Sabbin matakai 5 da Tinubu zai ɗauka don yaƙi da matsalar tsaro

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da ɗaukar ƙarin sojoji 28,000 da jami'an 'yan sanda 50,000 a wani bangare na sabon shirin da take yi na yaƙi da matsalar tsaro a Najeriya.
Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaben shugaban ƙasa na jam'iyyar APCn, Dele Alake, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamban 2026.
Ya ce matakan na cikin wani shirin samar da tsaro na shekaru biyar da Shugaba Tinubu ya amince da shi, domin ƙarfafa rundunonin tsaron kasar da inganta yadda suke tunkarar matsalolin ta'addanci, da fashi da makami, da garkuwa da mutane da sauran laifuka.
Sanarwar ta ce shirin zai mayar da hankali kan matakai biyar da suka hada da:
1. Ƙara yawan jami'an tsaro da faɗaɗa sansanonin soji
Mataki na farko shi ne ƙara yawan jami'an tsaro ta hanyar daukar karin sojoji 28,000 da 'yan sanda 50,000.
Haka kuma, gwamnatin ta samar da sabbin rundunonin sojoji guda huɗu tare da sake fasalin wasu rundunonin da ake da su, domin fadada ayyukan soji da bai wa dakarun damar kai dauki cikin gaggawa a wuraren da ake fama da matsalar tsaro.
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya kuma amince da gina ƙarin cibiyoyin horas da sojoji guda biyu a Osogbo, da ke jihar Osun, da kuma Amasiri-Edda a jihar Ebonyi.
An ce kowace cibiyar tana da damar horas da sababbin sojoji 6,000 a lokaci guda, wanda hakan zai sa a rika horas da sojoji 12,000 a cibiyoyin biyu.
2. Ƙarfafa tattara bayanan sirri da sa ido kan ayyukan masu aikata laifuka
Mataki na biyu shi ne inganta tattara bayanan sirri da amfani da fasaha wajen gano barazanar tsaro tun kafin ta faru.
Gwamnatin ta ce shirin zai samar da ingantacciyar hanyar haɗa bayanai tsakanin hukumomin tsaro, tare da tabbatar da cewa ana amfani da bayanan da aka tattara wajen tsara ayyukan soji da daukar matakan da suka dace.
Wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnatin na sauya tsarin yaki da rashin tsaro zuwa wanda ya fi dogaro da bayanan sirri, sa ido da kuma dakile barazana tun kafin ta rikide zuwa babbar matsala.
3. Inganta hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro
Mataki na uku shi ne kara daidaita ayyukan rundunonin soji da sauran hukumomin tsaro domin kauce wa rashin fahimta da matsalolin rashin musayar bayanai.
Sanarwar ta ce shirin zai samar da tsarin da zai bai wa hukumomin tsaro damar hada karfi da karfe wajen tunkarar matsalolin ta'addanci, da 'yan bindiga, da masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka.
4. Inganta horo, kayan aiki da walwalar jami'an tsaro
Mataki na hudu shi ne karfafa karfin rundunonin tsaro ta fuskar horaswa, da samar da kayan aiki da inganta yanayin aikin jami'an tsaro.
Gwamnatin ta ce tana kuma zuba jari wajen gina muhallan zama na sojoji da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa da za su taimaka wajen inganta aikinsu.
Daya daga cikin irin wadannan ayyuka shi ne gina barikin sojoji mai gidaje 700 a Ikere-Ekiti, da ke jihar Ekiti.
A cewar sanarwar, wannan mataki zai taimaka wajen samar wa jami'an tsaro yanayin zama da aiki mai kyau, tare da inganta karfin rundunonin wajen gudanar da ayyukansu.
5. Daidaita kashe kudaden tsaro da bukatun kasa
Mataki na biyar shi ne tabbatar da cewa ana amfani da kudaden da ake warewa bangaren tsaro bisa bukatun da ake da su da kuma barazanar da kasar ke fuskanta.
Sanarwar ta ce shirin zai taimaka wajen gano gibin da ake da shi a bangaren tsaro, tantance kayan aikin da ake bukata da kuma tabbatar da cewa ana amfani da kudaden yadda ya kamata ba tare da almubazzaranci ba.
Ya masana tsaro ke kallon shirin?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar Dr Kabiru Adamu, masanin harkokin tsaro a Najeriya, wannan ne karon farko da aka tsara wani cikakken shiri irin wannan, wanda ya fayyace matakan da za a bi wajen magance matsalar rashin tsaro da kuma yadda za a aiwatar da su dalla-dalla.
Ya ce an tsara shirin ne domin ya zama taswirar da za a bi wajen yaki da matsalar tsaro a Najeriya cikin shekaru biyar masu zuwa.
Ya ƙara da cewa: "Wannan shiri zai zama ma'aunin da za a rika amfani da shi wajen tantance kokarin da ake yi na magance matsalar tsaro. Za a iya duba shi a kowane lokaci domin a tantance ko an samu ci gaba ko ba a samu ba."
Sai dai wani abin da ke janyo tambayoyi shi ne cewa Shugaba Tinubu zai sake neman wa'adin mulki a zaɓen da ke tafe, kuma ba a san ko zai ci gaba da mulki ba. Wannan ya sa wasu ke nuna shakku kan yadda za a ci gaba da aiwatar da shirin da kuma makomarsa idan aka samu sauyin gwamnati.
Sai dai Dr Adamu ya ce shirin bai kamata ya tsaya ga gwamnatin Tinubu kawai ba, domin duk wanda ya karɓi ragamar mulkin Najeriya a nan gaba ya kamata ya ɗauke shi a matsayin wani muhimmin tsarin da ya dace a ci gaba da aiwatarwa, har sai an shawo kan matsalar rashin tsaro a ƙasar.


























