Yadda za ku duba sakamakon jarabawar WAEC a wayarku

how to check waec result

Asalin hoton, WAEC

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta yammacin Afrika WAEC, ta sanar da fitar da sakamakon jarabawar ta shekarar 2026.

WAEC ta fitar da sanarwar ne a shafinta na X a yau Laraba.

Sanarwar ta ce: "An saki sakamakon WASSCE (SC) na shekarar 2026. Ku samar da lambobin PIN a shafin intanet na http://waec.org sannan ku ziyarci shafin http://waecdirect.org," domin ganin sakamakon jarabawarkuin ji sanarwar.

Ta ce cikin mutum 1,950,726 da suka rubuta jarabawar a wannan shekarar, mutum 1,200,514 sun lashe aƙalla darussa biyar ciki har da Lissafi da Ingilishi.

Aƙalla mutum miliyan 1.96 daga makarantun sakandare sama da 24,200 a faɗin Najeriya ne suka rubuta jarabawar da aka gudanar tsakanin 21 ga watan Afrilu zuwa 19 ga watan Yuni, 2026.

Ga wanda zai duba sakamakon jarabawarsa a karon farko, ga matakan da ake duba sakamakon jarabawar WAEC ta intanet da kuma ta waya ta hanyar tura saƙon kar-ta-kwana (SMS).

Matakin farko: Samun lambobin PIN

Kafin ka duba sakamakon jarabawar WAEC, kana buƙatar lambar jarabawarka, da lambobi na musamman (WAEC serial number) da lambobin PIN.

  • WAEC ta ce duk wanda ya manta lambobin na musamman ɗinsa wato serial number ko kuma PIN, zai iya samunsu ta waɗannan hanyoyin:
  • A ziyarci shafin intanet na waec.org
  • A latsa wajen "Serial Number and PIN" da ke saman shafin farko.
  • Zai a zaɓi shekarar jarabawa ta 2026.
  • Sai a rubuta lambobin jarabawa da kuma lambar katin ɗanƙasa na NIN da aka yi amfani da shi a yayin rijistar WAEC
  • A sanya adirehin imel da lambar waya domin a tura lambobin sirri na OTP
  • A shigar da lambobin OTP domin ganin Serial Number da PIN

"Za kuma a iya sauke katin shaidar WAEC (ID Card) daga shafin ta waya," in ji WAEC.

Mataki na 2: A ziyarci shafin intanet na WAEC

Bayan an samu lambobin PIN da Serial Number

Kai tsaye sai a tafi shafin duba sakamakon jarabawar a waecdirect.org ta waya, ko kwamfiyuta.

Mataki na 3: Sanya lambobin jarrabawa

Bayan an buɗe shafin sai a bi waɗannan matakan:

  • A rubuta lambobin jarabawa masu haruffa guda 10 da suka ƙunshi:
  • Lambobin cibiyar da aka rubuta jarabawa mai haruffa bakwai (centre number)
  • Lambobin rubuta jarabawar ɗalibi mai haruffa uku (candidate number)

Alal misali: 2345678901.

Matakai na gaba

Mataki na gaba shi ne sai a zaɓi shekarar da aka rubuta jarabawa. Alal misali 2026.

Sai a zaɓi jarabawar da aka rubuta

Daga nan sai a shigar da lambobin PIN da Serial Number

Waɗannan lambobin su ne lambobin da aka fitar daga shafin WAEC na http://waec.org

Daga nan sai a danna Submit

Da zarar an bi waɗannan matakan, sakamakon jarabawar zai bayyana domin ɗalibi ya ga sakamakon da ya samu, daga nan sai a ɗauki hoto ko a fitar da sakamakon.

Yadda ake duba sakamakon jarrabawar WAEC ta waya

how to check waec result

Asalin hoton, WAEC

Ga waɗanda ba su da damar shiga ta shafin intanet kuma, akwai hanyoyin da za su iya dubawa ta saƙon SMS a tura musu sakamakon da suka samu.

A rubutu kalmar WAEC haɗe da lambobin jarabawa da PIN, sa a rubuta alamar tauraro sannan a rubuta shekarar jarabawa a gaba. Wato WAEC*ExamNo*PIN*ExamYear

Alal misali ga yadda za a rubuta: WAEC2345678901123456789012*2026

Sai a tura waɗannan lambobin ga wannan lambar saƙon SMS ta WAEC - 32327

Daga nan za a aiko maka sakamakon jarabawarka.

WAEC na shawartar waɗanda ke son duba sakamakon jarabawar tasu, su tabbatar sun fitar da lambobin PIN da Serial Number a shafin waec.org kafin shiga shafin waecdirect.org domin duba sakamakon.