane gidan mai na matse litar fetur
Masu sayen da man fetur na yawan kokawa kan yiwuwar wasu gidajen mai na ba su adadin man da bai kai wanda suka biya kuɗinsa ba, ta hanyar matse lita.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Yamma, 19:29, 24 Satumba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurara Kai Tsaye, Shirin Rana, 13:59, 24 Satumba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 24 Satumba 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 24 Satumba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
Barcelona ta fasa ɗaukar Alvarez, Liverpool ba zata siyar da Wirtz ba
Barcelona ta fasa siyen Alvarez daga Atletico Madrid, yayin da Liverpool kuma ta fasa siyar da Wirtz, inda kuma Chelsea ke harin ƴan wasan Ingila biyu, da ƙarin wasu labaran.
United da Liverpool na harin Mitchell, Munich na son Gibbs-White
Manchester United da Liverpool na zawarcin ɗan wasan Crystal Palace Tyrick Mitchell, yayin da ƙungiyoyi da ke buga La Liga masu yawa na sa ido kan ɗan wasan Aston Villa Alejandro Garnacho, inda ita kuma Bayern Munich ke harin Morgan Gibbs-White, da ƙarin wasu labaran.
KAI TSAYE, Mbappé ya bayyana yadda ya kusa komawa Liverpool a 2017
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 20 zuwa 26 ga watan Satumbar 2026.
Jarumta da tarihin Ebola a fagen damben gargajiya
Abdurrazak Ebola daya ne daga fitattun yan damben gargajiya da ya yi fice a fadin duniya. Mohammed Abdu ya hada rahoto kan rayuwarsa da dalinlin da aka sa masa suna Eboda da jarumtar da ya yi a fagen wasan.
Liverpool na harin Read, yayin da Gabriel ke son barin United
Liverpool na masata kaimi wajen daukar dan wasan Feyenoord Givairo Read, JJ Gabriel ya fidda rai da ci gaban da zama a Manchester United da batun komawarsa Newcastle. da karin wasu labaran.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Ko Mbappe zai iya lashe Ballon d'Or ba tare da kofi ba?
Shin Mbappe zai iya lashe Ballon d'Or ba tare da ya ɗauki kofi ba? Ga labarin da Mohammed Abdu ya haɗa kan dokokin zaɓe da ƴan takara 30 na 2026.
Barazana 5 da Trump ya yi wa Iran a taron Majalisar Dinkin Duniya
A yayin jawabin Trump a Majalisar Ɗinkin Duniya, mutum ɗaya kacal daga tawagar Iran ne ya zauna yana sauraron abin da shugaban Amurka ke faɗa.
Fitattun Sha'irai 5 da ke tashe a TikTok
Galibinsu matasa ne waɗanda shekarunsu ba su wuce tsakanin 20 zuwa 30 ba, kuma sun shiga zuciyar mutan da dama a faɗin duniya, ciki har da yan arewacin Najeriya da ma 'yan kudancin ƙasar.
Me ya sa tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu ke ziyartar malaman addini?
A baya-bayan nan tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu ƙarƙashin jagorancin babban daraktan kwamitin Sanata Abdul'aziz Yari ya ziyarci Sheikh Sani Yahya Jingir da Sheikh Bala Lau da Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi da kuma Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara.
Su wane ne masu tsaron shugaban Rasha Vladmir Putin?
Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ziyarci Indiya domin halartar taron koli na ƙasashen BRICS karo na 18, wanda aka gudanar a cibiyar taro ta Bharat Mandapam da ke New Delhi a ranakun 12 da 13 ga Satumba.
Iran ta ce ta ƙarfafa sabon shirinta na yaƙi
Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 22/09/2026
Abubuwa 7 da aka haramta wa ƴansanda game da siyasa
Masana na cewa ko da ba a ba da umarni kai tsaye ba, wasu halaye da matakan da jami'ai ke ɗauka kan iya haifar da zargin nuna son kai da ɓangaranci.
Mutumin da ya yi kwanaki 555 ba tare da zuciya a jikinsa ba
A wannan lokaci, zuciyarsa ta daina aiki kuma an cire ta yayin da yake jiran a samu masa zuciyar da za a dasa masa.
Wane ne ke jagorantar Najeriya idan Tinubu da Shettima ba sa nan?
Masu sukar shugaban ƙasar na cewa domin martaba sashe na 145 na kundin tsarin mulki ya kamata shugaban ƙasa idan zai je hutu ya miƙa riƙon mulki a hukumance ga mataimakinsa.
Abin da ya jawo aka sanya dokar hana fita a wasu yankunan Filato
Gwamnatin jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, ta sanya dokar hana fita daga magariba zuwa wayewar gari a ƙananan hukumomi uku na jihar
'Fitsari da gumi muka riƙa sha a inda aka tsare mu a Neja'
Mutane biyu da suka tsallake rijiya da baya bayan tsare su a jihar Neja da ke Najeriya sun shaida wa BBC cewa sun rika shan fitsarinsu da kuma zufarsu domin su rayu bayan ƙishirwa mai tsanani ta addabe su a wani ƙaramin ɗaki da aka tsare ɗimbin mutanen da ake zargin masu haƙar ma'adinai ne ba bisa ƙa'ida ba.
Abu 5 da za su sa a zarge ku da taimaka wa ƴanbindiga
Yayin da ake ci gaba da fama da matsalar tsaro a sassa daban-daban na Najeriya, wasu mutane na faɗawa tarkon ƴan bindiga, ko ƴan ta'adda da sauran masu aikata laifuka ba tare da sanin hakan ba.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































