Ƙungiyoyin da suka yi ƙaurin suna wajen korar kociyoyi a Ingila

Asalin hoton, Getty Images
A duniyar kwallon kafa ta zamani, sakamako ne ke tabbatar da zaman koci a aiki ko kuma korarsa. Duk da cewa wasu kungiyoyi suna bai wa masu horarwa lokaci domin gina kungiya, wasu kuwa ba sa jinkiri wajen sallamar koci da zarar sakamako ya fara tangal-tangal.
A cikin shekaru ashirin da suka gabata a Ingila, an ga wasu kungiyoyi sun zama tamkar "makabartar masu horarwa" saboda yawan sauya koci da suke yi.
Masana kwallon kafa na ganin cewa yawan korar koci ba koyaushe ne yake kawo ci gaba ba. A wasu lokuta ma, hakan na kara haddasa matsaloli saboda sabon koci kan sake gina kungiya daga tushe, lamarin da ke jawo asarar lokaci da kudi.
Ga jerin kungiyoyin da suke kan gaba a yawan sallamar kociyoyi:
Watford: Kungiyar da ta fi shahara wajen korar koci
Idan ana maganar kungiyoyin da suka fi shahara wajen sallamar masu horarwa, babu wata da ta fi Watford suna. Tun bayan dangin Pozzo da suka mallaki kungiyar a shekarar 2012, sun yi ta fama da jerin sauye-sauyen masu horarwa cikin gajeren lokaci. An ga kociyoyi suna zuwa su tafi kafin ma su kammala kakar wasa guda.
Daga Sean Dyche, Gianfranco Zola, Giuseppe Sannino, Oscar Garcia, Billy McKinlay, Slavisa Jokanovic, Quique Sanchez Flores, Walter Mazzarri, Marco Silva, Javi Gracia, Nigel Pearson, Claudio Ranieri zuwa wasu da dama, kusan babu wani koci da ya samu cikakken lokacin da yake bukata domin gina kungiyar.
A hakikanin gaskiya, Watford ta sauya sama da koci 25 daga 2012 zuwa Oktoban 2026, kuma na karshe da ta raba gari da shi a cikin watan Oktoba shi ne Alessio Dionisi wanda ya ja ragamar wasa 12.
Hakan ne ya sa ake kallonta a matsayin wadda ta fi saurin sallamar koci a Ingila.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Nottingham Forest Ta Kafa Tarihin Sauya Koci
A cikin kungiyoyin da ke buga Premier League a wannan zamani, Nottingham Forest na cikin wadanda suka fi sauya masu horarwa tun daga shekarar 2000. Rahotanni sun nuna cewa Forest ta yi sauye-sauyen masu horarwa har sau 22 daga ciki biyar suka ajiye aikin don radin kansu.
Wannan adadi ya zarce na yawancin kungiyoyin gasar, kuma ya nuna irin yadda shugabanninta suka rika neman mafita ta hanyar canza koci idan ba a samu sakamakon wasannin ba yadda ake bukata.
Leeds United Da Sunderland
Leeds United tda Sunderland duk sun sauya masu horarwa sama da 20 tun daga shekarar 2000 har da wadanda suka ajiye aikin da kansu.
Dukkan kungiyoyin biyu sun fuskanci matsalolin faduwa daga gasar Premier League da kuma kokarin komawa babban mataki, abin da ya sa shugabanninsu suka rika canza koci akai-akai.
A mafi yawan lokuta, koci na karbar aiki ne domin ceton kungiyar daga faduwa ko kuma kai ta matakin Premier League. Da zarar sakamako bai zo da sauri ba, ana yanke shawarar sauya shi.
Chelsea Da Al'adar "Rashin Hakuri"
A cikin manyan kungiyoyin Turai, babu wata da ta yi suna wajen sallamar masu horarwa fiye da Chelsea. Tun farkon shekarun 2000, kungiyar ta Landan ta yi amfani da kociyoyi da dama duk da nasarorin da wasu suka samu.
Ko da koci ya lashe kofi, hakan ba ya tabbatar masa da ci gaba da aikin. Jose Mourinho, Carlo Ancelotti, Thomas Tuchel, Maurizio Sarri da wasu fitattun masu horarwa sun taba rasa aikinsu duk da samun nasarori a wasu lokuta.
Rahotanni sun nuna cewa Chelsea ta yi akalla sauye-sauyen manyan koci fiye da 20 a zamanin Premier League, harda wadanda aka rabu ta cimma yarjejeniya, abin da ya sanya ta cikin kungiyoyin da suka fi yawan canjin jagoranci a Ingila.
