Abubuwa biyar da mata ba sa so

Wata mata kwance da wani namiji a gefen ta yana latsa waya
    • Marubuci, Rabiatu Kabir Runka
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wani lokaci sai ka ga kamar matarka na fushi ko ta canza halinta, amma ba ka fahimci abin da ya faru ba.

Wataƙila ka tambaye ta abin da ke damunta, ta ce babu komai, alhali a zuciyarta akwai abin da ya ɓata mata rai.

A wasu lokuta kuma, namiji kan yi wani abu da yake ganin ba shi da wani muhimmanci, amma mace ta ɗauke shi da muhimmanci sosai.

Hakan na iya faruwa ne saboda yadda maza da mata ke kallon wasu abubuwa a zamantakewa ya bambanta. Abin da namiji zai iya ɗauka a matsayin wasa, ƙaramar magana ko al'amari da bai kamata a damu da shi ba, mace na iya ganin sa a matsayin rashin kulawa, rashin girmamawa ko kuma rashin nuna mata ƙauna.

Amma shin maza suna sanin waɗannan abubuwan da mata ba sa so?

Ka taɓa tsayawa ka yi tunanin halayen da matarka ko abokiyar zamanka ba ta so, waɗanda ƙila ba lallai ne ta faɗa maka kai tsaye ba?

A zamantakewa, ba wai manyan matsaloli ne kaɗai ke iya kawo sabani tsakanin mace da namiji ba.

Wasu ƙananan abubuwa da ake maimaitawa a kullum su ne kan taru su haifar da rashin fahimta ko kuma su sa ɗaya daga cikin ɓangarorin ya ji cewa ba a daraja shi.

Maryam Hassan Baba ƙwararriyar mai bada shawarwari kan aure da zamantakewar iyali, kuma wadda ta kafa ƙungiyar masu bada shawara ta Northen Therapist ta shaidawa BBC cewa duka mata ba su taru sun zama ɗaya ba kuma kowace na bayyana abubuwan da ba ta so ne bisa laʼakari da abin da ya same ta ko ta ci karo da shi.

Wata mace ta juya wa wani namiji dake kusa da ita baya

Abubuwan da ya kamata a kiyaye

Maryam Hassan Baba ta ce kowace akwai abubuwan da ke sosa mata rai, sai dai yawanci mata sun yi tarayya ga wasu abubuwan da suka haɗa da :

Maƙo ko Rowa

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Idan ka san cewa hannun jariri gare ka, wato kana da halin yin abu ko taimakawa amma kana ƙin yi, akwai yiwuwar matarka ko abokiyar zamanka ta daɗe tana haƙuri da kai fiye da yadda kake zato.

Wasu maza kan ɗauka cewa mace tana son kuɗi ne kawai idan tana buƙatar a saya mata wani abu ko kuma tana son namiji ya taimaka mata da wasu buƙatu.

Amma ba koyaushe haka lamarin yake ba.

Ga wasu mata, abin da ya fi muhimmanci shi ne su ga cewa namijin da suke tare da shi yana kula da bukatunsu kuma yana shirye ya yi abin da zai iya idan yana da hali.

Rashin kyautawa ko rashin damuwa da buƙatun mace na iya sa ta ji cewa ba a daraja ta ko kuma ba a damu da jin daɗinta ba.

Maryam Hassan Baba ta ce ba rashin kashe ma mata kuɗi ne matsala ba, ʼMatsalar ita ce sai su yi tunanin mutumin da ba ya sakin hannu baya laʼakari ne da halin da suke ciki kuma ba ya so ya sauƙaƙa masu su samu sauƙi.ʼ

"Saboda duk wanda baya baka gani kake kamar yana son sanya ka cikin ƙunci a rayuwarka musamman wanda yake son ka,"cewar Maryam.

Wata mata rike da kudi

Rashin yabo

Duk nauyin bakinka, mace ba ta son ta yi girki, ta yi kwalliya ko ta yi wani abu na musamman, amma namijin da take tare da shi ya kasa cewa komai.

Maryam Baba ta ce mata na ɓata lokaci wajen yin wani abu ne domin su nuna suna son waɗanda suke tare da su, saboda haka idan ba a yaba masu ba suna jin kamar ʼan raina ƙoƙarinsuʼ.

Yabo ba sai ya kasance mai tsawo ba, wani lokaci kalma guda kamar "Kin yi kyau yau,ko na ji daɗin abincin nan, na iya isar da saƙo mai girma."

Kuma idan ka yaba mata, ba ita kaɗai za ta amfana ba. Yabo na iya ƙara mata ƙwarin gwiwa da azama, ta kuma ji cewa ƙoƙarinta yana da amfani.

Wata mata ta sha kwalliya

Rashin sauraron ta

Idan mace tana son ta faɗa maka abin da ke damunta, kada ka yi saurin ce mata ta cika ƙorafi ko ta cika raki.

Maryam ta ce wani lokaci ba tana neman mafita ba ne, abin da take so shi ne ka ba ta lokaci, ka saurare ta kuma ka fahimci abin da take ji.

Idan ba ka saurare ta ba, wa kake so ta je ta yi wa ƙorafin?

Mace da ta saba ƙoƙarin bayyana abin da ke damunta amma kullum ana katse ta ko kuma a raina abin da take ji na iya fara rufe bakinta.

"Hakan na iya sa ta ji cewa ba ta da mahimmanci ko kuma ba a daraja ra'ayinta, ko kuma ba ta da wanda za ta iya dogara da shi idan tana cikin damuwa."

Mace da namiji zaune suna dariya

Tsananin kishi

Kishi na iya kasancewa wani ɓangare na soyayya, amma idan ya wuce gona da iri, zai iya zama abin da mace ba ta jin daɗinsa.

Idan namiji yana yawan zargi, tambayar duk inda mace ta je, wanda ta yi magana da shi ko kuma dalilin da ya sa ta yi magana da wani mutum, hakan na iya jefa ta cikin fargaba.

Wasu mata kan fara ɓoye wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu, ba wai saboda suna yin wani abu ba, sai don gudun zargi, mita ko rigima.

A irin wannan yanayi, kishi wanda ya kamata ya kasance alamar kulawa na iya koma wa abin da ke kawo rashin kwanciyar hankali a zamantakewa.

Wata mata tana duba wayar ta mijinta na mata leke

Yaudara

Mace ba ta son namijin da yake faɗin abin da ba haka yake a zuciyarsa ba.

Misali, namiji na iya cewa mace ita kaɗai ce yake so, alhali kuma akwai wasu mata da dama da yake faɗa musu irin wannan magana.

Maryam Hassan Baba ta ce irin wannan ɗabiʼa kan sanya mace ta ji namiji ya fice ma ta daga rai.

"Yaudara ba ta tsaya kan batun soyayya da wata mace kawai ba. Tana iya kasancewa ta hanyar yin ƙarya, ɓoye gaskiya ko kuma faɗin abin da mutum ya san ba haka yake ba domin ya samu abin da yake so."

Idan mace ta gano cewa ana yaudararta akai-akai, zai iya yi mata wahala ta sake yarda da abin da namijin yake gaya mata.