Matsaloli huɗu da zaɓen Najeriya ya fara fuskanta gabanin 2027

Asalin hoton, Facebook
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist Team Manager
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaɓen ƙasar na 2027, ana ƙara fuskantar wasu muhimman matsaloli da za su iya yin tasiri ga yadda zaɓen zai kasance.
Duk da cewa akwai sauran lokaci kafin gudanar da babban zaɓen, muhawarar siyasa da yadda jam'iyyu ke yaƙin neman zaɓe gami da matsalolin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki sun fara nuna yanayin siyasar ƙasar.
Akwai kuma damuwa da ake nunawa kan yadda hukuncin kotu ya shafi wasu manyan ƴantakara a zaɓen na 2027.
BBC ta tuntuɓi masana harkokin siyasa domin jin fashin baƙinsu kan irin matsalolin da aka fara gani tun kafin shekarar zaɓen ta kama.

Asalin hoton, INEC/X
Farfesa Abubakar Kari, masanin harkokin siyasa a jami'ar Abuja ya bayyana cewa matsaloli da dama sun kunno kai gabanin babban zaɓen Najeriya. A cewarsa, matsalolin sun haɗa da;
Rashin tabbas game da takarar waɗansu ƴantakara
Wannan ya janyo ruɗani da kuma zullumi tsakanin ƴantakarar da magoya bayansu da kuma sauran zaɓe. Misali a baya-bayan nan wata kotu ta soke shugabancin David Mark da ya haifar da Atiku Abubakar a matsayin ɗantakarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC. Haka kuma har yanzu, babu sunan ɗantakarar gwamna na jam'iyyar NDC a jihar Kano cikin jerin ƴantakarar da za su fafata a zaɓen.
Hana amfani da wuraren kamfe
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Farfesa Kari ya ce irin wannan ta'annatin da ke faruwa inda ake samun kai wa jam'iyyun siyasa da ƴantakararsu hari, wani abu ne da alhakin faruwarsu zai zama kan ɓangarori da dama. Ya ce "ƴan'adawa suna ta ƙorafi kuma akwai hujjar cewa ana uzzira musu, a duk lokacin da suka so su yi kamfe ana ɗaukan wasu matakai na daƙile samun nasarar kamfe ɗin."
Amfani da kalaman tunzurawa
A cewar Farfesa Kari, wata matsala da ta kunno kai ita ce yadda wasu ke amfani da munanan kalamai a lokacin kamfe.
Hari kan masu kamfe
Farfesa Kari ya ce abin da ya fi kowanne muni shi ne yadda ake kai hari kan tawagar masu kamfe "wanda kusan ya shafi duka jam'iyyu. "A wasu lokutan, har ma rasa rayuka ake, ko kuma a yi [arangama] tsakanin masu kamfe da masu kai musu hari.". Ya ce yaƙin neman zaɓe ya zo da ruɗani da tashin hankali da abubuwa masu ɗaga hankali. "Wata ƙididdiga da aka yi a kan cewa daga lokacin da aka fara kamfe zuwa tsakaniyar makon da ya gabata, an yi abubuwa da suka saɓa wa yarjejeniyar da ƴantakara suka sa hannu har sau 86." in ji Farfesa Kari. Irin wannan harin ya shafi tawagar dan takarar shugaban kasa na NDC a lokacin yakin neman zabe a jihar Cross River. Haka ma an ga irin hakan kan jam’iyyar ADC a jihar Sokoto da Katsina har ta kai ga a jihohi kamar Edo da Plateau, an tuge allon tallata yantakara na bangaren adawa.

Asalin hoton, UGC
Me hakan ke nunawa game da zaɓen?
Farfesa Kari ya ce irin waɗannan matsaloli na nuna abubuwa da dama game da babban zaɓen na 2027 musamman abubuwan tsoratarwa wanda ya alaƙanta da zafin adawa da ake gani tsakanin jam'iyyu.
Ya kuma nuna fargabar cewa irin wannan yanayi da ake gani, muddin aka ci gaba da tafiya a kan haka, zaɓen zai iya zuwa da yanayi na tashin hankali.
"Ana maganar kamar kwanaki 60 ne suka rage a yi wannan zaɓe, sai ga irin matuƙar tashin hankali da abubuwa masu tsoratarwa da razanarwa da suke faruwa. Idan aka ci gaba da haka, waɗannan abubuwa ba za su samar da [wani ci gaba ba]."
Matakan da suka kamata a ɗauka

Asalin hoton, Getty Images
Masanin ya ce idan har ana son daƙile irin wannan lamari daga haifar da wani tasiri ga babban zaɓen na 2027, dole ne masu ruwa da tsaki su ɗauki mataki musamman gwamnati da jami'an tsaro da jam'iyyun siyasa, da ƴantakara da magoya bayansu da mutanen gari.
Ya ce dole ne al'umma su fahimci cewa dimokraɗiyya ƴanci ne kuma ba ta tafiya da tashin hankali da tsoratarwa da razanarwa.
Farfesa Kari ya ce faruwar irin haka na nuna ƙalubale ga jami'an tsaro waɗanda a wasu lokutan ake zargin akwai hannunsu.
"Zuwa yanzu babu rahotanni da suka nuna cewa jami'an tsaro sun kama waɗansu da ake zargi da aikata waɗannan laifuka balle ma a rubuta su" kamar yadda ya faɗa.
Masanin ya jaddada cewa yana da muhimmanci jami'an tsaro su ɗauki matakan da suka dace domin kare rayuka da daƙile hari kan ƴansiyasa.
Ga ƴansiyasa kuwa, masanin ya ce ya kamata su san cewa siyasa ba yaƙi bane ba kuma hauka ba ne, "magana ce kawai ta neman goyon baya saboda haka ba sai sun yi maganganu na tunzura ba, ba sai sun ingiza mutane ko ɗaukar hayar wasu su tayar da hankalin jama'a ba."
Ya kuma ce ya kamata gwamnati musamman kwamitin sasanci tsakanin ƴansiyasa ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasa Abdussalami Abubakar ya sake kiran manyan ƴansiyasa da kuma jam'iyyu su ja musu kunne tare da yi musu gargaɗi da kuma haska musu cewa zuwa yanzu ba sa mutunta alƙawuran da suka ɗauka kan cewa za a yi yaƙin neman zaɓe mai tsafta - a yi lafiya a wanye lafiya.


























