Wane zaɓi ya rage wa Pantami bayan kotu ta soke takararsa?

Pantami
    • Marubuci, Bashir Zubairu Ahmad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 2

Har yanzu jama'a na ci gaba da muhawara kan makomar takarar gwamnan jihar Gombe da Farfesa Ali Isa Pantami ke yi a zaɓen da ke tafe.

A ranar Alhamis ne babbar kotun tarayya da ke Gombe ta soke tikitin fitaccen malamin Addinin Musuluncin, wanda ke yi wa jam'iyyar adawa ta PDP takara a zaɓen 2027.

Usman Aliyu Garry ne ya shigar da ƙarar Pantami a gaban kotun yana ƙalubalantar halascin hanyar da ya bi wajen samun takarar.

A watan Yunin 2027 ne jam'iyyar PDP ta tsayar da tsohon ministan sadarwar Najeriyar takarar gwamnan jihar, kwanaki kaɗan bayan komawarsa jam'iyyar daga APC.

Tun da farko Pantami ya tsaya takarar gwamnan ne a jam'iyyar APC, amma da bai yi nasara ba ya fice daga cikinta.

Me hukuncin kotun ya ƙunsa?

A hukuncin da ta yanke babbar kotun tarayyar ta buƙaci jam'iyyar PDP ta sake zaɓen fitar da gwanin gwamnan jihar.

Mai shari'a Amina Mohammed ta ce tsarin da PDP ta bi wajen bai wa Pantami takara ya saba wa ƙa'idojin jam'iyyar da kuma dokokin zaɓe da suka dace ba.

A cewar kotun hakan ya haifar da cire wasu masu neman takarar da aka tantance kuma aka amince su shiga zaɓen fidda gwani.

Kotun ta kuma buƙaci PDP ta sake gudanar da sabon zaɓen fidda gwani, bisa ƙa'idojin jam'iyyar da kuma tanade-tanaden dokokin zaɓe da suka dace.

Me ɓangarorin biyu ke cewa?

Bayan zartas da hukuncin wanda ya shigar da ƙarar Usman Aliyu Garry, ya shaida wa BBC cewa, mataki ne da ya yi musu daidai.

A cewar sa, "mun kai wannan ƙarar yau kusan wata biyu kenan kuma mun samu nasara cewa zaben da aka yi ba sahihi ba ne, sannan kuma shi Farfesa Isa Ali Pantami takarar da ya samu ya same ta ne ta bayan gida kamar yadda muka sha faɗa," in ji shi.

Ya kuma ƙara da cewa tun da farko akwai matakai da suka haɗa da yin zaɓen share fage ko dai ta ƴar tinƙe ko maslaha domin a bar wa ɗan takara guda, amma a cewarsa ba a yi ko da ɗaya ba.

''Hakan ne ma ya sa muka lura babu wani adalci na amincewa da tikitin Pantami'', in ji shi.

BBC ta tuntuɓi ɓangaren Pantami, amma makusantansa sun shaida mana cewa lauyoyinsu na nazarin hukuncin domin ɗaukar mataki na gaba.

Wane zaɓi ya rage wa Pantami?

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

BBC ta tuntuɓi Barista Sanusi Musa SAN, wani babban lauya, masanin harkokin shari'a a ƙasar, wanda kuma ya ce wannan hukuncin mai baki biyu ne.

Kwararren lauyan ya ce Pantami na da zabi biyu, ko dai ya amince da hukunci a je a sake zaben fitar da gwani, ko kuma ya daukaka kara kan hukuncin.

''Saboda akwai shari'u da suka wuce a baya da har Kotun Kolin, wadda ta ce zancen a je a sake zaɓen fitar da gwanin bai taso ba tunda ita jam'iyya ta karya doka ba ta da ɗan takara kenan'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa an taɓa samun haka a shari'ar jihar Zamfara da na da majalisar jiha na ƙaramar hukumar Kura da Garun Malam a jihar Kano a shari'ar da aka ba suna ''Ƙarfi da APC''.

A cewar Barista Sanusi a yanzu Farfesa Isa Ali Pantami na da dama ta biyu ta ɗaukaka ƙara kuma kotun gaba na iya ba shi nasara saboda jam'iyya ce ta amince da takararsa.

"Ko kuma idan su biyun idan sun amince da hukuncin kotun, to suna iya amincewa da gudanar da zaɓen fitar da gwani nan gaba", in ji Barista Sunusi Musa.