Arsenal na zawarcin Nusa, Chelsea na son ɗaukar Morante daga Betis

Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran RB Leipzig za ta nemi Yuro miliyan 80 (fam miliyan 66) kan ɗan wasan Norway mai shekara 21, Antonio Nusa, yayin da Arsenal ke shirin gabatar da tayin sayensa a watan Janairu. (Teamtalk)
Real Betis ta yi watsi da tayin da Chelsea ta gabatar na sayen ɗan wasan gaba ɗan ƙasar Spain mai shekara 19, Jose Antonio Morante. (ABC Sevilla)
Ɗan wasan tsakiya na Paris St-Germain kuma ɗan ƙasar Spain, Fabian Ruiz, mai shekara 30, na son kammala aikinsa na ƙwallon ƙafa a ƙungiyar da ya fara bugawa, wato Real Betis. (Diario Sport)
Ɗan wasan gaba na Bournemouth ɗan ƙasar Brazil, Rayan, ya bayyana cewa tun da daɗewa yake goyon bayan Manchester United; ƙungiyar ta Old Trafford ta taɓa nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan mai shekara 20 kafin ya koma Bournemouth daga Vasco da Gama a watan Janairu. (ESPN Brasil)
Ƙungiyar Coventry City na fargabar cewa za a iya samun ruɗani a ƙungiyar idan ɗan wasan tsakiya Jack Rudoni, mai shekara 25, ya bar ƙungiyar a sabuwar shekara, duba da cewa ƙungiyoyin Newcastle da Leeds United na nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan na Ingila. (Football Insider)
Ɗan wasan tsakiya na Belgium, Kevin de Bruyne, mai shekara 35, na da sha'awar barin Napoli domin komawa ƙasarsa ta asali, a cewar bayanan da matarsa Michelle ta bayar. (Mirror)
Everton na fafatawa da Nottingham Forest don ɗaukar ɗan wasan baya na ƙungiyar Gremio ta Brazil, Gustavo Martins, mai shekara 24, wanda darajarsa ta kai tsakanin Yuro miliyan 12 zuwa 15 (fam miliyan 10 zuwa 12.5). (Fussball Europa)





















