Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 6/08/2026

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 6 ga watan Agustan 2026.

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • xxx
  • xxx
  • Bola Tinubu
  • Senator Gaya
  • xxx
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu

Rahoto kai-tsaye

Daga Muslim Muhammad Yusuf

  1. Anthony Fauci na fuskantar barazanar fuskantar shari'a

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani kwamitin Majalisar Dattijan Amurka ya kaɗa ƙuri'ar samun tsohon babban mashawarci a fannin lafiya na fadar White House, Anthony Fauci da raina majalisa, bayan ya ƙi amsa tambayoyi kan yadda ya tafiyar da annobar korona.

    Ƙwararren a fannin cutuka masu yaɗuwa ya yi togaciya da 'yancin da tsarin mulki ya ba shi na yin shiru a makon jiya lokacin da sanatocin ke titsiye shi kan annobar -- da kuma tambayar ko akwai rufa-rufa game da asalinta.

    Babu masaniya ƙarara ko matakin samun Fauci da raina majalisa, zai kai ga ɗaukar matakin shari'a a kansa.

    Rahotanni sun ce a wannan lokaci dai ba za a iya fayyacewa ba, ko ma'aikatar shari'a za ta zaɓi gurfanar da Dr Fauci a gaban shari'a.

  2. 'Hatsari ne mu bar tsaron iyakokinmu ga hannun wata kasa'

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwamishinan Ƙaura na Tarayyar Turai, Magnus Brunner ya ce ƙungiyarsu na cikin hatsari matuƙar kula da kan iyakarsu ya dogara a kan karimcin wata ƙasa mai maƙwabtaka.

    Yana jawabi ne mako guda bayan mutum dubu saba'in daga Moroko sun yi kukan kura sun fantsama cikin Ceuta -- yankin ƙasar Sifaniya na Arewacin Afirka.

    Ya faɗa wa taron Majalisar Dokoki na musamman cewa jazaman ne Tarayyar Turai ta yi amfani da duk wani tasirinta a kan Moroko da sauran ƙasashe wajen haɗa gwiwa kan harkokin ƙaura.

    Ƙasashen Tarayyar Turai da dama sun yi matuƙar sukar lamirin Sifaniya saboda gazawarta na kare kwararar ɗumbin mutane cikin Ceuta.

  3. Amurka ta sanya wa Ministan Cuba takunkumi

    ,

    Asalin hoton, Getty Imagesa

    Amurka ta sanya wa ministan rundunar sojin Cuba da harkokin safarar kayan sojojin ƙasar takunkumai.

    Washington ta kuma sanar da sabbin matakan matsa lamba kan wasu 'yan ƙasar Cuban da yawa.

    Tun farko, ƙwararru a Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi kiran a ɗauki matakan gaggawa na hana takunkuman Amurka tura Cuba cikin abin da suka kira wani gagarumin hargitsi.

    Sun kuma yi alla-wadai da ƙarin matakai a baya-bayan nan a kan tsibirin Cuba, suna gargaɗin cewa akwai kasadar wata "Gaza a fakaice" tana faruwa a can.

    Cuba na fama da katsewar lantarki da ƙarancin kayan masarufi tsawon watanni - hakan ya ta'azzara ne sanadin matsin lambar Shugaba Trump na neman Cuba ta yi garambawul ko ta fuskanci canjin gwamnati.

  4. Har yanzu za su iya ƙaurace wa FIFA ciki har da ta Kofin Duniya - UEFA

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙwallon ƙafan Turai UEFA ta ce ƙungiyoyinta har yanzu za su iya ƙaurace wa gasannin FIFA ciki har da ta Kofin Duniya, duk da dakatar da shirin sayar da hannun jarinsu mai cike da taƙaddama.

    Shirin, wanda Shugaban FIFA, Gianni Infantino ya sanar ya harzuƙa UEFA wadda ta ce ba ta ƙwarin gwiwa a kansa.

    Yayin wani taro ranar Laraba, hukumar gudanarwar FIFA ta jaddada goyon bayanta ga Infantino, amma UEFA ta ce goyon bayan bai canza komai ba.

    Wata sanarwa ta UEFA na cewa da farko sai an janye matakin sayar da hannun jarin, sannan a ba ta tabbaci ba za a sake kawo yunƙuri irin wannan da zai gurɓata gasar ba. Sharuɗɗan da, in ji ta, har yanzu ba a cika su ba.

    A lokaci guda kuma hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Amurka ta Kudu CONMEBOL ta yi maraba da janye matakin - amma ta ce ba za ta goyi bayan neman tsige shugaban na Fifa ba.

