Ana zarfin kwalera ta yi ajalin aƙalla fursunoni shida a gidan yari a Najeriya
Aƙalla fursunoni shida ne suka mutu cikin mako guda bayan da ake zargin an samu ɓarkewar cutar kwalera a wani gidan yari mai tsananin tsaro da ke jihar Kano, a arewacin Najeriya, kamar yadda jaridar Daily Post ta yanar gizo ta ruwaito a ranar 26 ga Satumba.
Ƙungiyar Amnesty International reshen Najeriya ta yi kira ga hukumomi da su ayyana dokar ta-ɓaci ta lafiyar jama'a a gidan yarin Kurmawa mai tsawon shekara 115, bayan mutuwar fursunonin.
Ƙungiyar ta ce a ranar 25 ga Satumba cewa adadin waɗanda suka mutu na iya zama sama da haka, yayin da ake zargin cutar na ci gaba da yaɗuwa tsakanin fursunonin.
Amnesty ta ce: "Gaskiyar magana ita ce, a Najeriya waɗanda ke gidan yari ba sa samun cikakkiyar kariyar haƙƙoƙinsu," kamr yadda sanarwar ta nuna.
An samu rahoton sabbin mutuwar ne bayan Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Najeriya ta ce ta shawo kan ɓarkewar cutar kwalara a gidan gyaran hali na Kurmawa mai matsakaicin tsaro da ke Kano, inda ta ce mutum biyu ne suka mutu sakamakon cutar.




