Tottenham Da Matsalar Neman Kofi
Duk da kasancewarta daya daga cikin manyan kungiyoyin Ingila, Tottenham ta yi canje-canje da dama a kujerar koci. Kungiyar ta yi amfani da kociyoyi fiye da 20 a zamanin Premier League, yayin da ta yi ta kokarin kawo karshen jiran shekaru wajen lashe manyan kofuna.
Harry Redknapp, Andre Villas-Boas, Mauricio Pochettino, Jose Mourinho, Antonio Conte da wasu da dama sun jagoranci kungiyar a lokuta daban-daban.
Manchester United: Ba Ta Cikin Masu Yawan Korar Koci
Duk da cewa magoya bayan Manchester United suna yawan korafin yadda ake canza masu horarwa, alkaluma sun nuna cewa kungiyar ba ta cikin wadanda suka fi yin hakan. Tun shekarar 2000, United ta yi sauye-sauyen koci guda bakwai kawai, adadi da ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da Chelsea, Leeds, Sunderland ko Nottingham Forest.
Sai dai mafi yawan sauye-sauyen nata sun zo ne bayan ritayar Sir Alex Ferguson a 2013.
Jerin kociyoyin da Manchester United ta sallama ko ta raba gari da su bayan Ferguson
Manchester United ta tsinci kanta a wani mawuyacin hali, bayan da take ta sallamar masu horarwa, domin ganin ta koma kan ganiya tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi riatay.
David Moyes (2013-2014)
An zabo shi a matsayin magajin Ferguson amma ya kasa kai kungiyar cikin manyan guraben tebur, lamarin da ya sa aka sallame shi kafin ya kammala kakarsa ta farko.
Louis van Gaal (2014-2016)
Ya lashe FA Cup amma salon wasansa ya fuskanci suka saboda rashin jan hankali, abin da ya sa aka kawo karshen zamansa.
Jose Mourinho (2016-2018)
Ya lashe Europa League da League Cup, amma sabani tsakaninsa da shugabanni da wasu 'yan wasa ya kawo karshen aikinsa.
Ole Gunnar Solskjaer (2018-2021)
Ya kai kungiyar wasu fina-finai na gasar Turai tare da zama na biyu a Premier League, amma kasa lashe kofi da munanan sakamako suka sa aka sallame shi.
Ralf Rangnick (2021-2022)
Ya zo a matsayin mai rikon kwarya bayan korar Solskjaer.
Erik ten Hag
Ya lashe kofuna a zamansa amma rashin daidaiton sakamako da rashin ci gaban da ake fata ya janyo cece-kuce kafin karshen zamansa a kulob din.
Ruben Amorim da kuma (2024 -2026)
Darren Fletcher daga 5 Jan, 2026 zuwa 12 Jan, 2026
Michael Carrick daga 13 Jan, 2026 zuwa 12 Nov, 2026
Shin Korar Koci Ne Magani?
Tarihin kungiyoyi da dama ya nuna cewa korar koci ba koyaushe ne mafita ba. Misali, Arsenal ta ba Mikel Arteta lokaci duk da shekarun farko da ya kasa taka rawar gani, ammam daga baya kungiyar ta zama daya daga cikin masu fafatawa wajen lashe Premier League.
Haka ma Liverpool ta ba Jurgen Klopp lokaci kafin ya gina kungiyar da ta lashe Premier League da Champions League da sauran manyan kofuna.
A daya bangaren kuma, kungiyoyin da ke yawan sallamar koci sau da yawa kan kasa samun dorewar nasara, saboda sabbin tsare-tsare da sabbin 'yan wasa na ci gaba da zuwa tare da kowane sabon mai horarwa.
Watford ce ke kan gaba wajen korar koci, yayin da Chelsea, Nottingham Forest, Leeds United da Sunderland suma suka yi kaurin suna wajen sauya masu horarwa.
Duk da matsalolin Manchester United tun bayan ritayar Sir Alex Ferguson, kungiyar ba ta cikin wadanda suka fi korar koci idan aka kwatanta da wasu manyan kungiyoyin Ingila.
Abin da tarihi ya nuna shi ne cewa nasara mai dorewa ba ta dogara da korar koci kawai ba. Maimakon haka, tana bukatar tsari mai kyau, shugabanci mai dorewa, da kuma hakurin bai wa mai horarwa lokaci domin gina kungiyar da zai iya jagoranta zuwa ga daukaka.


























