Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barazana 5 da Trump ya yi wa Iran a taron Majalisar Dinkin Duniya
Barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Iran a jawabinsa na babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 ta ɗauki hankalin shugabannin duniya.
A yayin da ya hau mumbari gaban shugabanni da wakilan ƙasashe daban-daban, Trump ya yi kalamai masu nauyi, inda ya bayyana cewa yana nazarin "babban zaɓi" tsakanin ko ya sake kai hari kan Iran ko kuma cimma yarjejeniya da ita.
Sai dai abin da ya ja hankali shi ne yadda kusan babu wani jami'in Iran da ya zauna domin sauraron jawabin nasa, yayin da wakili guda kacal daga tawagarsu ya kasance a ɗakin taron.
Trump ya ce idan rikicin da ke tsakaninsa da Iran ya ci gaba kuma aka kasa samun mafita, Amurka na da ƙarfin da za ta iya murƙushe ƙarfin sojin Iran da kuma raunana tattalin arzikinta cikin ƙanƙanin lokaci.
Shugaban na Amurka ya ce yana iya "shafe Iran daga taswirar duniya" tare da hana ta damar sake barazana ga wasu ƙasashe.
Kalaman nasa sun zo ne a yayin da rahotanni suka ce an gudanar da tattaunawar diflomasiyya tsakanin wakilan Amurka da Iran.
Ga muhimman abubuwa biyar da Trump ya faɗa kan Iran a taron na Majalisar Ɗinkin Duniya.
1. Hana Iran mallakar makamin nukiliya
Babbar manufar da Trump ya jaddada a jawabinsa ita ce tabbatar da cewa Iran ba ta taɓa mallakar makamin nukiliya ba.
A cewarsa, matsin lambar da Amurka ta sanya wa Tehran da kuma matakan da ta ɗauka sun hana Iran cimma burinta na samun irin wannan makami. Ya kuma yi iƙirarin cewa abin da ya kira "zaman lafiya ta hanyar nuna ƙarfi" ya fi sassauci ko sulhu wajen tilasta wa Iran canza halayyarta.
"Ko dai in murƙushe Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne cikin gaggawa, ba tare da ba ta damar sake kashe mutane ko lalata ƙasashe ba? Shin in tura ta zuwa hallaka ne?" in ji Trump a yayin jawabinsa.
Trump ya bayyana gwamnatin Iran a matsayin wata barazana da ta daɗe tana damun duniya, yana mai cewa abin da ke sa ta yi abin da yake ganin ya saɓa wa doka ba ƙarfin da take da shi ba ne, sai dai saboda tana cikin matsin lamba da neman mafita.
"Abin da nake so kawai shi ne Iran kada ta taɓa mallakar makamin nukiliya."
Baya ga haka, Trump ya ce yana son:
- Dakatar da hare-haren da ake kai wa jiragen ruwan dakon kaya
- Tilasta wa Iran janye duk wani shiri na mallakar makamin nukiliya
- Da kuma kawo ƙarshen abin da Amurka ke zargin Iran da yi na goyon bayan ƙungiyoyin da take kira ta'addanci.
2. Takunkumin tattalin arziki
Wani muhimmin saƙo da Trump ya aika a jawabinsa shi ne buƙatar a ƙara tsaurara wa Iran takunkumin tattalin arziki domin a ƙara mata matsin lamba.
Shugaban na Amurka ya yi kira ga ƙasashen duniya da su haɗa kai da Washington wajen ware Iran daga tsarin tattalin arzikin duniya gaba ɗaya.
"Ina kira ga dukkan ƙasashe su haɗa kai da mu wajen tabbatar da maida Iran saniyar ware ta fuskar tattalin arziki...," in ji Trump.
Ya ƙara da cew, irin wannan matsin lamba ne kaɗai zai sa gwamnatin Iran ta daina abin da Amurka ke zarginta da aikatawa, ciki har da hare-hare kan jiragen dakon kaya da kuma ci gaba da yunƙurin mallakar makamin nukiliya.
Ya kuma ce hakan zai ƙara tilasta wa Iran ta yi watsi da abin da Amurka ke zargin ta da shi na goyon bayan ƙungiyoyin da ke tayar da zaune tsaye a yankuna daban-daban.
