Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 25/09/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. Atiku ya naɗa El-Rufai cikin mambobin kwamitin yaƙin zaɓensa

    Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya amince da kafa kwamitin yakin neman zabensa na shugaban kasa, wanda zai kasance ƙarƙashin jagorancin Kashim Ibrahim-Imam sai Nasir El-Rufai a matsayin mataimakinsa.

    Naɗin na zuwa ne yayin da El-Rufai ke tsare a hannun hukumomi bisa tuhume-tuhumen da gwamnati ke yi masa.

    Daraktan yaɗa labarai na kwamitin, Phrank Shaibu, wanda kuma shi ne babban mataimaki na musamman ga Atiku kan harkokin sadarwa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

    Sanarwar ta ce an tsara kwamitin ne bisa la'akari da halin tattalin arzikin da 'yan Najeriya ke fuskanta, ciki har da tashin farashin kayan masarufi da tsadar sufuri da kuma raguwar kudaden shiga.

    An nada Sanata Austin Akobundu a matsayin babban daraktan yakin neman zaben, wanda zai jagoranci aiwatar da dabarun kwamitin cikin tsari.

    Haka kuma, mataimakan babban darakta shida za su kula da harkokin gudanarwar kwamitin, inda za su yi aiki tare da daraktoci 30 da aka ɗorawa nauyin kula da fannoni daban-daban.

    Dele Momodu ne zai shugabanci harkokin yaɗa labarai da sadarwa yayin da Dino Melaye kuma zai jagoranci sashen tuntuɓa.

    Shi kuma Mohammed Hayatudeen zai jagoranci kwamitin tsara manufofi tare da Farfesa Mohammed Sagagi da wasu mambobi kamar Farfesa Kingsley Moghalu.

  2. Dangote, Habasha da Djibouti za su gina bututun mai na dala miliyan 600

    Attajirin Afirka Aliko Dangote da gwamnatocin Habasha da Djibouti sun cimma yarjejeniyar gina bututun man fetur da rumbun ajiyarsa da za su haɗa ƙasashen biyu, a wani aiki da zai laƙume dala miliyan 600.

    Aikin zai haɗa da gina bututun mai mai tsawon kilomita 120 da zai haɗa tashar jiragen ruwa ta Damerjog a Djibouti zuwa cibiyar rarraba mai da ke Dewele a Habasha. Haka kuma, za a gina rumbunan da za su iya ɗaukar kusan lita miliyan 400 na man fetur.

    Ana sa ran fara aikin cikin watanni 18.

    Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya ce bututun zai rage lokacin da ake ɗauka wajen jigilar mai daga tashar jiragen ruwa ta Djibouti zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha, daga kwanaki biyar zuwa kwana ɗaya.

    A matakin farko, za a riƙa jigilar muhimman albarkatun man fetur, ciki har da man jirgin sama, dizal da fetur.

    Da yake jawabi a bikin ƙaddamar da aikin, Dangote ya ce aikin zai ƙarfafa makamashi a Habasha tare da inganta tsarin samar da man fetur na ƙasar.

  3. Fashewar jirgi mara matuƙi ta halaka sojin Isra'ila biyu a Gaza

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce sojojinta biyu sun mutu a arewacin Gaza bayan da jirgi mara matuƙi da suke aiki da shi ya fashe bisa kuskure.

    Jirgin ya tarwatse ranar Alhamis a sansanin sojoji amma ba a san dalilan faruwar hakan ba.

    Sojojin sun ɗauko jirgin mara matuƙi, kwatsam kuma sai ya fashe.

    Rundunar sojin ta dakatar da amfani da ƙananan jirage mara matuƙa da ke ɗauke da abubuwan fashewa.

  4. An samu ƙaruwar masu fama da talauci a Argentina

    Adadin 'yan kasar Argentina da ke fama da talauci ya karu a bana, yayin da gwamnatin shugaba Javier Milei ke kokarin shawo kan hauhawar farashin kayayyaki, abin da ya kasance daya daga cikin muhimman alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zabe.

    A yanzu, kusan mutum daya daga cikin kowane mutum uku a kasar yana fama talauci wanda ke nuna karuwar kashi hudu cikin dari.

    Masu suka sun ce tsare-tsaren tattalin arzikin shugaban kasar da kuma rage shirye-shiryen tallafawa al'umma da ya yi sun kara ta'azzara matsalar matsin rayuwa.

    Argentina ta ga karuwar shigo da kayayyaki daga waje, wanda hakan ya haifar da asarar ayyukan yi a masana'antun cikin gida

  5. An hana kafafen yaɗa labarai shiga White House duk da umarnin alƙali

    'Yan jarida daga gidajen talabijin din CNN da MS NOW sun bayyana cewa an hana su shiga wurin liyafar cin abincin daren da aka shiryawa shugaban na China, duk da hukuncin da wani alkali ya yanke na cewa a bar su su koma Fadar White House.

    Gwamnatin Trump ta ce hukuncin ba ya nufin suna da ƴancin shiga su kuma bayar da rahoto kan duk wani taron da ake gudanarwa.

    Wakiliyar BBC ta ce Shugaba Trump ya fara hana kafafen yada labaran shiga Fadar White House a daren Juma'ar da ta gabata ne, inda ya zarge su da yada "labaran karya," da kuma rashin yi wa gwamnatinsa adalci a rahotanninsu.

    Wani alkalin kotun tarayya ya yanke hukuncin mayar da takardun izinin shiga fadar White House ga 'yan jaridar nan take na tsawon kwanaki 14, yayin da kafofin yada labaran ke ci gaba da kalubalantar lamarin a gaban kotu.

  6. Amurka da China sun cimma matsaya kan batutuwa da dama - Xi

    Shugaban Amurka Donald Trump ya karbi bakuncin shugaban China, Xi Jinping, da matarsa ​a wata liyafar cin abinci ta musamman a Fadar White House, inda ya bayyana su a matsayin mutanen arziki.

    Mista Trump ya tabbatar da cewa kasashen biyu suna da "tsare-tsare daban-daban" -- amma ya ce suna samun fahimtar juna fiye da kowane lokaci a shekarun baya.

    Xi ya ce dole ne kasashen biyu su “tafiyar da al’amuransu a matsayin manyan kasashe masu ɗaukar nauyi domin biyan muradun al’umominsu”, yayin da Trump ya yi fatan samun makoma ta “jituwa, zaman lafiya da nasara” ga kasashen biyu.

    Mista Xi ya bayyana cewa, a yayin tattaunawar da suka yi ranar Alhamis, sun cimma matsaya kan batutuwa da dama, ba tare da ya yi wani karin bayani ba.

    Wakilin BBC ya ce ba a nuna jawaban - da kuma yawancin abubuwan da aka gudanar lokacin ziyarar a gidajen talabijin na Amurka da sauran wurare ba, sakamakon takunkumin da Shugaba Trump ya sanya wa kafofin yada labarai guda uku a makon da ya gabata.

  7. Salam Alaikum!

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye da BBC Hausa ke kawo maku a kullum, barka da hantsi.

    Da fatan muna cikin ƙoshin lafiya. Kamar kodayaushe, za mu ci gaba da wallafa labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya musamman Najeriya da ƙasashe maƙwabta.

    Sai ku kasance tare da mu.