Buƙatu 7 da Najeriya ta miƙa a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

..
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Alhamis ne Najeriya ta yi jawabi ga wakilan ƙasashe a yayin zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) da aka gudanar a birnin New York na ƙasar Amurka.

Shugaba Bola Tinubu, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilta, ya bayyana wasu buƙatu guda 7 da Najeriya ta nema a zauren majalisar.

Buƙatun da Kashim Shettima ya gabatar

  • Kujerun dindindin a majalisar tsaro: Najeriya na neman a bai wa Afirka kujeru biyu na dindindin a kwamitin tsaro na majalisar, tare da dukkan hakkokin da sauran mambobin dindindin ke da su, da kuma kujeru biyar wadanda ba na dindindin ba.
  • Mutunta dokokin ƙasa da ƙasa: Najeriya ta yi kira da a koma ga manufofin da aka kafa Majalisar Dinkin Duniya a kansu, wato tattaunawar diflomasiyya da mutunta juna, maimakon amfani da karfi ko danniya, da kuma mutunta dokokin kasa da kasa.
  • Amfani da diflomasiyya don warware rikici: Game da rikice-rikicen da ke faruwa a sassan duniya, Najeriya ta bukaci a kara amfani da diflomasiyya wajen samar da mafita, musamman a Sudan da sauran kasashen da yaki ya daidaita, da kuma kiran dukkan bangarorin da ke rikici su kare fararen hula, su mutunta dokokin jin kai na duniya, tare da bai wa masu aikin agaji damar kai dauki ga wadanda ke cikin bukata.
  • Ƙirƙirarriyar basira: Najeriya ta bukaci a yi amfani da fasahar kirkirarriyar basira, wato AI, wajen bunkasa harkokin lafiya, noma, ilimi da tattalin arziki, maimakon amfani da ita wajen yaki da tada rikici.
  • Hada-hadar kuɗi: A bangaren tattalin arziki, Najeriya ta nemi a sake fasalin tsarin hada-hadar kudi na duniya, domin bai wa kasashe masu tasowa damar samun rance cikin sauki, da kuma tsarin biyan basussuka da zai ba su damar ci gaba, wanda ya yi dai dai da bukatunsu.
  • Ayyukan tabbatar da zaman lafiya: Najeriya ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta kara karfafa ayyukan tabbatar da zaman lafiya, da shiga tsakani, da dakile barkewar rikice rikice, da kuma hadin gwiwar kasashe wajen yaki da ta'addanci da sauran manyan laifuka.
  • Sauyin yanayi: Najeriya ta nemi a yi adalci a batun sauyin yanayi, inda ta yi kiran a samar da fasahohi da ilimi da kuma kudade wajen taimakawa kasashe masu tasowa cimma bukatar rage samar da abubuwan da ke gurbata muhalli, domin su samu damar tinkarar matsalar ba tare da hana ci gaban tattalin arzikinsu ba.

Me ya hana Tinubu zuwa taron?

Fadar shugaban ƙasa ta ce Shugaba Bola Tinubu ba zai halarci taron UNGA karo na 81 da kansa ba ne saboda yana hutunsa na shekara a ƙasar Faransa.

Jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce rashin halartar shugaban ba yana nufin Najeriya ba ta da wakilci a taron ba, domin tawagar ƙasar za ta ci gaba da shiga dukkan zaman da za a gudanar.

Shi ma babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin ƙasashen waje, Ademola Osodi, ya ce rashin zuwan Tinubu taron ba zai rage tasirin Najeriya a harkokin diflomasiyya ko shugabancinta a nahiyar Afirka ba.

Da yake magana a shirin Sunday Politics na tashar Channels TV, Osodi ya ce shugaban na mayar da hankali kan muhimman batutuwan cikin gida ne, musamman tattalin arziki da tsaro.

Ya ƙara da cewa Najeriya na ci gaba da hulɗa da ƙasashen duniya ta wasu hanyoyin, ba sai ta Majalisar Ɗinkin Duniya kaɗai ba.

"Akwai muhimman batutuwan da suka shafi tattalin arziki da tsaro da shugaban ke mayar da hankali a kansu a gida," in ji Osodi.

Ya kuma ce kasancewar Tinubu ko rashinsa a taron ba zai sauya matsayin Najeriya a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasashen Afirka ba.

Me rashin halartar Tinubu ke nufi ga Najeriya?

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masana harkokin Diplomasiyya a Najeriya sun fara tsokaci kan damarmakin da ƙasar ke rasawa saboda rashin zuwan shugaba Bola Tinubu babban taron majalisar Dinkin Duniya karo na uku a jere.

Masana na ganin hakan zai iya hana Najeriya wasu damarmaki musamman wajen ganawa da shugabannin ƙasashe domin inganta alaƙa.

Ambasada Aminu Iyawa, tsohon jakadan Najeriya ne a ƙasar Mexico, ya ce duk shugaban da ya san mahimmancin halartar wannan taron ba zai ƙi zuwa da kansa ba sai idan akwai ƙwaƙƙwaran dalili.

"Yawancin mutane sun ɗauka cewa waɗannan jawaban da shugabannin ƙasa ke yi a wajen taron shi ne mafi muhimmanci, a'a ba haka ne ba,".

Ya ce akwai ganawar da shugabannin ke yi a gefen taron, wanda shi ne ya fi amfani ga duk wata ƙasa da ke da wata buƙata musamman ma ƙasashe masu tasowa irin Najeriya.

Masanin ya ce "Najeriya ta yi asara sosai" saboda rashin halartar Shugaba Tinubu a taruka uku da suka gabata. A cewarsa shugabanni sun fi son ganawa da takwarorinsu domin yanke hukunci da ɗaukar mataki nan take wanda wakilci ba zai iya yi ba.

'Damarmakin da Najeriya ke rasawa'

Ambasada Iyawa ya ce Najeriya za ta iya amfani da wannan damar wajen neman sassaucin basussukan da ake bin ta daga Bankin Duniya da IMF, wanda shugabannin da suka ci gaba irin su Amurka, India, Faransa da China ke da ruwa da tsaki.

Ya ce ba lallai a kalli buƙatun da mataimakin shugaban zai gabatar ba, amma in da Tinubu ya je zai iya neman a yafe wasu basukan ko a rage su.

"Ai duk wani shugaba da yake son ƙasarsa ta ci gaba, zai je,... wataƙila shi shugaba Tinubu bai ɗauki wannan taro da muhimmanci ba," in ji shi.

Baya ga batun yafe basussuka da Najeriya za ta iya neman sassauci a kai, akwai batun da Ambasada Iyawa ya ce babbar dama ce ga Najeriya.

Ya ce sakamakon yadda ƙasar kullum take neman masu zuba jari su shiga ƙasar a fannonin harkar mai, zinare da wasu ma'adanan ƙasa, ba lallai ta iya jan hankalin duniya ba idan shugabanta ba ya irin wannan waje da kansa.

"Idan ba shi ya yi magana da su ba, babu wani tasiri da abin zai yi... Idan kana so ƙasar ka ta ci gaba, ta samu daraja, ka yi magana a ji, sai in ga ka ga su," in ji Ambasada Iyawa.