Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa EFCC ta sake ayyana neman Abdulrasheed Maina ruwa a jallo?
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta sake ayyana tsohon shugaban Kwamitin Gyaran Tsarin Fansho (PRTT), Abdulrasheed Maina, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.
Wannan na zuwa ne watanni kaɗan bayan da Maina ya kammala zaman gidan yari na shekara takwas da aka yanke masa.
A wata sanarwa da EFCC ta fitar ranar Laraba 23 ga Satumban 2026, hukumar ta ce tana neman Maina ne dangane da zargin karɓar kadarorin da ake zargin an samo su ta haramtacciyar hanya.
Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya buƙaci duk wanda ke da sahihin bayani kan inda Maina yake da ya kai rahoto ofishin hukumar mafi kusa.
Wannan ba shi ne karo na farko da Maina ke fuskantar irin wannan matsala da EFCC ba.
A shekarar 2015, hukumar ta ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo domin ya yi bayani kan rawar da ake zargin ya taka a wasu kwangilolin tantance masu karɓar fansho ta hanyar amfani da fasahar bayanan halittu (biometric contracts).
Har ila yau, EFCC ta zarge shi tare da tsohon Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayyar Najeriya, Steve Oronsaye, da wasu mutane biyu da almundahanar sama da Naira biliyan biyu na kuɗaɗen fansho.
Kafin ya zama shugaban Kwamitin Gyaran Tsarin Fansho (PRTT), Maina ya yi aiki na tsawon shekaru a Ofishin Fansho na Hukumar Kwastam, da Shige da Fice da Gidajen Yari (CIPPO).
A shekarar 2010 ne aka naɗa shi shugaban PRTT, inda ya jagoranci kwamitin har zuwa shekarar 2013.
Sai dai tun daga wannan lokaci ya kasance cikin jerin mutanen da ke fuskantar bincike da tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa.
Tsoffin tuhume-tuhumen da ya fuskanta
A watan Nuwamban shekarar 2021, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa Maina hukuncin daurin shekara takwas a gidan yari bayan ta same shi da laifin almundahanar kuɗi.
Alƙalin da ya shari'ar, Mai Shari'a Okon Abang, wanda ya yanke hukuncin a ranar Litinin, ya ce Mista Maina ya wawure sama da naira biliyan biyu na kuɗaɗen fansho.
Kotun ta ce masu gabatar da ƙara daga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) sun gabatar da kwararan hujjoji ta hannun shaidu da suka tabbatar ba tare da wata shakka ba cewa Maina ya aikata laifin almundahanar kuɗi har naira miliyan 171,099,000.
Kotun ta kuma ce Maina ya umarci ma'aikatan bankin Fidelity su buɗe masa asusun banki ba tare da aiwatar da matakan tantancewa da suka dace ba.
Haka kuma kotun ta ce ya ɓoye kansa a matsayin mai sa hannu a wasu asusun ajiya da aka buɗe a bankunan UBA da Fidelity, inda ya yi amfani da sunayen 'yan uwansa ba tare da saninsu ba.
A watan Oktoban shekarar 2019, wata babbar kotun tarayya ta bayar da umarni cewa tsohon shugaban kamitin fanshon, Maina, ya koma gidan yari.
A lokacin, EFCC ta kai tsohon shugaban kotu kan tuhume-tuhume 12, amma bayan an karanta masa su, Maina ya musanta aikata laifukan.
EFCC ta gurfanar da Maina da ɗansa a gaban kotu kan zargin damfara da ta kai naira biliyan 100.
A ranar 22 ga Oktoban 2019, Mai Shari'a Folasade Giwa-Ogunbanjo ta babbar kotun tarayya ta umarci Maina da ya miƙa kadarori 23 da aka gano suna da alaƙa da shi.
Wasu daga cikin kadarorin sun haɗa da gidaje, da kamfanoni da ke jihohin Abuja, da Kaduna, da Borno da Nasarawa.
A yayin da ake ci gaba da shari'ar, ɗansa Faisal Maina ya musanta aikata laifukan guda uku da suka shafi almundahanar kuɗi.
Alƙalin da ke sauraron ƙarar, Mai Shari'a Okon Abang, ya bayar da umarnin a tsare shi, har sai an fara sauraron shari'arsa.
A shekarar 2020 kuma, Maina ya faɗi a kotu.
Tsohon shugaban hukumar fansho ya yanke jiki ya faɗi ne yayin da lauyansa, Anayo Adibe, ke gabatar da jawabi a gaban kotu.
A lokacin, gwamnatin Najeriya na bincikarsa, kan tuhume-tuhume 12 da suka haɗa da zamba da almundahanar kuɗi.
A ranar 3 ga Disamban 2020, wani shaida a shari'ar Abdulrasheed Maina ya shaida wa babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa tsohon shugaban hukumar fanshon ya sayi kadarori a Dubai da Amurka, da kuma wata kadara a Jabi da ke Abuja wadda darajarta ta kai dala miliyan biyu.
Takaitaccen tarihin lamarinsa
2010: Aka naɗa shi shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Gyaran Tsarin Fansho.
2012: Aka fara zarginsa da cin hanci da rashawa.
2013: Aka sallame shi daga aikin gwamnati.
2015: EFCC ta saka sunansa cikin jerin waɗanda ake nema ruwa a jallo.
2015: Rahotanni suka ce ya tsere zuwa Dubai.
2017: Aka naɗa shi mukaddashin Daraktan Albarkatun Ma'aikata a Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida.
23 ga Oktoban 2017: Shugaba Muhammadu Buhari ya sake sallamarsa daga aikin gwamnati.
Tarihin rayuwarsa
An haifi Abdulrasheed Maina a ƙaramar hukumar Biu da ke jihar Borno.
Ya auri Laila Maina, kuma suna da yara. Ɗaya daga cikinsu, Faisal Maina, ya samu hukuncin zaman gidan yari na shekara 14 kan laifukan da suka shafi halasta kuɗaɗen haram.
Maina ya shahara ne bayan ya zama shugaban Kwamitin Gyaran Tsarin Fansho tsakanin shekarun 2010 zuwa 2013, kafin ya shiga jerin manyan jami'an gwamnati da suka fuskanci zarge-zargen almundahanar kuɗaɗen fansho a Najeriya.