Dars Hausa: BBC ta ƙaddamar da shirin ilmantar da yaran da ba sa zuwa makaranta

BBC ta ƙaddamar da Dars a harshen Hausa yayin da shirin ilmantar da yara ya cimma gagarumar nasarar gabatar da darussa 700
BBC World Service ta ƙaddamar da shirin ilimantarwa mai suna Dars a harshen Hausa domin gabatar da darrussa ga yara a sassan yammacin Afrika.
Yanzu Hausa ta zama ta biyar, baya ga harsunan Dari da Pashto da Larabci da Nepali da ke gabatar da darussan.
Shirin Dars Hausa zai riƙa gabatar da darussan Inglishi da lissafi da kimiyya tare da shawarwari kan lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma labarai masu ƙarfafa gwiwa.
Zuwa yanzu, shirin Dars ya gabatar da darussa sama da 700 ga yaran da ke matuƙar buƙatar ilimi sakamakon rikici da ya raba su da gidajensu, dalilan da suka hana su zuwa makaranta.
Waɗanne fannoni za a riƙa koyarwa?
A cikin darussan Dars, an koyar da fannoni da dama da suka haɗa da yadda za a tunkari bala'o'i da sanin ilimin ƙasa da tarihi da ilimin ƙirƙirarriyar basira ta AI da kuma hanyoyin bayar da agajin gaggawa.
An fara ƙaddamar da Dars, wanda ke nufin 'Darasi' a Afghanistan a shekarar 2023, a harsunan Dari da Pashto domin ba yaran ƙasar da ba sa iya zuwa makaranta damar samun ilimi.
Tun 2021, ƙungiyar Taliban ta haramta wa 'yan mata zuwa makarantun boko na sakandare a Afghanistan.
Tun bayan ƙaddamar da shirin, an kalli darussan Dars fiye da sau miliyan 14.5 a shafukan sada zumunta na sashen BBC Dari da Persian da BBC Pashto, da suka ƙunshi YouTube da Facebook da Instagram.
Ana kuma gabatar da shirin a talabijin da rediyo, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen isar da darussan ga waɗannan yaran.
A Fabrairun 2025, sashen BBC na Larabci ya ƙaddamar da Dars Arabic, domin taimaka wa yara a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afrika samun ilimi.
Tun ƙaddamar da shirin, an kalli darussan Dars Arabic fiye da sau miliyan 5.5 a shafukan BBC Arabic na intanet.
An kuma gabatar da shirin Dars a matsayin wani ɓangare na Nepali Lifeline tun daga Oktoban 2026 domin tallafa wa al'ummomin da mummunar ambaliyar ruwa ta shafa a tsakiyar Nepal.
Me ya sa BBC ta ɓullo da shirin ga Hausawa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bisa nasarorin da shirin Dars ya samu, BBC ta ga dacewar ƙaddamar da Dars Hausa, a matsayin wata damar samun ilimi ga yara a Najeriya da ba sa samun damar zuwa makaranta.
Sashen Hausa na BBC ne zai riƙa shirya shirin Dars daga ofishin BBC da ke Abuja.
Najeriya na fuskantar babban ƙalubalen ilimi kamar yadda Hukumar UNESCO ta bayyana.
Yawancin yaran da ba sa zuwa makaranta sun fito ne daga arewacin Najeriya, inda hare-hare kan makarantu da satar ɗalibai suka zama ruwan dare.
Dars ya yi tasiri matuƙa ga matasa a duniya da ba su da damar zuwa makaranta.
Sadaf, ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana da shirin Dars a Afghanistan, ta ce: "Ina da shekara 13, kuma ina aji shida a firamare lokacin da Taliban ta sake ƙwace mulki. Bayan dawowarsu, an hana mu zuwa makaranta. Na shiga wani mawuyacin hali. Na shiga damuwa da baƙin ciki, har na fara fargaba game da makomata. An rusa duk wani tsarin da na yi na rayuwata."
"Ina kallon darussan Dars a shafukan sada zumunta da YouTube. Baya ga koyon Inglishi wanda ya sauƙaƙa min fahimtar sabbin bayanai kan kimiyya a harshen. Na kuma ji daɗin darussan da suka shafi lafiyar ƙwaƙwalwa da shawarwari kan tunkarar bala'o'i da kuma yadda ake amfani da fasahar zamani."
"Lokacin da na kalli bidiyon shirin Dars kan yadda ake ba da agajin gaggawa, sai na yanke shawarar cewa ina son zama likita wata rana... Wannan shiri ba wai darussa kaɗai yake koyarwa ba, yana ba mu ƙwarin gwiwa da ƙarfin gwiwar cewar za mu iya ci gaba da samun ilimi da ƙoƙarin gina makomarmu."
Yaushe za a riƙa gabatar da shirin?
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana shirin a matsayin wata muhimmiyar hanyar da ke taimaka wa yaran Afghanistan ci gaba da samun ilimi.
Domin bikin ƙaddamar da Dars Hausa, BBC ta fitar da wani gajeren fim mai suna 'Three Girls: Lessons in Limbo', wanda ya fito da tasirin ƴanbindiga da auren wuri da kuma yadda talauci ke shafar ilimin 'yan mata a arewacin Najeriya.
Za a riƙa gabatar da shirin Dars Hausa a radio a shirin safe na BBC Hausa a duk ranar Lahadi da misalin ƙarfe 5:45 agogon GMT, (6:45 agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi ).
Sannan a maimaita shi a shirin dare da ƙarfe 7:45 na yamma agogon GMT, (8:45 agogon Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru) Za a iya kallon shirin a shafukan intanet na BBC Hausa da suka kunshi YouTube da za a kalli cikakken shirin da kuma a Facebook da X da Instagram.


























