Yadda Iran ta gina babban rumbun makaman linzami a ƙarƙashin ƙasa

Asalin hoton, Noghte Zan
- Marubuci, فرزاد صیفیکاران
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, راستیآزمایی بیبیسی
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Rundunar juyin juya halin Iran, IRGC ta fitar da wasu hotuna a ranar 9 ga Nuwamba, inda ta ce na wani sabon wurin ajiyar makamai masu linzami da ke ƙarƙashin ƙasa mallakin rundunar.
Hotunan sun kuma nuna babban kwamandan sojojin Iran, Ali Abdollahi, da kwamandan rundunar Khatam al-Anbiya, yayin da suke duba wurin tare da Majid Mousavi, kwamandan rundunar sararin samaniya ta IRGC.
Kamar yadda aka gani a wasu irin waɗannan wurare a baya, sabon wurin na ɗauke da nau'o'in makamai masu linzami da kuma na'urorin harba su.
Fitar da hotunan na zuwa ne bayan da aka kai hare-hare masu yawa daga Amurka da Isra'ila kan cibiyoyin Iran masu alaƙa da shirye-shiryen makamai masu linzami, ciki har da sansanonin makamai da wuraren sarrafa su da ƙera su, a lokacin yaƙin da ya ɗauki kwanaki 40.
Duk da waɗannan hare-hare, Iran ta ce har yanzu tana da wani ɓangare na ƙarfin makamanta masu linzami, kuma tana ci gaba da sake gina wasu muhimman cibiyoyinta.
Sai dai har yanzu ba a san ainihin irin ɓarnar da hare-haren suka yi wa ƙarfin makamai masu linzami na Iran ba idan aka kwatanta da yadda suke kafin ɓarkewar yaƙin.
Sashen Tabbatar da Sahihancin Labarai na BBC ya taɓa amfani da hotunan tauraron ɗan'adam wajen nuna cewa Iran na gyarawa tare da gina sabbin cibiyoyi a wasu sansanoninta na makamai masu linzami, ciki har da sansanin Garmdareh da ke birnin Karaj da kuma sansanin Imam Ali da ke lardin Kermanshah.
Shirin Iran na gina wuraren adana makamai masu linzami a ƙarƙashin ƙasa ba sabon abu ba ne, domin ƙasar ta sha nunawa duniya irin waɗannan wurare a cikin 'yan shekarun baya.
Sai dai sabbin sauye-sauyen da aka samu a fagen soja, da kuma lalacewar wasu wuraren da ake ƙerawa da adanawa da harba makamai masu linzami sakamakon hare-hare, sun sa muhimmancin waɗannan cibiyoyin ya ƙaru fiye da kowane lokaci.
Masana na cewa irin waɗannan wurare na ƙarƙashin ƙasa na taimaka wa Iran wajen kare muhimman kadarorinta na soji daga hare-haren sama, tare da bai wa ƙasar damar ci gaba da ajiya da sarrafa makamanta masu linzami ko da a lokacin rikici.
Wannan ne babban rumbun makaman linzamin Iran?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan ne karon farko cikin kusan shekara biyu da Iran ta bayyana wani irin wurin ajiyar makamai masu linzami da take kira "birnin makamai masu linzami" ko rocket city.
Sai dai har yanzu akwai tambayoyi da dama da ba a samu amsarsu ba.
Rundunar IRGC ba ta bayyana inda wannan wuri yake ba, haka kuma ba ta faɗi lokacin da aka gina shi, girman wurin, yawan makaman da ake ajiyewa a ciki ko kuma irin ƙarfin ayyukan soja da yake da shi ba.
Saboda haka, abin da za a iya tabbatarwa kai tsaye a halin yanzu shi ne cewa an fitar da hotunan da ke nuna wani wuri a ƙarƙashin ƙasa tare da wasu makamai masu linzami da kayan aikinsu.
Amma har yanzu ba a tabbatar da iƙirarin da ake yi kan girman wurin, ƙarfin aikinsa, ko ko sabuwar cibiyar makamai ce ba.
A wani bidiyo da IRGC ta fitar, an nuna wurin sau da dama daga cikin wasu hanyoyin ƙarƙashin ƙasa, inda aka ɗauki hotuna daga kusurwoyi daban-daban.
A baya dai an yi hasashen cewa wasu daga cikin wuraren da rundunar ke kira "biranen makamai masu linzami" a zahiri hanyoyin ɓuya ne da ke haɗe da juna a ƙarƙashin ƙasa.
Haka kuma akwai masu zargin cewa wasu sassan tsofaffin wuraren ajiyar makamai da ba a taɓa nunawa a baya ba ne ake sake gabatarwa a matsayin sabbi, domin nuna yawan kayan yaƙinta da ƙarfin soja.
Sai dai masana na cewa lokaci da Iran ta zaɓa wajen fitar da waɗannan hotuna yana da muhimmanci fiye da tambayar ko wurin sabo ne ko ba sabo ba.

