Oshoala: Ƴar Najeriya Musulma da ta fi samun nasara a ƙwallon mata a Afirka

Asisat
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Lokacin da Asisat Oshoala take yarinya a Ikorodu a jihar Legas, ƙwallo ba ta kasance abin da iyayenta suke ganin zai zama hanyar samun abin sakawa a bakin salati ga ƴarsu ba.

Amma duk da haka ta dage lallai tana son taka leda domin tsanain sha'awar harkar da take yi.

Yanzu abin da ya fara a matsayin wasa da yara maza a tituna, ya zama sana'a da ta kai ta zuwa wasu daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon mata a duniya.

An haifa Asisat Lamina Oshoala OON a ranar 9 ga Oktoban 1994 a garin Ikorodu da ke jihar Legas a kudu masso yammacin Najeriya, kuma yanzu hka tana taka leda ne a matsayin ƴar wasan gaba a ƙungiyar Al-Hilal ta mata ta ƙasar Saudiyya, da kuma tawagar ƙasar Najeriya ta mata.

Ana ɗaukar ta a matsayin ɗaya daga cikin zaratan ƴan wasan ƙwallon mata na zamaninta, kuma tana cikin ƴan wasan ƙwallon mata na Afirka da suka fi shahara a tarihi.

Yadda ta fara ƙwallo

Asisat

A wata tattauna da mahaifinta ya yi da BBC , Alhaji Oshoala ya ce da farko ba su ga hanya mai ɓillewa ba a ƙwallon ƙafa ga mace, wanda hakan ya sa suka so Asisat ta mayar da hankali kan karatu.

Ita ma ta tabbatar a hirar cewa iyayenta ba su so ta buga ƙwallo da farko, har ta kai ga ta komawa bugawa a ɓoye. Ta ce a wasu lokuta idan ta fita buga ƙwallo sai ta gudu zuwa gidan kakarta domin gudun hukunci.

Asisat ta ce a lokacin tana ƙoƙarin haɗa karatu da ƙwallo, amma burinta shi ne ta kai matakin ƙwararru.

A wata hira da Sky Sports a 2025, ta bayyana yadda ta fara da buga ƙwallo da yara maza a titi har wata rana ta gano cewa akwai ƙungiyar ƙwallon mata da ke atisaye kusa da inda take wasa, lamarin da ya buɗe mata ƙofar zama abin da ta zama a yanzu.

Daga baya ta shiga ƙungiyar FC Robo tana shekara 15, kafin ta koma Rivers Angels. A shekarar 2014 ne duniya ta fara ganin irin baiwar da take da ita.

A gasar kocin duniya ta mata ƴan ƙasa da shekara 20 wato FIFA U-20 Women's World Cup da aka gudanar a Canada, ta ci ƙwalloe bakwai, inda ta lashe Golden Boot a matsayin wadda ta fi cin ƙwallaye da kuma Golden Ball a matsayin gwarzuwa ƴar wasa.

A wannan shekarar kuma ta taka rawar gani a gasar cin kofin Afirka ta mata. Ta ci ƙwallao huɗu a gasar, ta taimaka wa Najeriya ta doke Kamaru 2-0 a wasan ƙarshe, sannan aka ba ta kyautar gwarzuwar ƴar wasa na gasar.

Daga Najeriya zuwa Turai

Asisat
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan nasarorin da ta samu a Najeriya, tafiyarta ta kai ta Ingila inda ta buga wa Liverpool, sannan ta koma Arsenal.

A shekarar 2016, ta taimaka wa Arsenal lashe FA Women's Cup. Daga nan ta koma China, inda ta lashe gasar China Women's Super League a 2017 kuma ta zama wada ta fi cin ƙwallaye a gasar da ƙwallo 12.

A shekarar 2019 ne ta koma Barcelona, inda ta fara wani sabon babi a rayuwarta. A Champions League na shekarar, ta zama ƴar Afirka ta farko da ta ci ƙwallo a wasan ƙarshe na gasar, lokacin da Barcelona ta sha kashi a hannun Lyon.

