Yadda matsalar ƴanbindiga ta hana yin shuka mai tsayi a arewacin Najeriya

Gonakin kan hanya a babbar hanyar Zaria zuwa Sokoto
Bayanan hoto, Yanbindiga sun sha kai hare-hare a hanyar Funtua zuwa Gusau
    • Marubuci, Awwal Ahmad Janyau
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Matsalar tsaro musamman ma a yankin arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da tasiri da haifar da sauyi a rayuwar yau da kullum.

Ga ma'abocin bin hanyar Zaria zuwa Sokoto, wani sabon sauyi da yankin ke gani, shi ne na gajerun shukoki a daminar bana maimakon shuka mai tsayi.

Tun daga Zaria idan ka tashi, ka ratsa Funtua zuwa Gusau, fili ne kake iya gani cike da gajerun korayen tsirrai. Ana iya hango mutumin da ke can nesa.

Yankin wanda ya ƙunshi jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kaduna ya daɗe yana fama da matsalar tsaro sakamakon ayyukan ƴan fashin daji da ke kai hare-hare da shatar shanu da garkuwa da mutane domin kuɗin fansa.

Wasu alƙalumman kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited da ke nazari kan matsalolin tsaro a yankin Sahel sun nuna cewa yankin ne ya fi fuskantar hare-hare daga Fabrairun zuwa watan Maris na 2026.

Hanyar Zaria zuwa Sokoto a baya can ana bayyana ta da tarkon mutuwa - saboda rayuka da suka salwanta sakamakon hare-haren yanbindiga masu kashewa da satar mutane domin kudin fansa.

Matsalar tsaron ta tilasta ɗaukar matakai da dama kuma ɗaya daga cikin matakin shi ne haramta wa manoma shuka duk wani amfanin gona mai tsayi.

Ana zargin ƴanbindiga na fakewa cikin duhun gonaki suna yi wa matafiya da jami'an tsaro kwanton ɓauna, dalilin ɗaukar matakin da ya samar da wani sabon sauyi ga manoma.

Shuka mai tsayi na hana jami'an tsaro tsinkayar yanbindiga ko motsin su daga nesa.

Me manoma suke shukawa a yanzu?

Gonar Waken suya a Zamfara
Bayanan hoto, Tun daga Zaria da wahala ka tsinkayi masara ko karan dawa ko geru a gonakin yankin sai dai kananan shuka.

Galibi manoma da ke da gonaki gefen hanya tsakanin Kaduna zuwa Sokoto sun shuka amfanin gona ne irinsu gyada ko wake ko waken suya ko shinkafa ko kuma dankali.

Sabanin shekarun baya idan kana tafiya a wannan hanyar a wannan lokacin na tsakiyar damina za ka ga shuka mai tsayi irinsu masara da gero da dawa saboda manoman yankin sun fi noma abin da suke ci.

Tun daga Zaria da wahala ka tsinkayi masara ko karan dawa ko geru a gonakin yankin sai dai kananan shuka.

Yawanci an fi noma waken suya da gyada a gonakin watakila saboda sun fi daraja a kasuwa.

Galibi waɗannan nau'in amfanin gona irin su waken soya da gyaɗa ba su buƙatar taki, sai dai feshi.

"Ba haka muka so"

Gonar waken Suya a Zamfara
Bayanan hoto, Manoman suna noma wake da waken suya da gyaɗa da shinkafa
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wasu manoman musamman a yankin Zamfara da Katsina sun ce duk da mataki ne na tsaro amma noman tilas ne suke yi.

Manoman sun fi shuka amfanin gona da suke ci maimakon na sayarwa.

Matakin ya hana su damar shuka abincin da suka saba da shi kamar dawa da masara da gero a waɗannan yankuna.

"Kyawon manomi ka yi noman abin da za ka ci ka sha, shi za ka noma, dawa da masara da gero, mu ba haka suka so ba."

"Duk wani abu da sai ka sayar sannan ka saye abin da kake so ba zai gyara manomi ba," in ji Malam Adamu wani manomi a ƙauyen Fegin Ɗanmarke a jihar Zamfara.

Haka ma wani manomi a yankin Fegin Baza a jihar Zamfara wanda ya suka waken suya a gonarsa ya ce idan son samu ne sun fi son su shuka masara da gero da dawa.

"Dole kawai ta sa muke shuka waken soya saboda dalilin tsaro musamman yadda yanbindiga ke yi wa matafiya kwanton ɓauna," in ji shi.

Manoman sun ce da son samu ne za su a ce sun noma duka biyu, abincin da za su ci da kuma wanda za su kai kasuwa su sayar.

Dalilin ɗaukar matakin

Sabuwar hanyar Funtua zuwa Gusau
Bayanan hoto, Yanzu fili ake gani tun daga Funtua zuwa Gusau cike da gajerun korayen tsirrai. Ana iya hango mutumin da ke can nesa.

Gwamnatocin jihohin yankin da jami'an tsaro sun yin la'akari da matakin tsaro ne domin kare rayukan al'umma.

Tun a shekarar 2025, jihohin Zamfara da Katsina da jami'an tsaro suka hana masu gonakin kusa da babbar hanya shuka amfanin gona mai tsayi.

Doka ce ga duk manoman da ke da gonaki a hagu da dama a babbar hanyar Zaria zuwa Sokoto shugaka duk wani amfanin gona mai tsayi da zai iya rufe mutum da ba za a iya ganinsa.

A watannin baya jami'an tsaro sun ta shiga gonaki suna sare masara da dawa da gero ga manoman da suka saɓa umarnin.

Matakin ya shafi hana wa manomi yin shuka kusan tazarar mita 100 da babbar hanya saboda matsalar yanbindiga da ke fakewa suna kai wa mutane da jami'an tsaro hari.

Akwai kwamiti da aka kafa a Zamfara da yake kula da matakin tabbatar da dokar ga manoma.

Ko ana samun sauƙi?

Manoma na cikin waɗanda suka fi shan wahalar matsalolin tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Baya ga hana shuka a kusa da hanya, matsalar tsaro na ci gaba da shafar aikin noma kuma har yanzu ƴanbindiga na ci gaba da kai wa manoma hari a gonakinsu.

Wasu al'ummar yankin arewa maso yammaci sun ce matakin hukumomi na hana shuka mai tsayi ya sa an samu sauƙin hare-hare musamman ma a babbar hanyar da ta taso daga Zaria zuwa Sokoto.

Wasu kuma sun ce duk da matakin amma har yanzu ƴanbindigar na samun dama suna tare hanya suna kai wa ƙauyukan da ke kan babbar hanyar hari.

Wani manoma a yankin Tsafe ya ce akwai lokacin da ba ya iya zuwa gonarsa saboda tsoron hari.

"Kanena ya shafe kwana 11 a hannun ƴanbindiga kuma a gida suka ɗauke shi, kuma akwai waɗanda suka fita cirar rogo da aka sace su," in ji shi.

Masana na ganin duk da wannan mataki zai iya sa a samu lafawar hare-haren da kuma wadatuwar amfanin gona irin su waken soya da gyada da dankali saboda tilasta wa manoma nomansu a wannan yankin - amma kuma a daya bangaren matakin na iya haifar da ƙarancin amfani gona irin su masara da gero da dawa saboda ƙarancin noman su a yankin da ke tunƙaho da arzikin noma.