Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jihohi 7 da suka fi arziƙin ma'adinai a Najeriya
- Marubuci, Imam Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- Aiko rahoto daga, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Najeriya na daga cikin ƙasashen duniya da Allah Ya huwace wa albarkar ma'adinai iri daban-daban a karkashin kasa.
Duk da cewa man fetur ya daɗe yana zama tushen mafi yawan kuɗaɗen shiga na ƙasar, masana tattalin arziki da masana harkokin ma'adinai na ci gaba da jaddada muhimmancin amfani da dimbin ma'adinan da ke kwance a jihohi daban-daban domin bunƙasa tattalin arziki.
Rahotanni sun nuna cewa Najeriya na da nau'ikan ma'adanai sama da 40 da ake samu a wurare fiye da 500 a faɗin ƙasar.
Daga Arewa zuwa Kudu, akwai jihohin da suka yi fice wajen yawan ma'adinan da suke da su da kuma muhimmancin waɗannan albarkatu ga ci gaban masana'antu.
Kan haka ne muka tuntuɓi Injiniya Zakari Adamu, Kodineta mai kula da jihohin arewa ta takiyar Najeriya a hukumar ma'adinan ƙasar, wanda kuma ya lissafo mana jihohin da ke kan gaba a arzikin ma'adinai a ƙasar, amma banda man fetur da iskar gas.
Kogi
Jihar Kogi da ke yankin arewa ta tsakiyar ƙasar ce kan gaba wajen arzikin ma'adinai a cewar Injiniya Zakari Adamu.
Wurin Itakpe da ke jihar na ɗaya daga cikin manyan ma'adanan ƙarafa a Najeriya.
Baya ga ƙarfen tama, jihar na da kwal (coal), da limestone, da dolomite, da feldspar da marble da sauransu.
Wannan ne ma babban dalilin da ya sa aka kafa masana'antar siminti ta Obajana a jihar, kamar yadda masanin ma'adinan ya bayyana.
Masana sun yi imanin cewa idan aka farfaɗo da masana'antar Ajaokuta tare da inganta harkar hakar tama a Itakpe, Kogi za ta zama ɗaya daga cikin jihohin da za su fi samar da kuɗaɗen shiga daga bangaren ma'adinai.
Nasarawa
Jihar Nasarawa mai maƙwabtaka da Kogi na ɗaya daga cikin jihohin da suka fi tara nau'o'in ma'adanai a Najeriya, a cewar masanin.
Saboda ɗimbin albarkatun da ake samu a cikinta, mutane da dama suna yi mata laƙabi da "Gidan Ma'adanai''
A jihar akwai ma'adanai kamar zinariya, da baryte, da tantalite, da columbite, marble, da limestone, da kaolin da gemstones iri-iri da kuma Lithium.
''Saboda yawan ma'adinin Lithium da ke jihar akwai kamfanonin sarrafa ma'adinin a jihar har guda biyu manya da ke aiki'', kamar yadda Injiniya Zakari ya bayyana.
Haka kuma wasu bincike sun nuna cewa kusan kowane yanki na jihar yana ɗauke da wani nau'in ma'adani.
Plateau
Plateau na daga cikin jihohin da tarihin haƙar ma'adanai ta fi tsawo a Najeriya.
Tun zamanin Turawan mulkin mallaka jihar ta zama shalkwatar sarrafa ma'adinai a Najeriya, a cewar babban kodinetan ma'adinan na arewa ta tsakiyar Najeriya.
Tsawon shekaru da dama, ma'adanan tin na Plateau sun kasance daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga Najeriya.
''Kusan ka iya cewa babu kalan ma'adinin da ba za ka samu ba wannan jiha'', in ji shi.
Duk da cewa harkar ta ragu idan aka kwatanta da shekarun baya, masana na ganin jihar na da damar sake zama babbar cibiyar hakar ma'adanai idan aka samar da sabbin fasahohi da zuba jari.
Zamfara
Jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin ƙasar ce ta huɗu a yawan albarkatun ma'adinai a Najeriya.
A cewar Injiniya Zakari, Zamfara na da nau'o'in ma'adinai da dama, amma wanda ta fi shahara da shi shi ne zinare.
''Ka iya cewa ƙananan hukomomi da dama na da ɗimbin arzikin wannan ma'adini a faɗin jihar'', in ji shi.
Sai dai ya a halin yanzu ayyukan ƴanbindiga na kawo tsaiko wajen haƙar ma'adinan jihar.
Masana tsaro sun jima suna alaƙanta ayyukan ƴanbindiga da harkar haƙar ma'adinan jihar.
Inda wasu ma ke ganin ma'adinan na daga cikin abubuwan da suka janyo ayyukan ƴanbindiga a jihar.
Ondo
Jihar Ondo da ke yankin kudu maso yammacin ƙasar na daga cikin jihohin da suka fi arzikin ma'adinan karƙashin ƙasa, kamar yadda Injiniya Zakari ya bayyana.
''Ondo na na da ma'adinin bitimin, mai kama da coal, wanda makamashi ne, inda ma jihar ta fi kowane wuri arzikin wannan ma'adini a faɗin duniya'', in ji shi.
Ogun
Jihar Ogun mai makwabtaka da ondo ce a matsayi na shida cikin jerin jihohin Najeriya da suka fi arzikin ma'adinai a cewar Injini Zakari Adamu.
''Ogun na da arzikin ma'adinin Limestone, wanda ya zarta na kowace jiha a Najeriya'', in ji shi babban jami'in na ma'aikatar ma'adinan ƙasar.
Baya ga limestone, Ogun na da granite da silica da clay da wasu albarkatun da ake amfani da su wajen gine-gine da masana'antu.
Saboda haka jihar na taka muhimmiyar rawa wajen samar da kayan gini a Najeriya.
Neja
Jihar Niger da ke yankin arewa ta tsakiyar Najeriya ce ta bakwai a arzikin ma'adinai a Najeriya a cewar, Injiniya Zakari.
''Jiha ce mai ɗimbin arzikin zinare, a ƙananan hukumomin jihar masu yawa'', in ji shi.
Haka ma ya ce akwai ma'adinai irin su talc da granite da limestone da lead da quartz.
Ya ƙara da cewa jihar na da wurare masu yawa da har yanzu ba a yi cikakken binciken albarkatun da ke cikinsu ba.