  5. Fatanmu Amurka da Iran su biyo sahu - Pakistan

    Pakistan ta ce tana fata aiki da yarjejeniyar da Iran ta cimma da Oman a kan Mashigar Hormuz za ta kai Amurka da Iran su koma teburin tattaunawa don kawo ƙarshen yaƙinsu.

    Gwamnatin Pakistan tare da Qatar sun ba da gagarumar gudunmawa wajen shiga tsakani a ƙoƙarinsu na ganin Amurka da Iran sun cimma zaman lafiya.

    Sai dai, Amurka da Oman ba su ce uffan ba a kan iƙirarin ƙasar Iran na cewa ita da Oman ɗin sun kusa cimma wata yarjejeniya a kan sabuwar hanyar wucewar jiragen ruwa a Mashigar Hormuz.

  6. 'Yan kwacen waya sun kashe kyaftin in Uganda

    Ana ci gaba da tura saƙonnin ta'aziyya ga iyalan wani ɗan ƙwallon ƙafa na ƙasar Uganda, David Owori wanda ya rasu bayan 'yan fashi sun kai masa hari a babban birnin Kampala.

    'Yan sanda sun ce an far masa ne ranar Litinin da yamma bayan ya ƙi yarda da yunƙurin gungun wasu tsagerun kan titi su satar masa wayar salula da sauran kayansa a kusa da gidansa.

    Ya rasu a asibiti daga bisani sakamakon raunukan da ya ji.

    Majalisar Dokokin Ƙasar ta yi shiru na minti ɗaya ranar Laraba domin karrama shi, sannan ta yi kira a gaggauta yin bincike Owori kaftin ɗin ƙungiyar ƙwallon ƙafa na Sports Club Villa ne, wadda ta fi cin Gasar Firimiyar Uganda.

    Lamarin ya janyo damuwa a kan ƙaruwar manyan laifuka a Uganda.

  7. Isra'ila ce ke zagon ƙasa ga yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza - Rahotanni

    Ministocin wajen Jordan da na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Indonesiya da Pakistan da Turkiyya da Saudiyya da Qatar da kuma Masar sun zargi Isra'ila da yin zagon ƙasa ga ƙoƙarin baya-bayan nan na cimma yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza.

    A wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar bayan tattaunawa a Amman, ministocin sun yi allaa-wadai da abin da suka kira "keta haddi"n Isra'ila a Zirin Gaza, wanda suka ce yana barazana ga shirin Shugaba Trump na kawo ƙarshen rikici a yanki.

    Mataki ya zo ne bayan sanarwar da hamas ta fitar inda ta ce ta amince da shirin kwance ɗamara, wanda zai sanya ƙungiyar miƙa makamanta.

    Isra'ila ta ce hare-harenta a Gaza cikin 'yan kwanakin nan ta kai su ne kan 'yan ta-da-ƙayar-baya na Hamas da kuma kayan aikinsu.

    Ta kafe kai da fata cewa ba za ta fara janye dakarunta ba sai an samu ƙwaƙƙwaran ci gaba a batun ajiye makaman Hamas.

  8. Shugaban sojan Myanmar Min Aung Hlang ya isa Thailand

    Shugaban mulkin sojan Myanmar, Min Aung Hlang ya samu tarbar arziƙi a ƙasar Thailand, yayin da yake neman kawar da matakin saniyar ware da aka mayar da ƙasarsa ta fuskar diflomasiyya, duk da yaƙin da suke ci gaba da yi.

    Bayan ganawa da firaministan Thailand, Min Aung Hlaing ya yi iƙirarin cewa Myanmar na kan hanyar komawa tafarkin dimokraɗiyya da kuma rayuwa mafi inganci a gaba.

    Ita ce ziyararsa a hukumance ta farko zuwa maƙwabciyar ƙasar tasa tun bayan hamɓarar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin Aung San Suu Kyi a 2021.

    Ƙungiyoyin kare 'yancin ɗan'adam sun soki lamirin ziyarar suna cewa ƙoƙari ne na halarta mulkin baƙin zalunci na sojoji.

    Thailand dai ta ce ya zame mata jazaman ta koma hulɗa da Myanmar da nufin shawo kan matsalolin da take fama da su a kan iyaka.

  9. Trump ya musanta ƙarancin alburusai, tare da barazanar ɗaure jami'in da fallasa hakan

    Shugaba Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka na da isassun makamai da alburusai tare da barazanar ɗaure masu yaɗa jita-jitar ƙarancinsu.

    Mista Trump ya ce ƙasarsa na da tarin alburusai da makamai masu yawa, tare da yin barazanar cewa duk wanda ya yaɗa jita-jitar akasin haka zai iya fuskantar hukuncin ɗaurin kurkuku na dogon lokaci.

