Hanyoyi 4 da za ku gane gidan mai na matse litar fetur

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Shin ka taɓa sayen man fetur amma sai ka ga nan da nan ya ƙare kamar an zuba maka iska a tankin abin hawan ka?

Hakan na yawn faruwa da wasu mutane a duk lokacin da suka ce su sayi man a wasu gidajen mai a Najeriya. Wataƙila za ka sayi man naira dubu 10 amma ka ga ko tafiyar kilomita 2 ba ka yi ba ya ƙare.

Irin wannan yanayi ya sa ake yawan zargin wasu gidajen mai da aikata wata almundahana ta hanyar matse mitar da ke fitar da man. Ko da yake akwai gidajen da ake ala-sam-barka da yanayin man su.

To amma da gaske ne ana iya matse litar man fetur? Idan ana yi ta yaya za ku gane abin da ake yi kuma ku ɗauki mataki?

Abin da hukumomi suka bankaɗo

A cikin makon nan ne, Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta ce ta gano wasu gidajen mai a sassan ƙasar da ke ba kwastomomi man fetur ƙasa da adadin da suka biya kuɗinsa.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, hukumar ta bayyana cewa wannan ɗabi'a ta rage wa mutane mai lokacin saye babban laifi ne da ke karya amincewar kwastomomi, kuma ba za ta lamunci hakan ba.

NMDPRA ta umarci dukkan masu gidajen mai su gaggauta duba da kuma sake gwada na'urorin sayar da mai domin tabbatar da cewa suna aiki yadda ya kamata.

Hukumar ta kuma ce ta ƙara yawan sintiri da bincike a gidajen mai a faɗin ƙasar domin gano masu aikata irin wannan laifi.

Ta yi gargaɗin cewa duk gidan man da aka kama yana rage wa kwastomomi mai, ko kuma yana amfani da na'urorin da ba a daidaita su yadda ya kamata ba, za a tilasta masa gyara kuskuren cikin gaggawa.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da masu sayen da man fetur ke yawan kokawa kan yiwuwar wasu gidajen mai na ba su adadin man da bai kai wanda suka biya kuɗinsa ba.

Ta yaya masu gidajen mai ke matse lita?

Wani manajan gidan mai da ya tattauna da BBC ba tare da an bayyana sunansa ba ya ce wasu gidajen mai na amfani da dabarar sauya tsarin na'urar famfon mai domin rage adadin man da ke fita, yayin da mitar ke nuna kamar an zuba wa mutum cikakken adadin da ya saya.

Ya ce irin wannan sauyi ba abu ne da kowa zai iya gani ba, domin ana yin sa ne a ɓoye, kuma galibi masu aikin gidan man da jami'an sa ido ne kaɗai ke sanin inda mitar take.

"Idan [gidajen man] suka yi irin hakan ne, sai mutum ya sha man lita 10 amma ba zai masa aikin da cikakkiyar lita 6 ko 7 za ta yi masa ba" in ji Manajan.

Manajan ya ƙara da cewa a akwai wani ma'auni da ake kira Seraphin, wanda ake amfani da shi wajen gwadawa da tabbatar da daidaiton na'urorin famfon mai.

Wannan na'ura na gwaji yana da ma'auni da a jikinsa, kuma yana taimaka wa masu gidan mai wajen auna ko famfon na fitar da adadin man da ya kamata.

Saboda haka, ma'aikatan gidan mai kan yi amfani da wannan damar wajen sauya tsarin yadda man ke fita.

Ya bayyana cewa tankin yana da mitoci kama daaga 10L, 100, 200, 300L da kuma 400mL.

Manajan ya ce su kansu sukan yi asara idan har mitar ba ta kan lambar da ta dace. "Kamata ya yi a koda yaushe ta kasance a kan 100 da ke ƙasan 10L. Idan tana kan 200 ko 300 ko 400mL dake ƙasan 10L to tabbas ana zuba wa mutane ƙasa da abin da suka saya," in ji shi.

Sai dai ya ce idan har alamar mitar tana kan 10L ko kuma lambobin da ke samans, a nan ne su kuma masu gidajen man ke asara, domin mitar za ta riƙa zuba wa kwastomomi fiye da abin da suka saya.

Shi dai wannan ma'auni ba kasafai ake ganinshi a fili ba in ji Manajan, sai idan ma'aikatan za su duba shi ko kuma masu bincike sun zo.

A taƙaice dai ya ce kamata ya yi alamar mitar da ke jikin ma'aunin ya kamata tsaya ne kan 100 da ke ƙasan 10L. Ta hakan mutum zai sha daidai ƙiyasin man da ya saya ba tare da ƙari ko ragi ba.

Hanyoyi 3 da za ku gane gidan mai ya matse lita

Manajan ya shaida wa BBC cewa duk da yake a bayyana ba lallai mutum kai tsaye ya iya yin ido biyu da wannan na'ura ta auna mita ba, amma akwai hanyoyin da mutum zai gane litar gidan mai na da matsala idan yana zargin sun matse ta.

Bugu da ƙari ya ce ba lallai mutum ya iya gane daga gudun mitar injimin zuba man fetur ɗin ko an matse lita ko ba haka ba.

Ga wasu daga cikin hanyoyi uku da ya bayar da shawarar yadda mutum zai gane:

Duba mitar mota: Manajan ya ce abu na farko shi ne mutum ya kalli mitar man motarsa bayan ya sayi mai domin ganin ko ya kai mizanin adadin litocin da ya saya idan har mitar na aiki.

Idan kuma mitar motar mutum ba ta aiki, to ya yi nazarin tsawon tafiyar da adadin man yake masa a baya da kuma wanda ya saya idan yana zargin an yi masa ƙwange a sabon gidan man.

Sayen mai a wani ma'auni: Wata dabara da ya ce mutum zai iya amfani da ita wajen gane ko gidan mai na matse litar mai ita ce sayen man fetur ɗin a wani ma'auni ko gorar da ta kai aƙalla lita guda.

"Mutum zai iya zuwa sayen mai a gora kamar ta lita ɗaya, sai ya gani idan man ya kai mizanin lita ɗayan," in ji shi.

Ta hakan ne ya ce mutum zai gane gidan man na amfani da mita mai kyau wajen sayar da mansu ko akasin haka.

Mai mara nauyi: A hirar da muka yi da shi, ya ce akwai kuma yadda mutum zai gane cewa ya sayi man fetur mai kyau ko mara kyau wanda ba zai daɗe masa ba.

Ya ce yawancin man fetur mai haske fari fat, bai cika nauyi ba, kuma yana daga cikin dalilan da zai sa mutum ya ga kamar man fetur ɗin ya yi saurin ƙarewa.

Manajan ya bayar da shawarar cewa mutane su duba wani kalar mai da yake da alamar ja kuma ba kore-kore ba, wanda ya ce shi ne man fetur mai nauyi da ba ya saurin ƙonewa idan aka yi amfani da shi.

Duba mita kafin a fara zuba mai: A zantawar BBC da shugaban ƙungiyar dillalan man fetur a Najeriya IPMAN, Bashir Danmalam ya ce duk lokacin da mutum ya je sayen mai amma ya ga ba a nuna masa litar kafin fara zuba masa ba, to akwai alamar gidan mai yana tauye mudu.

A shawarce, Danmalam ya ce yana da kyau mutum ya duba mitar da ke jikin famfo kafin a fara zuba masa, ta yadda zai san yadda ta fara da kuma yadda ta gama.