Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Aikin wutar lantarkin Mambilla da muhimmancinsa ga Najeriya
A makon jiya ne Najeriya ta samu gagarumar nasara a wata kotun sulhu ta ƙasa da ƙasa da ke ƙarkashin International Chamber of Commerce (ICC) da ke birnin Paris na ƙasar Faransa.
Kotun ta yi watsi da buƙatun kamfanin Sunrise Power and Transmission Company Limited na neman biliyoyin daloli kan aikin samar da wutar lantarki na Mambilla Hydroelectric Power Project.
Wannan hukunci ya kawo ƙarshen ɗaya daga cikin manyan matsalolin shari'a da suka jima suna hana aiwatar da aikin da ake sa ran zai taimaka wajen magance matsalar lantarki a Najeriya.
Wannan ya sa aka fara waiwaye kan tarihin tashar wutar, da tsaikon da aka samu da ma ko nasarar da ƙasar ta samu za ta taimaka mata wajen tabbatar da aiwatar da aikin da kuma samar da wutar da ake buƙata daga aikin.
Asalin aikin Mambilla
An fara tunanin aikin Mambilla ne tun shekarun farko na ƙarni na 21 domin samar da babbar tashar lantarki ta ruwa a jihar Taraba.
Da farko an tsara aikin ne domin samar da megawatt 3,050 na lantarki, amma daga baya aka sake fasalta shi zuwa kusan megawatt 3,960 kafin a ƙara rage shi zuwa tsakanin megawatt 1,500 zuwa 1,525 domin a samu sauƙin samun tallafin kuɗi daga masu zuba jari da cibiyoyin bayar da lamuni.
An daɗe ana kallon aikin Mambilla a matsayin mafi girman aikin samar da lantarki ta hanyar ruwa a Najeriya.
A bisa yadda aka tsara shi, idan aka kammala shi, zai ƙara yawan wutar lantarkin da ake samarwa tare da rage dogaro da janareto da man dizal da miliyoyin ƴan Najeriya ke amfani da su saboda rashin wadataccen lantarki.
Sai dai an yi ta samun tsaiko da kwan-gaba-kwan-baya a aikin, lamarin da ya sa aikin ya tsaya cak.
Yadda rikicin ya fara
Rikicin ya samo asali ne tun shekara ta 2003 lokacin da aka danganta kamfanin Sunrise da aikin Mambilla. Daga baya gwamnati ta sauya tsarin gudanar da aikin tare da shigar da wasu kamfanoni, lamarin da ya haifar da taƙaddama kan ko an bi ƙa'ida wajen cire kamfanin Sunrise kamar yadda aka yi yarjejeniyar da aka yi da shi tun a farko.
Tsohon babban lauyan Najeriya, Michael Aondoakaa, ya taɓa ba da shawarar cewa a sasanta da Sunrise saboda akwai yiwuwar gwamnati ta fuskanci ƙalubale a game da shari'ar.
Haka kuma a shekarar 2012 gwamnatin tarayya ta shiga wata yarjejeniya da Sunrise da kamfanin Sinohydro duk a ƙoƙarin warware matsalar.
Sai dai daga bisani an shiga kotu, inda Kamfanin Sunrise ya ce yana da haƙƙin samun diyyar dala biliyan 2.7 tare da ƙarin kuɗin ruwa saboda dakatar da ci gaban aikin. Baya ga haka, ya nemi biyan dala miliyan 680 bisa wata yarjejeniyar sulhu da aka yi a baya.
Ta a ce Najeriya ta yi rashin nasara a shari'ar, jimillar kuɗin da za ta biya sun kai sama da dala biliyan 3.38, adadin da masana ke cewa zai yi matuƙar tasiri ga tattalin arzikin kasar.
Bayan hukuncin kotun, an samu muhawara kan rawar da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami, ya taka a rikicin.
Ofishinsa ya bayyana cewa ba a zamaninsa aka fara rikicin ba. A cewarsa, duk tattaunawar sasantawa da aka yi ta biyo bayan umarnin gwamnati da umarnin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na neman hanyar warware taƙaddamar cikin lumana.
A wata sanarwa da ofishin ya fitar, sun bayyana cewa a shekarar 2019 an yi tattaunawar sulhu inda Sunrise ya fara neman dala miliyan 500, gwamnatin tarayya ta bayar da tayin dala miliyan 100, sannan daga bisani aka cimma matsaya kan dala miliyan 200 a matsayin sulhu.
Ya ce Shugaba Buhari ya ƙi amincewa da biyan kuɗin, yana mai cewa gwamnati ba ta da damar biyan dala miliyan 200.
Malami ya ce bayan ƙin amincewar Buhari, ya umarci lauyoyin gwamnati su ƙalubalanci duk wani yunƙuri na Sunrise na tilasta wa Najeriya biyan kuɗaɗen.
Malami ya musanta zarge-zargen samunsa da rashawa, yana cewa bai taɓa karɓar kuɗi ko wata alfarma daga kamfanin ba.
Ya kuma jaddada cewa hukuncin kotun sulhu ba hukuncin laifi ba ne, kuma ba a gurfanar da shi a wata kotun hukunta masu aikata laifi ba.
Ya ce idan akwai zargin aikata laifi, to ya kamata a bi hanyoyin shari'a na daban domin bincike da hukunci.
Martanin Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana hukuncin a matsayin babbar nasara ga Najeriya. Ya ce kotun ta yi watsi da dukkan buƙatun Sunrise kuma ta kare Najeriya daga abin da ya kira "iƙirarin karɓar kuɗaɗen da ba su dace ba."
Tinubu ya yaba wa Ma'aikatar Shari'a ƙarƙashin Lateef Fagbemi, lauyoyin da suka kare Najeriya, da kuma tsoffin shugabanni Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari waɗanda suka bayar da shaida a yayin shari'ar.
Ya kuma ce hukuncin ya kawar da mafi girman cikas na shari'a da ya hana aikin Mambilla ci gaba tsawon shekaru.
A nasa ɓangare, mai ba shugaba Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi bayani kan wasu zarge-zargen da suka taso daga shari'ar.
Onanuga ya ce rahotannin kotun sun danganta Atiku da wata baɗakala da ake zargin an biya tsohuwar matarsa Jennifer Douglas dala 500,000 a lokacin da ake gudanar da harkokin kwangilar Mambilla a shekarar 2003.
Sai dai har zuwa yanzu babu wata kotun laifuka da ta same Atiku da laifi kan wannan batu.
Rikicin Mambilla ya shafe sama da shekaru 20 yana yawo tsakanin gwamnatoci daban-daban, ministoci, ƴan kasuwa da kotunan ƙasa da ƙasa.
Hukuncin ICC na Paris ya ba Najeriya damar kauce wa asarar maƙudan kuɗaɗe tare da buɗe sabon babi ga aikin da ake sa ran zai taimaka wajen magance matsalar lantarki.
Sai dai duk da haka, ana ganin muhawara kan yadda aka gudanar da kwangilar tun daga 2003, da kuma zarge-zargen da suka taso daga shari'ar, na iya ci gaba da kasancewa muhimmin batu a siyasar Najeriya da kuma tattaunawar jama'a a nan gaba.