    A baya-bayan nan ne dai wasu kafofin yaɗa labarai suka ambato wani jami'in ƙasar ce iƙirarin cewa ƙasar na fuskantar karancin alburusai da makamai a rumbunan ajiyar makamanta.

    To sai dai cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin Truth Social, Trump ya soki rahotannin kafafen yaɗa labaran.

    "Duk wanda ya yaɗa wannan bayanin na ƙarya za a gurfanar da shi a gaban kotu kuma zai fuskanci hukuncin ɗaurin kurkuku na dogon lokaci," in ji shi.

    Shugaban ya kara da cewa Amurka na da "adadi mai yawa na alburusai da makamai, musamman wasu nau'o'i na musamman", amma bai bayar da ƙarin bayani ba.

    Ya ƙara da cewa ana samar da manyan adadi na alburusai a halin yanzu, kuma za a kai su Amurka idan buƙata ta taso.

    Ya kuma ce kamfanonin tsaro suna gina mafi yawan masana'antu da cibiyoyin samar da makamai a tarihin ƙasar.

    Jaridar Washington Post ta ruwaito cewa Trump ya nemi Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya yi bayani kan ƙarancin alburusai a wani taron majalisar ministoci da aka gudanar a Camp David ranar Juma'ar da ta gabata.

    Jaridar, ta ambato majiyoyi biyu da ba a bayyana sunayensu ba, da ke cewa Trump ya shaida wa Hegseth cewa ''yana tsammanin an riga an magance matsalar ƙarancin alburusan''.

    A wani rahoto daban, gidan talabijin na CNN ya ce ƙarancin makamai masu linzami masu dogon zango da kuma makaman kariyar sararin samaniya ya yi tasiri kan manufar Donald Trump dangane da rikicin Iran

  10. Mutane 11 sun mutu a harin Rasha kan Ukraine

    Ukraine

    Asalin hoton, State Emergency Service of Ukraine

    Adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin da Rasha ta kai kan birnin Pavlohrad da ke gabashin Ukraine ya kai 11.

    Mahukuntan yankin sun ce a ƙarin wasu mutum biyu sun mutu a sabon harin.

    Jami'in yankin, Oleksandr Hanzha, ya ce mutane bakwai sun jikkata a harin, yayin da gobara ke ci gaba da tashi a wasu rumbunan ajiya da harin ya shafa.

    Da wannan sabon adadi, mutanen da aka tabbatar sun mutu a hare-haren da aka kai a sassan Ukraine a yau sun kai aƙalla 11.

  11. Sojojin Kamaru sun musanta zargin kashe fararen hula a yankin masu rajin ɓallewa

    Rundunar sojin Kamaru

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Kamaru ta musanta zargin cewa jami'anta sun kashe fararen hula tare da lalata dukiyoyi a wani samame da suka kai a yankin Kudu maso Yamma mai amfani da Turanci a watan da ya gabata.

    A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Kyaftin Cyrille Serge Atonfack, ya fitar ranar Laraba, ya ce samamen da aka kai ƙauyuka biyu da ke ƙaramar hukumar Akwaya an kai shi ne kan mayaƙan masu rajin ballewa.

    Ya ce jami'an tsaron sun gudanar da aikin ne bisa bayanan sirri da suka samu daga mazauna yankin, wanda ya kai ga kashe mayaƙa biyar tare da ƙwato makamai a ranar 17 ga Yuli.

    Sanarwar ta ce manufar samamen ita ce daƙile mayaƙan da ake zargin suna shirin kai hare-hare da lalata muhimman cibiyoyin sadarwa a yankin.

    Rundunar ta kuma yi watsi da zargin cewa sojojinta sun kashe fararen hula ko kuma sun lalata dukiyoyi yayin samamen, tana mai bayyana rahotannin a matsayin "farfaganda."

    Ya ƙara da cewa har yanzu jami'an tsaro na ci gaba da gudanar da samame domin cafke sauran mayaƙan da suka tsere.

    A baya dai ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun sha zargin sojojin Kamaru da kai hare-hare kan fararen hula yayin yaƙin da suke yi da masu rajin ballewa a yankunan masu amfani da Turanci.

  12. Kuwait ta rufe makarantar ƴan Iran da ke ƙasar

    Kuwait

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahukuntan Kuwait sun ba da umarnin rufe makarantar ƴan Iran guda ɗaya tilo da ke ƙasar, bayan hare-haren da Iran ta kai wa Kuwait a lokacin yaƙin Gabas ta Tsakiya.

    Wata majiya daga Ma'aikatar Ilimi ta Kuwait ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an bayar da umarnin rufe makarantar, sai dai ba ta bayyana takamaiman dalilin matakin ba.

    Kuwait na cikin ƙasashen yankin Tekun Fasha da Iran ta kai wa hare-hare a lokacin yaƙin, saboda kasancewar sojojin Amurka a ƙasar.

