Mece ce gaskiyar zargin gwamnatin Kano na ware miliyoyin kuɗi kan ayyukan bogi?

Asalin hoton, Isah Muhammad Salisu
Wani batu da yake ta waɗari a kafar sada zumunta shi ne zarge-zarge da rahotanni da ke nuna cewa an ware ko an biya kuɗaɗe ga wasu ayyuka a jihar Kano da ake cewa ba a same su a wurin da aka ce an aiwatar da su ba.
Ƙungiyar da ke bibiyar aiwatar da kasafin kuɗi a Najeriya ta Tracka ce ta wallafa bayanan da ke zargin cewa gwamnatin ta Kano ta ware miliyoyin kudaɗe a kasafin kudin 2025 amma ba a ga ayyukan ba.
A ranar 5 ga Agusta 2026, ƙungiyar da ke bibiyar aiwatar da kasafin kuɗin a Najeriya ta yi zargin cewa an fitar da fiye da naira biliyan ɗaya domin gyaran azuzuwa 100 a faɗin jihar ta Kano amma kuma ba a gano wurin da makarantun suke ba.
Har wa yau, Tracka ta kuma yi batun ƙarin wasu naira miliyan 235 da aka ware domin gina wata makaranta a ƙaramar hukumar Sumaila amma kuma babu ita babu labarinta.
Abin da Tracka ta gano

Asalin hoton, Facebook/Tracka
Ƙungiyar da ke bibiyar aiwatar da kasafin kuɗin, a shafinta na Facebook ta ce kasafin kuɗin jihar Kano na 2025 ya ware fiye da naira miliyan 235 domin gina azuzuwa a wata makaranta a ƙaramar hukumar Sumaila.
" A cewar rahoton Aiwatar da kasafin Kuɗi na zango na huɗu na jihar Kano na shekarar 2025, an biya Naira miliyan 235.4 domin gina azuzuwa biyu masu hawa ɗaya, kowannensu ɗauke da ajujuwa huɗu tare da ofis da ɗakin ajiya, a makarantar mata ta sakandare ta gwamnati, da ke Massu a ƙaramar hukumar Sumaila ta Jihar Kano," in ji bayanin na Tracka.
Tracka ta kuma ƙara da cewa jami'anta sun ziyarci Massu domin ganewa idanunsu yadda aikin ya gudana.
"Mun ziyarci al'ummar Massu a watan Yunin 2026, amma ba wai kawai ba mu ga wannan aikin ba, har ma mazauna yankin sun ce babu wata makaranta mai suna GGSSS a garin Massu. Haka kuma mun kai ziyara wasu ƙauyuka da ke gundumar Massu, amma ba mu samu wata makaranta mai wannan suna a duk faɗin yankin Massu ba."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bugu da ƙari, Tracka ta ƙara da nuna damuwa dangane da yadda ta nemi wasu ayyukan gyaran azuzuwa 100 a faɗin jihar da aka ware musu tsabar kuɗi har naira biliyan ɗaya, da aka ce ba a san takamaiman wurin da za a yi aikin ba.
" A cewar Rahoton aiwatar da Kasafin Kuɗi na zango na huɗu na jihar Kano na shekarar 2025, an fitar da sama da Naira biliyan 1 domin gyaran ajujuwa 100 a faɗin jihar," in ji Tracka.
Sai dai kuma Tracka ta ce ta nemi bayani dangane da makarantun da wuraren da ake aikin nasa amma ba su samu gamsasshen bayani ba.
"Mun aike da buƙatar samun bayanai ƙarƙashin Dokar 'Yancin Samun Bayanai (FOI) ga Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Kano (SUBEB) a watan Mayun 2026. Amma a martaninta, hukumar ta ce ba ta da bayanan wuraren da aka gudanar da gyaran ajujuwan."
"Makaranta ɗaya tilo da hukumar ta nuna mana ita ce Makarantar Firamare ta Jili da ke Rimin Gado, inda muka tabbatar cewa an yi mata fenti tare da wasu gyare-gyare. Daga nan ne aka shawarce mu mu tuntubi Ma'aikatar Ilimi ta Jihar Kano domin samun bayanai kan wuraren da aka aiwatar da wannan aikin," in Tracka.
Mene ne martanin gwamnatin Kano?

Asalin hoton, KNSG
BBC ta tuntuɓi gwamnatin Kanon domin jin bahasinta dangane da wannan batu, inda kuma ta ce ba haka batun yake ba, tana mai bayyana shi da jita-jita.
Daraktan yaɗa labaran gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya shaida wa BBC cewa bisa bayanan da ya samu daga ƙaramar hukumar Sumaila da ma'aikatar ƙananan hukumomin jihar babu wannan al'amari a cikin kasafin kuɗinsu.
''Hasalima ba ya cikin abubuwan da ƙaramar hukumar ta taɓa rubutowa a ba ta, kuma ba ya cikin abin da ƙaramar hukumar ta karɓa a hannun gwamnatin jiha domin ta yi,'' in ji shi.
Mai magana da yawun gwamnan jihar ya kara da cewa hasalima Shi gini ko gyaran makarantar sakandire alhakin gwamnatin jiha ne, ba na ƙaramar hukuma ba.
''Mafi akasari ƙananan hukumomi suna samu amincewa gwamnatin jiha ne, domin su yi gyara ko gina sababbin makarantun furamare, amma ba sakandire ba, sai dai in akwai wata bukatar gyaran sakandire da wataƙila karamar hukumar ke ganin za ta iya gyara wa bisa raɗin kanta da kuɗaɗenta'', in ji shi.
Kakakin gwamnan ya ci gaba da cewa ma'aikatar ilimin jihar Kano ba ta taɓa gabatar da wani aiki da ya shafi wannna makaranta ba.
Sai dai ya ce wataƙila aikin mazaɓa ne da wani ɗanmajalsia ya gabatar a matsayin abin da za a sanya cikin kasafin kuɗi, amma ba ya cikin ayyukan da ma'aikatar ilimin jihar da gabatar ba.
Ya yi zargin cewa irin ƙungiyoyin da ke gabatar da wanan bincike suna yi aiki ne da jita-jita.
''Ba sa tsayawa su binciko ainihin gaskiyar yadda aikin gwamnti ke tafiya ba, babu yadda za a yi ka ce an kashe naira miliyan kaza kan wata makaranta, bayan kuma babu wannan makarantar'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Daga karshe ya jaddada cewa babu inda gwamnatin jihar Kano ta fitar da wannan kudin domin gina wata makaranta a wannan yanki na ƙaramar hukumar Sumaila.
Ayyukan da Tracka ta yaba da su
Ƙungiyar mai bibibyar yadda ake aiwatar da kasafin kuɗi ta Tracka ta ce ta gane wa idanunta wasu ayyukan da ke cikin kasafin kudin na 2025 na jihar Kano waɗanda kuma aka aiwatar da su.
Ayyukan sun haɗa da:
- Titin Layin Maƙabarta Road da ya hada ƙananan hukumomi Kumbotso da Nassarawa wanda aka bayar akan naira miliyan 300 a kasafin kuɗin jihar na 2024.
- Sakataren ilimi na ƙaramar hukumar Rimin Gado ya shaida wa Tracka cewa an rarraba kujerun zama guda 1000 ga firamare a mazaɓu 12 na ƙaramar hukuma. Wannan na daga cikin ayyukan da aka ware naira miliyan 969.2 domin samar da kujerun zama ga makaratun firamare a ƙananan hukumomi 13 a jihar.












