Su wane ne za su jagoranci yaƙin zaɓen Atiku Abubakar?

Atiku Abubakar
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Jam'iyyar ADC ta bayyana waɗanda za su jagoranci yaƙin zaɓen tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar a fafutikar da take yi ta samun galaba a kan APC ta Bola Tinubu.

Daga cikin waɗanda suka fi jan hankali a jerin sunayen akwai tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai wanda yake tsare yana fuskantar shari'o'i daban-daban daga wajen hukumomin Najeriya.

A cikin sanarwar, wadda Phrank Shaibu, mai magana da yawun Atiku, wanda kuma aka naɗa a matsayin daraktan ɓangaren sadarwa na yaƙin zaɓen, ya ce Atiku ya amince da kafa kwamitin yaƙin neman zaɓe.

Ya ce: "Atiku Abubakar ya amince da kwamitin yaƙin zaɓe na ƙasa na neman zaɓen shugaban ƙasa," in ji shi.

INEC ta sanya ranar 20 ga Fabrairun 2027 domin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisun tarayya, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi kuma za su gudana ne a 6 ga Maris 2027.

Muhimman waɗanda suke ciki

Sanarwar ta ce Kashim Ibrahim-Imam ne zai jagoranci kwamitin yaƙin neman zaɓen na ƙasa a matsayin shugaba.

Wanda zai masa mataimaki shi ne Nasir El-Rufai, tsohon ministan Abuja kuma tsohon gwamnan Kaduna.

Sanarwar ta bayyana cewa El-Rufai na da gogewa sosai a fannin gudanar da gwamnati, tsara harkokin siyasa da shugabanci, kuma zai riƙa kula da haɗin gwiwar siyasa da muhimman masu ruwa da tsaki a faɗin ƙasar nan.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Darakta-Janar na yaƙin zaɓen shi ne Sanata Austin Akobundu, wanda sanata ne mai wakiltar Abia ta tsakiya a majalisar dattawa, wanda kuma kanal ɗin sojin Najeriya ne mai ritaya kuma tsohon ƙaramin ministan tsaro.

Sanarwar ta ƙara da cewa domin samun ingantacciyar gudanarwa, an raba yaƙin neman zaɓen zuwa manyan ɓangarori shida, kowanne ƙarƙashin jagorancin mataimakin darakta-janar.

A cikin waɗannan ɓangarorin akwai daraktoci 30, waɗanda aka sanya musu takamaiman ayyuka.

Fitaccen ɗan jarida Dele Momodu ne zai jagoranci ɓangaren watsa labarai a matsayin mataimakin darakta-janar.

Zai jagoranci harkokin yaɗa labarai da sadarwa ta hanyar jaridu, gidajen rediyo da talabijin, da kuma kafafen sada zumunta na zamani.

Ɓangaren tsara manufofi zai kasance a ƙarƙashin jagorancin Mohammed Hayatudeen, wanda tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma masanin tattalin arziki.

Zai yi aiki tare da Farfesa Mohammed Sagagi a matsayin mataimakin shugaba da Aare Aremijoye a matsayin sakatare.

Masu ba kwamitin yaƙin zaɓen za su kasance a ƙarƙashin jagorancin John Oyegun da tsohon gwamnan Jihar Edo kuma shugaban farko na jam'iyyar APC.

Tsohon Sanata Ben Obi da Lawal Batagarawa za su kasance mataimakan shugabanni, yayin da Eyitayo Jegede (SAN) zai zama sakatare.

Ba a tuntuɓe ni ba - Moghalu

Wani abu da ya ja hankali shi ne daga cikin ƴan kwamitin yaƙin zaɓen, akwai Kingsley Moghalu, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), wanda ya fito yi watsi da sanya sunansa cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma'a, masanin tattalin arzikin ya bayyana cewa ba a tuntuɓe shi ba kuma bai ba da amincewarsa ba kafin a saka sunansa cikin kwamitin.

Tunda farko, Atiku ya sanya Moghalu a kwamitin tsara manufofin yaƙin neman zaɓen, wadda Mohammed Hayatu-Deen ke jagoranta.

Sai dai Moghalu ya ce jam'iyyar ADC ba ta nemi izininsa ba kafin sanya sunansa a cikin jerin sunayen.

Ya ce: "Na yi mamakin ganin wata sanarwa daga kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku da ADC wadda ta haɗa sunana a matsayin mamba a kwamitin tsara manufofin Atiku Abubakar, domin zaɓen shugaban ƙasa na 2027."

Moghalu ya ƙara da cewa ya daina harkokin siyasa na jam'iyya a Najeriya tun shekarar 2022, kuma tun daga lokacin yake ci gaba da kasancewa ba tare da nuna goyon baya ga wata jam'iyya ba a harkokin ƙasar.

Takarar Atiku ta bakwai

Atiku Abubakar

A tsawon shekara sama da 30 da suka gabata, tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya kasance dumu-dumu cikin harkokin siyasar ƙasar ko dai a matsayin ɗan takara, ko a shugabanci.

Ya dade yana fafutikar siyasar tare da yunƙurin neman shugabancin ƙasar mai ɗimbin al'umma da tarin arziki.

A wannan karon, Atiku Abubakar ya samu jimillar ƙuri'a 1,846,370, inda ya kayar da sauran ƴan takara biyu Rotimi Amaechi, wanda yake mara masa baya da kuma Muhammed Hayatu-Deen wanda yanzu yake jagorantar kwamitin tsara manufofin ɗan takarar.

Atiku Abubakar ya fara takara ne tun a shekarar 1993, inda ya shiga zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar SDP, amma ya yi rashin nasara, inda Abiola ya doke shi da sauran ƴan takarar domin samun tikiti.

Daga lokacin zuwa yanzu, ya yi yunƙurin zama shugaban ƙasar sau shida ke nan jimilla, sannan yanzu yake sake yunƙuri na bakwai.