Mece ce kujerar dindindin a MDD da Najeriya ke yawan nema a taron UNGA?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A lokuta da dama ƙasashen Afirka, ciki har da Najeriya na yawan maimaita buƙatar samun kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a duk lokacin da suka halarci babban taron MDD da aka fi sani da UNGA.

A jawabin da ya gabatar a zauren taron, Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya sake jaddada buƙatar bai wa Afirka damar samun kujerar.

Batun ya kasance ɗaya daga cikin buƙatun da Najeriya ta jima tana kira a duk lokacin taron na UNGA.

Shettima ya kafa hujjar Najeriya ta na neman kujerar da irin rawan da take takawa a ayyukan wanzar da zaman lafiya na duniya daban-daban.

Dangane da Afirka kuwa mataimakin shugaban na Najeriya ya kafa hujja da ƙaruwar yawan al'umma da kuma tasirin da nahiyar ke da shi.

Sai dai duk da yawan maganganun da ake yi kan batun, mutane da dama na tambayar mene ne ainihin kujerar dindindin a Kwamitin Sulhu? Kuma me ya sa Najeriya da sauran ƙasashen Afirka ke ganin samun irin wannan kujera na da matuƙar muhimmanci a gare su?

Mene ne kwamitin tsaro na MDD

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya shi ne ƙololuwar majalisar yanke hukunci kan manyan ƙudurorin duniya.

Farfesa Tukur Abdulƙadir, ƙwararren masanin diplomasiyyar ƙasashe kuma malami a jami'ar Kaduna ya ce kwamitin tsaro ne dama ta ƙarshe wajen tabbatar da kowane irin ƙuduri a duniya.

Wata ƙwarya-ƙwaryar majalisa ce mai mambobi biyar masu kujerar ƙarfin faɗa a ji a duniya, masu ƙarfi a lokacin da aka kafa majalisar Duniya bayan Yaƙin Duniya na biyu.

Ƙasashe biyar masu kujerar dindindin a kwamitin sun haɗa da:

  • Amurka
  • Birtaniya
  • Faransa
  • Rasha
  • China

Baya ga ƙasashen biyar akwai wasu mambobi masu kujerar wucin gaɗi a majalisar, da ake sauyawa bayan shekaru.

''Idan duka ƙasashen duniya suka amince da ƙudiri a matakin duniya, amma aka samu ɗaya daga cikin ƙasashe masu kujerar dindindin ta ƙi amincewa da shi, to shikenan ya rushe'', in ji shi.

Me ya sa ƙasashen Afirka ke son kujerar dindindin?

Ƙasashen Afirka sun jima suna kiraye-kirayen samun kujerar dindindin a majalsiar Dinkin Duniya.

Farfesa Tukur Abdulƙadir ya ce neman adalci ne ya sa ƙasashen Afirkan ke kiraye-kirayen samun wakilcin.

''Babu yadda za a yi ƙaramar ƙasa a Turai kamar Birtaniya da Faransa - waɗanda ba su da yawan jama'a kamar Najeriya da wasu ƙasashen Afirka - a ce suna da wakilci a kwamitin, amma duk yawan jama'ar Afirka ba ta da wakilci'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa babban dalilin da ya sa ƙasashen Afirka ke son samun kujera a kwamitin shi ne yawan al'ummarsu.

''Baya ga wannan suna kuma son samun wakilci ne kan al'amuran da suka shafi duniya'', in ji masanin diplomasiyyar ƙasashen.

Sai dai wasu na cewa ai lokacin da aka kafa majalisar mafi yawan ƙasashen Afirka na ƙarƙashin mulkin mallaka.

To amma Farfesa Tukur Abdulƙadir ya ce hakan ba zai zama hujja ba, ai yan zu an gama mulkin mallakar, don haka babu dalilin hana wasu ƙasashen shiga kwamitin.

Najeriya ta cancanci samun kujerar?

Najeriya ta ɗauki shekaru da dama tana kiraye-kirayen samun kujerar wakilci a kwamitin tsaron na MDD.

Lamarin da ya sa wasu ke ganin ƙasar ta cancanci samun kujerar da ta jima tana neman a ba ta a duk lokacin da ta halarci babban taron na MDD.

Sai dai Farfesa Tukur Abdulƙadir ya ce a halin da ake ciki a yanzu Najeriya ba ta cika sharuɗɗan samun kujerar dindindin a kwamitin tsaro ba.

''Idan ana maganar yawan al'umma da tasirinta a Afirka za a iya cewa ta cantanta, amma a tsarin shugabanci da diplomasiyya ba ta kai matakin da ake buƙata ba'', in ji malamin jami'ar.

Ya ci gaba da cewa bayanan da ake nunawa shi ne har yanzu akwai sojojin Amurka a ƙasar nan, kuma sun shigo ƙasar nan ba tare da an kai batun gaban majalisun dokokin ƙasar nan domin su amince da hakan ba.

''Har yau Najeriya ba ta taka rawar da ya kamata ta taka a siyasar duniya da Afirka, kada mu manta da irin matakan da ta ɗauka da ba su dace da diplomasiyya ba a lokacin da aka samu juyin mulki a Nijar'', in ji shi.

Ya ce ire-iren waɗannan kura-kurai na daga cikin abubuwan da za su hana Najeriya samun wannan dama.

Masanin diplomasiyyar ya kuma ce wani dalilin da zai hana Najeriya samun wannan dama shi ne yadda ake zarginta da kasance ƴar amshin shatan wasu manyan ƙasashen Turai.

Me ya sa samun kujerar ke da wahala?

Ƙasashe da dama sun jima suna neman kujerar, amma har yanzu babu wadda ta samu wannan dama.

Farfesa Tukur Abdulƙadir ya ce tsari ne da aka gina tun farko da tsauri ta yadda zai yi wa sauran ƙasashen duniya wahala su samu damar shiga.

''Misali a yau ƙasa kamar Japan ko Indiya, wadda ta fi kowace ƙasa yawan al'umma a duniya a ce ba ta da kujera a kwamitin tsaron, haka ƙasar Masar irin gudunmowar da ta bayar a shekaru fiye da 50 na baya, amma wai a ce ba su da wakilci, wannan ka san da gayya aka yi'', in ji shi.

Masanin diplomasiyyar ya kuma ambaci ƙasashe irin su Brazil da Algeriya da irin gudunmowar da ya ce sun bayar a tsaron wasu ƙasashen duniya.