Ƙungiyoyin Premier na rububin Llorente, Juventus na harin Tyrick Mitchell

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester City da Liverpool da Chelsea na zawarcin ɗan wasan tsakiyar ƙasar Spain Marcos Llorente, mai shekara 31, wanda har yanzu bai yanke hukunci kan makomarsa a Atletico Madrid ba. (TeamTalk)

Har ila yau, waɗannan kungiyoyi uku na gasar Premier League na sa ido kan ɗan wasan bayan Inter Milan da Italiya Alessandro Bastoni, mai shekara 27, wanda Barcelona ita ma ke zawarcinsa. (TeamTalk)

Brentford na tattaunawa da ɗan wasanta mai buga gefen fili Kevin Schade kan sabon kwantiragi na dogon zango, yayin da ake samun ƙaruwar sha'awar ɗaukar ɗan wasan na Jamus daga ƙungiyoyi da suka haɗa da Arsenal da Liverpool. (Sky Sports)

Brighton na shirin tsawaita kwantiragin ɗan wasan tsakiyar ƙasar Sweden Yasin Ayari, mai shekara 22, a cikin makonni masu zuwa. (Football Insider)

Liverpool na nazarin yiwuwar mayar da yarjejeniyar aro ta ɗan wasan baya na Uruguay, Ronald Araujo (mai shekara 27), daga Barcelona zuwa ta dindindin. (Mundo Deportivo)

An bai wa Juventus damar ɗaukar ɗan wasan baya na Crystal Palace, Tyrick Mitchell (mai shekara 27), yayin da Liverpool da Manchester United suma ke nuna sha'awar ɗan wasan na Ingila. (Tuttosport)

Real Madrid na sha'awar ɗan wasan baya na Stuttgart kuma ɗan tawagar Jamus ta ƴan ƙasa da shekara 21, Finn Jeltsch (mai shekara 20). (AS)

Nottingham Forest da Aston Villa sun yi tambayoyi game da yiwuwar ɗaukar matashin ɗan wasan Faransa, Valentin Atangana. A yanzu haka, ɗan wasan mai shekara 21 yana buga wa ƙungiyar Al-Ahli ta Saudiyya wasa. (L'Equipe)

Daraktan harkokin wasanni na Newcastle, Ross Wilson, na jagorantar wani sabon tsarin ɗaukar ƴan wasa wanda zai sa ƙungiyar ta ba da fifiko kan matasa masu hazaƙa da kuma sabon tsarin cinikin ƴan wasa. (The I)