Trump na ganin cewa idan duniya ta haɗa kai ta katse hanyoyin kasuwanci da tattalin arzikin Iran, hakan zai ƙara raunana gwamnatin ƙasar tare da tilasta mata sake duba manufofinta.
3. "Mun ragargaza Iran"
Trump ya kuma yi ikirarin cewa matakan da Amurka da ƙawayenta suka ɗauka sun raunana Iran, har ta kai matsayin da gwamnatin ƙasar ke nuna alamun tana cikin tsananin matsin lamba.
A cewarsa, matakan da Iran ke ɗauka a yankin ba alama ba ce ta nuna suna da ƙarfi, sai dai alama ce ta damuwa da rashin mafita.
"Wannan gwamnati tana aikata waɗannan abubuwa ne ba don tana da ƙarfi ko kwarin gwiwa ba, sai don mun raunana ta da kuma matsananciyar buƙata."
Trump ya ce irin wannan raunin ne ya sa Iran ta fi saurin fuskantar tasirin matsin lambar ƙasashen duniya, musamman ta fuskar tattalin arziki da diflomasiyya.
4. Iran za ta ɗanɗana kuɗarta
Trump ya gabatar da abin da ya kira zaɓi biyu ga Iran: ko dai ta rungumi yarjejeniya da Amurka, ko kuma ta ɗanɗana kuɗarta da ƙarfin soji.
A cikin jawabinsa, ya tambayi ko za a iya cimma wata yarjejeniya da za ta bai wa Iran damar sake gina kanta da farfaɗo da tattalin arzikinta.
"Shin za a cimma yarjejeniya da Iran da za ta ba ta damar sake ginawa ta zama ƙasa mafi ci gaba fiye da da?"
Sai dai a gefe guda, ya sake jaddada cewa idan ba a samu maslaha ba, Amurka na da ikon ɗaukar matakan da za su iya jefa gwamnatin Iran cikin mawuyacin hali.
Duk da tsauraran kalaman nasa, Trump ya nuna akwai damar sasantawa. Ya bayyana cewa yana ganin ana iya kai wa ga yarjejeniya da Iran, wadda har yanzu ta gagara samuwa.
Kafin jawabin nasa, ya shaida wa manema labarai cewa jami'an Amurka da na Iran sun yi wata ganawa ta kusan sa'o'i uku a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda ya bayyana a matsayin ganawa mai amfani.
5. Trump na sa ran cimma yarjejeniya da Iran bayan zaɓen Amurka
Duk da kalaman barazana da ya yi wa Iran, Trump ya nuna cewa har yanzu yana ganin akwai yiwuwar cimma yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu.
"Amma na yi imanin za mu cimma yarjejeniya nan da nan bayan zaɓe, domin babu wani dalilin da zai sa su ƙi yin hakan."
Trump ya kuma bayyana cewa jami'an Amurka sun shafe kusan sa'o'i uku suna ganawa da tawagar Iran, inda yi nuna babban wakilinsa a tattaunawar, Steve Witkoff, wanda ya halarci ganawar tare da Jared Kushner.
Bayan taron, Trump ya ce yana jin daɗin yadda tattaunawar ta gudana.
Sai dai shugaban na Amurka ya yi zargin cewa Iran na jira ta ga sakamakon zaɓukan da za a gudanar kafin ta yanke hukunci kan makomar hulɗarta da Washington.
Amma ya ce shi batun zaɓe da manufofinsa kan Iran bai dame shi ba.
"Ban ba batun zaɓe wani muhimmanci ba, kuma ba zan ba shi tasiri ba idan ya zo kan batun Iran."
Me Iran ta ce?
Har zuwa lokacin da Trump ya gabatar da jawabinsa, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Iran a Tehran da ke mayar da martani kai tsaye ga kalaman nasa.
Duk da cewa ba a ji martani kai tsaye daga Iran kan barazanar da Trump ya yi ba, daga baya kafofin yaɗa labaran gwamnatin ƙasar sun tabbatar da cewa Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya gana da wakilin Amurka na musamman kan Gabas ta Tsakiya, Steve Witkoff, a gefen taron.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce tattaunawar ta gudana ne ta hannun masu shiga tsakani daga ƙasar Qatar. A cewarsa, Iran ta bayyana sharuddan da take ganin dole ne a cika kafin a samu matsaya.