Bayern na zawarcin Olmo, Bellingham ya yi watsi Man City

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Bayern Munich na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan gaban Barcelona, ​​Dani Olmo, mai shekara 28, a watan Janairu, inda aka kiyasta darajar ɗan wasan na Spain wanda ya lashe gasar kofin duniya—ta kai kimanin fam miliyan 60. (Sky Sports)

Ɗan wasan tsakiyar Ingila, Jude Bellingham, mai shekara 23, zai tsawaita kwantiraginsa da Real Madrid kuma ba shi da sha'awar komawa Manchester City.(Fichajes)

Chelsea ce za ta kasance a sahun gaba idan ɗan wasan tsakiya na Bournemouth kuma ɗan ƙasar Ingila, Alex Scott mai shekara 23, ya yanke shawarar sauya ƙungiya a watan Janairu. (Mail)

Tottenham da Newcastle da Chelsea na zawarcin ɗan wasan baya na Atalanta da Italiya, Giorgio Scalvini, mai shekara 22. (Caught Offside)

Yarjejemiya da ta kai ɗan wasan gefe na Argentina, Alejandro Garnacho (mai shekara 22), zuwa Aston Villa a matsayin aro na tsawon kakar wasa guda, ba ta ƙunshi sharaɗin da zai ba su damar dakatar da yarjejeniyar a watan Janairu ba. (Telegraph)

Liverpool na duba yiwuwar dawo da ɗan wasan tsakiya na Ingila, Tyler Morton (mai shekara 23), daga Lyon, yayin da ƙungiyoyin Nottingham Forest, da Crystal Palace da Brighton suma ke sa ido a kan ɗan wasan. (Teamtalk)

Chelsea na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin Premier League huɗu da ke sa ido sosai kan ɗan wasan baya na Manchester City da Uzbekistan, Abdukodir Khusanov, mai shekaru 22. (Caught Offside)

Juventus na iya sake nuna sha'awarta kan mai tsaron ragar Brazil, Alisson, mai shekara 33, wanda ke fuskantar rashin tabbas kan makomarsa a Liverpool (Football Italia)

Barcelona za ta buƙaci sayar da ƴan wasa a watan Janairu domin samun kuɗaɗen sayen wasu sabbin ƴan wasa, inda dan wasan baya na Inter Milan da Italiya, Alessandro Bastoni, mai shekara 27, ke cikin jerin waɗanda ta ke son ɗauka. (Fichajes)