Shin yawan sanya hijabi na iya janyo zubewar gashi?

d
    • Marubuci, Sajal Das Role
    • Aiko rahoto daga, BBC Bangla
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Akwai dalilai da dama da kan haddasa zubewar gashi, haka kuma ana ba da shawarwari iri-iri kan hanyoyin da za a bi domin hana matsalar ko magance ta. Sai dai ba duk shawarwarin da ake yaɗawa game da lafiyar gashi ne suke da hujjar kimiyya ba.

Shin sanya hijabi ko wani abu da ke rufe kai na tsawon lokaci na iya janyo zubewar gashi? Ko kuma shin rufe kai na tsawon lokaci na hana iska isa fatar kan mutum, har ta raunana tsirowar gashi?

Ko kuma amfani da man gashi a kullum na iya taimakawa wajen hana zubewar gashi?

Waɗannan na daga cikin batutuwan da ake yawan magana a kansu kan gashi. Amma wanne ne gaskiya, kuma waɗanne ne kawai ƙage kuma me masana ke cewa game da wannan batu?

A cewar hukumar lafiya ta Burtaniya, NHS, abu ne da aka saba gani mutum ya riƙa samun zubar gashi tsakanin 50 zuwa 100 a kowace rana. Sai dai idan mutum ya lura cewa gashinsa na zubewa fiye da yadda aka saba, ana ba shi shawarar ya garzaya wajen ƙwararren likita da wuri.

A fannin kimiyya, ana kiran yanayin da gashi ke zubewa fiye da yadda aka saba, ba tare da sabon gashi ya yi girma daidai da adadin da ya zube ba, da suna Alopecia.

Bisa ƙididdigar NHS, sama da mutum miliyan 140 ne ke fama da wannan matsala a faɗin duniya, wadda kan iya janyo zubewar wani ɓangare na gashi ko kuma duka.

Masana sun bayyana cewa zubewar gashi wani ɓangare ne na tsarin halitta na jikin mutum. Sai dai a wasu lokuta, rashin lafiya, sauyin sinadaran hormones a jiki, rashin samun isasshen abinci mai gina jiki ko damuwa na iya haddasa matsalar.

Saboda haka, yana da muhimmanci a fahimci yawan gashin da mutum kan zubar a kullum, lokacin da zubewar gashin ta zama matsala, da kuma sanin cewa wasu daga cikin batutuwan da ake yaɗawa game da gashi ba su da tushe a kimiyyance.

Me ke haddasa zubewar gashi?

d
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Akwai dalilai daban-daban da kan haddasa zubewar gashi, kuma waɗannan dalilai sun bambanta daga mutum zuwa mutum. Wasu na zubar da gashi saboda gadon halitta, wasu kuma saboda rashin kula da gashi da fatar kai yadda ya kamata, yayin da a wasu lokutan tsufa kan taka rawa.

Haka kuma, yadda gashi ke zubewa ya bambanta tsakanin maza da mata.

Na maza, nau'in sanƙo da aka fi samu shi ne wanda ake kira Androgenetic Alopecia. Wannan yanayi kan sa gashi ya fara zubewa a gaban kai, yayin da sanko kan fara bayyana a tsakiyar kai.

A wajen mata kuwa, gashi kan zama sirara a tsakiyar kai, ta yadda layin raba gashin kan iya zama mai faɗi fiye da yadda aka saba. Wannan matsala na iya faruwa sakamakon gadon halitta ko sauyin sinadaran hormones a jiki. Haka kuma, matsalar kan ƙaru yayin da mace ke ƙara shekaru.

A mata, wata cuta da ake kira Polycystic Ovary Syndrome (PCOS), wadda ke shafar ƙwayayen halittar mace, da kuma sauyin hormones a lokacin juna biyu da bayan haihuwa, na iya haddasa zubewar gashi.

Haka nan, yawan sinadaran hormones na thyroid a jiki fiye ko ƙasa da yadda ya kamata na iya taimakawa wajen haddasa matsalar.

Likitar fata kuma ƙwararriyar likitar gyaran jiki, Dakta Shaila Haq, ta ce zubewar gashi na iya faruwa sakamakon gadon halitta ko rashin daidaiton sinadaran hormones a jiki.

A hirarta da BBC, ta ce mutanen da ba sa samun isasshen abinci mai gina jiki, musamman waɗanda jikinsu ke da ƙarancin sinadaran da ke taimakawa samar da jini, sinadarin Vitamin D da Zinc, na iya fuskantar matsalar zubewar gashi.

Ta ƙara da cewa yawan damuwa da tashin hankali su ma na iya taimakawa wajen haddasa wannan matsala.

