'Abin da ya sa muke so majalisar Najeriya ta dakatar da hutu'

Asalin hoton, BENJAMIN KALU
Wasu gungun yanmajalisar wakilan Najeriya sun buƙaci majalisar tarayya ta dakatar da hutun da take yi domin gudanar da zaman gaggawa kan batutuwa da suka shafi ci gaban kasa.
Yanmajalisar da suka fito daga jam'iyyu daban-daban sun kafa wata kungiya da suka kira Save Democracy Group mai rajin kare dimokuradiyya.
Ƙungiyar ta bukaci shugabannin majalisun ƙasar guda biyu su kira zaman gaggawa domin tattauna batun aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 da 2025 da na 2026.
Sun ce rashin aiwatar da kasafin kudin ya kara ta'azzara matsalolin tattalin arziki da tsaro wadanda suka ce ke barazana ga ɗorewar dimokuradiyya a Najeriya.
Gungun ƴanmajalisar sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Juma'a inda suka zayyana wasu buƙatu da suka ce ya zama wajibi shugabancin majalisar ya yi la'akari da su.
Ɗaya daga cikin mamban ƙungiyar yanmajalisar, Hon Abubakar Yahaya Kusada daga jihar Katsina kuma ɗan jam'iyyar APC ya shaida wa BBC cewa suna son majalisa ta dakatar da hutun da take yi.
"Mun fahimci cewa rashin aiwatar da kasafin kuɗin ya haifar da koma-baya ga harakokin gwamnati da sha'anin tsaro da tattalin arzikin ƙasa."
Muna son majalisa ta dawo daga hutu ta kalli waɗannan abubuwa domin ba daidai ba ne a kama majalisa a rufe kuma ga matsaloli na damun ƙasa," in ji Hon Kusada.
Ya ƙara da cewa aiwatar da kasafin kuɗi zai inganta sha'anin tsaro kuma kuɗi za su yi yawo tsakanin al'umma idan an sallami yanƙwangila.
Batutuwan da ƴanmajalisar ke son a tattauna
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƴanmajalisar sun buƙaci a ba su rahoton yadda ake aiwatar da kasafin kuɗin 2024 da 2025 da 2026 da dukkanin kuɗaden da aka sakar wa hukumomi da ma'aikatun gwamnati da kuma bayani kan rashin sakin kuɗaɗen
Sun kuma buƙaci kafa kwamiti a majalisar tarayyar guda biyu domin gudanar da bincike kan rashin aiwatar da kasafin kuɗin ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Baya ga batun kasafin kuɗi, ƙungiyar ƴanmajalisar ta SDG na son a tattauna batun taɓarɓarewar tsaro musamman a arewacin Najeriya.
Batun kuɗirin samar da ƴansandan jihohi na daga cikin buƙatun ƴanmajalisar wanda ke ci gaba da haifar cecekuce.
Suna kuma son majalisar ta gaggauta dawo wa daga hutu diba damuwar da wasunsu suka nuna na rashin sakin kuɗi ga hukumomin tsaro na ƙasar.
Suna kuma son a tattauna zargin da suke yi na abin da suka kira gurguncewar dimokuradiyya da tafiyar da lamurran gwamnati.
Yanmajalisar sun jaddada cewa yunkurinsu ba na ƙawancen adawa ba ne ko kuma wani mataki na matsin lamba ta siyasa.
Sun ce su ƴanmajalisa ne da ke nuna damuwa da abin da suka kira rushewar cibiyoyin dimokuradiyya a Najeriya
Sai dai ana tunanin ƴanmajalisar sun nace ne kan batun aiwatar da kasafin kuɗi saboda ya shafe su wurin rashin samun kuɗaɗen aiwatar da ayyukan su na mazaɓu.











