Sama da mutum 5,500 sun mutu tun bayan ɓarkewar cutar Ebola a Kongo

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin lafiya a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar Ebola a asibitocin killacewa da jinya ya fi waɗanda suka mutu a gidajensu cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
Ƙididdigar da ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta fitar, wadda ta kai zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba, ta nuna cewa mutum 22 sun mutu a cibiyoyin jinya, yayin da mutum 14 suka mutu a gidajensu.
Masana harkokin lafiyar jama'a sun ce wannan na iya nuna cewa mutane da dama na kai marasa lafiya cibiyoyin killacewa da jinya. Sai dai wasu daga cikinsu na zuwa ne a cikin mawuyacin hali, ta yadda ba sa iya amfana sosai da jinyar da ake ba su.
Jinyar marasa lafiya a cibiyoyin musamman na kuma rage haɗarin yaɗuwar cutar ga 'yan uwansu ta hanyar taɓa su kai tsaye.
Ma'aikatar ta tabbatar da samun sabbin mutane 60 da suka kamu da nau'in cutar Ebola mai suna Bundibugyo, galibinsu a lardunan Ituri da North Kivu da ke gabashin ƙasar.
Tun bayan sanar da barkewar cutar a ranar 15 ga watan Mayu, sama da mutum 11,300 ne suka kamu da ita, yayin da fiye da 5,500 suka mutu. Sama da mutum 3,000 kuma sun warke kuma an sallame su daga asibiti.
Jami'an lafiya sun ce gano mutanen da suka yi mu'amala da waɗanda suka kamu da cutar na daga cikin manyan ƙalubalen da ke kawo cikas ga ƙoƙarin shawo kan barkewar cutar.
A halin yanzu, ana ƙoƙarin gano sama da mutum 25,000 da aka tabbatar sun yi mu'amala da masu cutar Ebola. Sai dai zuwa ranar 14 ga Nuwamba, an samu nasarar kai wa kusan kashi 83 cikin 100 daga cikinsu.




























