Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zazzafan martani da shugaban Iran ya yi wa Amurka a taron UNGA
A jawabinsa a taron Majalisar Ɗinkin Duniya, Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa Iran ba za ta taɓa "miƙa wuya" ba, amma a shirye take ta cimma matsaya ta diflomasiyya domin kawo ƙarshen rikicin.
Bayan kusan watanni bakwai na yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran, Mista Pezeshkian, yayin da yake mayar da martani kan barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na "wargaza" Jamhuriyar Musulunci ta Iran idan ba a cimma yarjejeniya nan take ba.
Ya ce: "Ya kamata ya sani cewa takunkumi, ƙara matsin lamba da kuma amfani da ƙarfin iko za su ƙara ƙarfafa juriyar al'ummar Iran ne kawai."
Ya kuma jaddada cewa duk wata yarjejeniya da za a yi dole ta ƙunshi kawo ƙarshen shingen da Amurka ta ƙaƙaba wa jiragen ruwa da tashoshin jiragen ruwa na Iran.
Ya ce: "Ba zai yiwu kowa ya ci moriyar albarkatun mashigar Hormuz, mu kuma a hana mu samun damar yin amfani da ita ba."
Mashigar Hormuz, wadda a kullum kusan kashi ɗaya bisa biyar na jigilar mai da iskar gas ta duniya ke ratsa cikinta, ta kusan kasance a rufe tun bayan ɓarkewar yaƙin a ƙarshen watan Fabrairu, sakamakon hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da Iran ke kai wa jiragen kasuwanci, da kuma shingen da Amurka ta kakaba.
'Iran babu gudu babu ja da baya'
Pezeshkian ya ce: "Babu wani a wannan yankin da zai kasance cikin tsaro shi kaɗai. Ko dai mu gina tsaro tare, ko kuma mu fuskanci rashin tsaro tare."
Shugaban na Iran ya kuma soki yadda ƙasashen duniya suka tafiyar da al'amura game da Iran. Da yake magana kan Isra'ila, ya ce:
"Bam ɗin nukiliya yana Isra'ila, amma masu sa ido suna Iran."
Mista Pezeshkian ya ce: "Isra'ila tana da bam ɗin nukiliya da kanta, amma ba a taɓa duba ta ba. Amma suna duba Iran. Isra'ila tana kisa, amma Iran ce ake kakaba wa takunkumi."
Shugaban Iran ya ƙara da cewa Tehran ba za ta ja da baya daga shirinta na amfani da makamashin nukiliya don dalilai na farar hula ba.
"Shugaban Amurka ya bayyana mu a matsayin ƴanta'adda. Amma a zahiri mu ne aka yi wa ta'addanci," in ji shugaban na Iran.
Pezeshkian ya ɗaga hoton Khamenei
Daga nan sai ya ɗaga hoton marigayi Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka kashe shi a wani hari da aka kai gidansa lokacin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da farmaki haɗin gwiwa a ƙarshen watan Fabrairu.
Haka kuma ya gabatar da hotunan wasu daga cikin fararen hula sama da 175 da hukumomin Iran suka ce an kashe a hare-haren makamai masu linzami da aka kai wata makarantar firamare a Minab da kuma wani filin wasanni a Lamerd a wannan rana.
Kashi biyu bisa uku na waɗanda suka mutu yara ne, kamar yadda hukumomin Iran suka bayyana.
Amurka ta musanta kai hari a Lamerd, kuma ta ce har yanzu tana binciken abin da ya faru a Minab.
Pezeshkian ya ce:
"Mutanenmu marasa laifi sun kasance makasudin hare-hare da ta'addancin da aka kakaba wa ƙasarmu. Kuma mun kare kanmu da dukkan ƙarfin da muke da shi."
Kausasan kalaman Trump kan Iran
Tun da farko, a jawabinsa a ranar farko ta taron Majalisar Ɗinkin Duniya, Donald Trump ya ce yana fuskantar "babban mataki" ko dai a cimma yarjejeniya da Iran a ba ta damar sake gina ƙasarta, ko kuma a "wargaza" ta.
Iran da Amurka sun cimma wata yarjejeniya ta farko a watan Yuni domin kawo ƙarshen yaƙin da kuma sake buɗe mashigar Hormuz, amma yarjejeniyar ta rushe cikin makonni bayan da Iran ta sake kai hare-hare kan jiragen ruwa, sannan Amurka ta sake sanya shingen ruwa.
A ranar Talata, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da Jakadan Amurka Steve Witkoff sun gudanar da tattaunawar kai-tsaye ta bayan fage, wadda Qatar ta shiga tsakani, a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya da ke gudana a New York.
Steve Witkoff ya bayyana fatan cewa tattaunawar za ta kasance "mai ma'ana kuma mai cike da kyakkyawar fata", yana mai cewa masu shiga tsakani za su ci gaba da ƙoƙarinsu.
Sai dai kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce tattaunawar ba ta ƙunshi "wani sabon batu ba", yana mai cewa Mista Araghchi ya jaddada sharuɗɗan Iran, ciki har da kawo ƙarshen shingen da Amurka ta sanya da kuma sakin kadarorin Iran da aka ƙwace.
A halin da ake ciki, wani babban jami'in Iran ya shaida wa Reuters a ranar Laraba cewa Iran da Amurka har yanzu suna da babban saɓani kan yadda za a kawo ƙarshen yaƙin, amma ya ce dole ne a ci gaba da tattaunawar diflomasiyya.
Jami'in, wanda ya yi magana ba tare da bayyana sunansa ba, ya ce Tehran na nazarin martanin Washington kan shawarwarin zaman lafiya da Iran ta gabatar, waɗanda suka fi mayar da hankali kan ɗage shingen ruwan da Amurka ta kakaba wa tashoshin jiragen ruwa na Iran da kuma sake buɗe mashigar Hormuz.
Jami'in ya ƙara da cewa: "Har yanzu akwai bambance-bambance masu yawa tsakanin matsayen Iran da Amurka, amma ana ci gaba da diflomasiyya."
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio shi ma ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa cimma yarjejeniya da Iran zai buƙaci aiki mai wahala na tsawon lokaci, inda ya ƙara da cewa Donald Trump har yanzu yana da zaɓin amfani da ƙarfin soji.