Asalin hoton, Noghteh Zan
A baya-bayan nan, cibiyoyin makamai masu linzami na Iran sun kasance cikin waɗanda hare-haren soja suka fi shafa, musamman hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai.
Waɗannan hare-hare ba wai wuraren adanawa da harba makamai kawai suka shafa ba, sun kuma kai ga wasu sassan masana'antar kera makamai masu linzami da kuma cibiyoyin da ke da alaƙa da samar da makamashin da ake amfani da shi wajen sarrafa su.
Masana na ganin cewa saboda irin waɗannan hare-hare, Iran na ƙoƙarin nuna cewa har yanzu tana da damar adanawa, karewa da kuma amfani da makamanta masu linzami duk da matsin lambar da take fuskanta.
Yadda wurin ya tsira daga hare-hare a baya?

Asalin hoton, Noghte Zan
Domin fahimtar muhimmancin sabon wurin ajiyar makaman masu linzamin da Iran ta bayyana, ya zama dole a fara duba halin da shirinta na makamai masu linzami ya tsinci kansa bayan yaƙin kwanaki 40.
Wani bincike da jaridar The Washington Post ta wallafa a watan Maris na wannan shekara, wanda ya dogara da hotunan tauraron ɗan'adam da tattaunawa da ƙwararrun makamai, ya ce a cikin makonni huɗu na farko na hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai, an lalata manyan cibiyoyi huɗu na ƙera makamai masu linzami na ballistic tare da ranana aƙalla wuraren harba makamai 29.
Rahoton ya bayyana sansanonin soji na Khojir, Parchin, Hakimiyeh da Shahroud a matsayin muhimman cibiyoyin da hare-haren suka shafa, musamman waɗanda ke da alaƙa da samar da makamai.
Haka kuma, an samu lalacewa ko toshe hanyoyin shiga wasu ramukan ƙarƙashin ƙasa da ake amfani da su wajen adana makamai masu linzami.
Sai dai ƙwararrun da The Washington Post ta tattauna da su sun jaddada cewa lalacewar waɗannan wurare ba ta nufin an rusa shirin makamai masu linzami na Iran gaba ɗaya ba.
A baya, sashen tantance labarai na BBC Verify ya yi nazarin hotunan tauraron ɗan adam da suka nuna cewa Iran na gudanar da manyan ayyukan gine-gine aƙalla a wasu manyan sansanonin makamai guda biyu da yaƙin kwanaki 40 ya shafa.
A sansanin makamai masu linzami na Kermanshah, da ke yammacin Iran kusa da iyakar Iraq, an sake gina rufin wasu gine-ginen da hare-haren suka rusa.
Haka kuma a sansanin soji na Parchin, da ke gabashin Tehran, an kwashe ɓaraguzan gine-ginen da suka lalace sakamakon hare-haren tare da sake gina wasu sassa na cibiyar.
Masana na cewa waɗannan ayyukan gyare-gyare na nuna cewa duk da irin ɓarnar da hare-haren suka haifar, Iran na ƙoƙarin farfaɗo da muhimman sassan shirinta na makamai masu linzami tare da dawo da wasu daga cikin ƙarfinta na soja.


