Shekara biyu bayan haka, ta ƙara kafa wani tarihi, inda a shekarar 2021, Oshoala ta zama ƴar Afirka ta farko da ta lashe gasar UEFA Women's Champions League, bayan Barcelona ta doke Chelsea 4-0 a wasan ƙarshe.

A Barcelona ta lashe kofuna masu yawa. Bayan shekar shida a ƙungiyar Barcelona ta ta lashe kofuna 14 tare da ƙungiyar: La Liga 5 a 2019–20, 2020–21, 2021–22, 2022–23 da 2023–24 da UEFA Women's Champions League biyu a 2020–21 da 2022–23 da Supercopa de España Femenina a 2019–20 da 2021–22 a 2022–23 da 2023–24 sai kuma Copa de la Reina da 2019–20 da 2020–21 da 2021–22.

Gwarzuwar ƙwallon Afirka shida

Asisat

Amma babban abin da ya sa sunan Oshoala ya zama na musamman a tarihin ƙwallon mata na Afirka shi ne yawan kyaututtukan da ta samu.

Ta lashe kyautar gwarzuwar ƙwallon Afirka wato CAF African Women's Player of the Year sau shida a 2014, 2016, 2017, 2019, 2022 da 2023.

Wannan shi ne tarihin da babu wata ƴar wasa ko ɗan wasa da ya kai. A 2023, ta lashe kyautar karo na shida, inda ta ƙara zarce tsohuwar ƴar wasan Najeriya Perpetua Nkwocha mai guda huɗu.

A shekarar da ta lashe kyautar karo na shida, Oshoala ta kuma taimaka wa Barcelona lashe Champions League, yayin da ta zama wada ta fi zura ƙwallaye ta ƙungiyar da ƙwallo 27 a dukkan gasa.

A Najeriya kuwa ta lashe gasar cin kofin Afirka ta mata wato Women's Africa Cup of Nations sau biyar: 2014, 2016, 2018 da 2024, sannan ta ta ci ƙwallo a gasar Kofin Duniya guda uku daban-daban

Ƴar Najeriya Musulma

Asisat

Bayan nasarorin da ta samu a filin wasa, wani muhimmin ɓangare na rayuwar Oshoala shi ne addininta.

A wata hira da shafin FC Barcelona, Oshoala ta bayyana kanta a matsayin Musulma, wadda ta taso a gida da aka kwatanta addinin Musulunci.

A hirar, ta bayyana cewa tana yin sallah kuma tana azumin Ramadan, duk da irin yanayin rayuwarta a matsayin ƙwararriyar ƴarwasa.

Ta kuma bayyana cewa ba koyaushe take iya rufe kanta ko sanya hijabi ba, amma tana yin hakan a wasu lokuta ko lokacin da take gida.

A wata hira da shafin FIFA, ta bayyana yadda ƙwallo ta sauya rayuwarta da yadda take ganin kanta a matsayin abin koyi ga ƴan mata. Ta ce addininta, iyalinta da inda ta fito suna daga cikin abubuwan da suka sa take ganin kanta a matsayin "alama ta cikar buri" ga ƴan mata da dama.

Nasara da taimako

Asisat

Abin da ya fi jan hankali shi ne yadda Oshoala ta yi amfani da labarinta wajen taimaka wa sauran ƴan mata.

Ta kafa Asisat Oshoala Academy domin ba ƴan mata damar shiga ƙwallo tare da ci gaba da karatunsu.

A hirarta da Sky Sports, ta bayyana cewa tana tabbatar da ƴan matan da ke makarantar suna ci gaba da karatu, domin ba ta son a fahimci cewa dole mace ta bar karatu idan tana son yin wasanni.

A cewar Asisat, abin da take son koyar da ƴan matan shi ne cewa za su iya yin karatu da ƙwallo a lokaci guda.

Daga yarinyar da iyayenta ba sa son ta buga ƙwallo, zuwa ƴar wasa da ta fi lashe kyautar kambun gwarzuwar ƙwallon ƙafa a Afirka da lahe kofuna da dama, labarin Asisat ya zama abin kwatance a harkar ƙwallon ƙafa.