An ƙara tsaurara tsaro a faɗin Bangladesh

Asalin hoton, Badhon Sheikh
An kara tsaurara matakan tsaro a Bangladesh yayin da hukumomi ke shirin tunkarar zanga-zangar kasa baki daya da magoya bayan haramtacciyar jam'iyyar Awami League ta tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina suka kira za a gudanar a ranar Alhamis.
Sheikh Hasina ta tsere zuwa makwabciyar kasar Indiya a watan Agustan shekarar 2024, amma ta sha alwashin komawa gida a wata mai zuwa, duk da cewa tana fuskantar hukuncin kisa. Gwamnatin kasar ta kuma yi watsi da bukatarta ta neman sabon fasfo da katin shaida.
A kwanakin baya-bayan nan, an samu karuwar tashe-tashen hankula, inda aka samu fashewar bama-bamai na gida da kuma kona ababen hawa da dama a fadin kasar.
A garin Gopalganj, mahaifar Sheikh Hasina, 'yan sanda sun ce wani ɗan gwagwarmayar jam'iyya mai mulki ta Bangladesh Nationalist Party (BNP), mai suna Raju Mollah, ya mutu sakamakon harin bam ɗin fetur

