N

A cewar Dakta Haq, yadda gashi ke zubewa a wajen maza ya bambanta da yadda yake zubewa a wajen mata.

Mata da dama a Bangladesh na fama da ƙarancin jini sakamakon rashin isasshen sinadari a jikinsu, matsalar da ke cikin abubuwan da kan haddasa zubewar gashi.

Haka kuma, rage ƙiba kwatsam sakamakon bin tsarin rage nauyi, yin azumi na tsawon lokaci ko matsalar rashin cin abinci yadda ya kamata na iya haddasa zubewar gashi fiye da kima.

Wasu mutane kan fuskanci zubewar gashi kwatsam bayan watanni biyu zuwa uku da fuskantar damuwa, zazzabi mai tsanani, cututtuka kamar kyanda, taifod da Covid-19, yin tiyata ko haihuwa.

Cututtukan fata kamar Ringworm, Seborrheic Dermatitis da sauran cututtukan da ke haddasa wa na iya shafar fatar kai tare da janyo zubewar gashi fiye da kima.

Haka nan, wata cuta da ke faruwa sakamakon garkuwar jiki ta kai hari ga ƙwayoyin halittar jikinsa, wadda ake kira Alopecia Areata, na iya haddasa zubewar gashi.

Wasu magunguna ma na iya janyo zubewar gashi, ciki har da magungunan cutar daji da ake amfani da su wajen yi wa marasa lafiya tiyatar sinadarai (chemotherapy), da kuma magungunan hawan jini, damuwa da ciwon gaɓoɓi.

A cewar Dakta Haq, yawan amfani da hanyoyin gyaran gashi daban-daban, kamar amfani da sinadarai wajen gyaran gashi da kuma miƙe shi ta hanyar rebonding, na iya taimaka wa wajen haddasa wannan matsala.

Wasu jita-jita game da zubewar gashi

Akwai ra'ayoyi da dama da ba su da tushe game da abubuwan da ke haddasa zubewar gashi da kuma hanyoyin magance matsalar. Wasu mutane kan ɓata lokaci da kuɗi mai yawa wajen gwada magunguna iri-iri, maimakon neman shawarar likita.

Sauya shamfu na iya hana zubewar gashi

Mutane da dama na ganin cewa sauya shamfu na iya taimakawa wajen hana zubewar gashi. Sai dai babban aikin shamfu shi ne tsaftace gashi da fatar kai, ba wai sa gashi ya yi girma ba.

Shamfu mai kyau na iya taimaka wa wajen tsaftace fatar kai da rage zubewar gashi, amma ba zai iya magance matsalolin da ke cikin jiki ba, kamar sauyin sinadaran hormones ko rashin isasshen abinci mai gina jiki.

Rashin shafa mai a gashi kullum na haddasa zubewarsa

Man gashi na taimakawa wajen laushin gashi da rage bushewar fatar kai, amma ba ya tsiro da gashi.

A ɗaya bangaren kuma, yawan shafa mai a fatar kai na iya ƙara matsalar amosani da cututtukan da fungi ke haddasa wa ga wasu mutane.

Ruwan albasa, citta da tafarnuwa na magance sanko

Babu hujjoji a kimiyyance da ke tabbatar da cewa waɗannan abubuwa na iya magance sanko.

Sai dai a ce ma amfani da su na iya haddasa kaikayi, ƙaiƙayi ko kuma lalata wasu sinadarai a fatar kai ga wasu mutane.

A hirarta da BBC Bangla, Dakta Shaila Haq ta ce waɗannan batutuwa ba su da tushe.

Ta ba da shawarar amfani da shamfu da ba su ƙunshi sinadarai masu tsanani ba, musamman waɗanda ba su da sinadarin sulfate ko kuma aka ƙera da sinadarai masu laushi, domin kula da fatar kai. Ta kuma ba da shawarar amfani da mai domin taimaka wa wajen riƙe danshin gashi.

Baya ga haka, mutane da dama na ganin cewa zubewar gashi alama ce ta cutar daji ko wata babbar cuta. Wasu kuma na ganin cewa da zarar mutum ya yi sanko, babu yadda gashi zai sake tsirowa.

Sai dai masana sun ce a mafi yawan lokuta, abubuwan da ke haddasa zubewar gashi ba su da hatsari sosai.

Duk da haka, idan mutum ya lura cewa gashinsa ya fara zubewa kwatsam da yawa har yana zubewa dunkulalliya, ko kuma ya ga raunuka da kaikayi a fatar kansa, yana da muhimmanci ya garzaya wajen likita nan take.