    Takardar umarnin Ma'aikatar Ilimi, wadda AFP ta gani, ta ce: "Ministan Ilimi ya yanke shawarar soke lasisin makarantar mai zaman kanta ta Iran tare da rufe ta."

    Bisa wannan umarni, an dakatar da karɓar sabbin ɗalibai domin shekarar karatu mai zuwa, yayin da aka buƙaci iyaye su mayar da ƴaƴansu zuwa wasu makarantu.

  13. Tinubu ya umarci EFCC ta buɗe asusun gwamnatin jihar Osun cikin gaggawa

    Tinubu

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/Facebok

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci hukumar EFCC da ta gaggauta komawa kotu domin neman a soke umarnin da ya ba ta damar rufe asusun gwamnatin jihar Osun.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Tinubu ya ce matakin da EFCC ta ɗauka ya ba shi kunya saboda "lokacin da ta ɗauki matakin."

    "Dole ne in bayyana cewa abin ya ba ni kunya ƙwarai. Ba wai saboda EFCC ta aiwatar da aikinta ba ne duk da cewa ta samu umarnin kotu ba, sai dai saboda lokacin da ta ɗauki wannan mataki," in ji shugaban.

    Ya ce duk wani mataki da hukumomin gwamnatin tarayya suka ɗauka, ana danganta shi da shugaban ƙasa ne ko da kuwa ba shi da masaniya kan abin da aka aiwatar.

    Shugaban ya kuma jaddada cewa tun lokacin da ya hau mulki ya guji tsoma baki cikin ayyukan EFCC da sauran hukumomin bincike domin ba su damar gudanar da aikinsu cikin 'yanci.

    "Na kasance ina jaddada cewa dole ne a bar hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran hukumomin tabbatar da doka su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa, ba tare da tsoro, son rai ko katsalandan na siyasa ba."

    Sai dai Tinubu ya ce, duk da cewa har yanzu bai samu cikakken bayani kan dalilan da suka sa EFCC ta nemi kotu ta ba ta umarnin rufe da asusun gwamnatin jihar Osun ba, yana ganin lokacin da aka ɗauki matakin bai dace ba.

    "Jihar Osun na daf da gudanar da zaɓen gwamna. Don haka bai kamata a yi wani abu da zai sa a yi zargin cewa ana amfani da EFCC ko wata hukumar gwamnatin tarayya wajen yin katsalandan a zaɓen ba."

    Saboda haka shugaban ya ce ya ba hukumar umarni ta ɗauki matakin gaggawa.

    "Na umarci EFCC da ta gaggauta komawa kotu domin neman a soke wannan umarni, tare da dakatar da duk wani mataki da ta ɗauka kan gwamnatin jihar Osun dangane da wannan lamari."

    EFCC ta samu umarnin kotu a ranar 5 ga Agustan 2026 na rufe asusun gwamnatin jihar Osun. Sai dai zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, hukumar ba ta fitar da karin bayani kan dalilan da suka sa ta nemi umarnin kotun ba.

  14. Gwamnatin Jihar Osun za ta ɗauki matakin shari'a kan rufe mata asusu da EFCC ta yi

    Gov Ademola Adeleke

    Asalin hoton, Gov Ademola Adeleke/X

    Gwamnatin Jihar Osun ta fara ɗaukar matakin shari'a kan abin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta yi na rufe asusun bankin gwamnatin, kwanaki kaɗan kafin zaɓen gwamna a jihar.

    Gwamnan jihar, Ademola Adeleke, ya tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa, inda ya ce a safiyar Laraba bankinsu ya aika musu da wasiƙar EFCC da ke umartar a rufe asusun gwamnatin jihar.

    Ya kuma ce ya umarci Babban Lauyan Jihar da ya ƙalubalanci matakin a gaban Kotun Tarayya da ke Osogbo.

    Gwamna Adeleke ya kuma ƙalubabalnci sahihancin matakin na EFCC, yana mai kira ga shugaban hukumar, Ola Olukoyede, da ya bayyana wa al'ummar Osun da 'yan Najeriya dalilin da ya sa aka rufe asusun gwamnatin jihar tare da gabatar da hujjoji.

    Gwamnan ya ce wannan na daga cikin jerin matsalolin da jihar ke fuskanta kafin zaɓen gwamna da za a gudanar ranar 15 ga Agusta, 2026, ciki har da hare-haren bindiga, tangarɗa ga tsarin ƙananan hukumomi da kuma kama mambobinta.

  15. Mummunan tarihin cinikin bayi a Afrika da ba za a taɓa mantawa ba

    A birnin Badagry da ke jihar Legas ne ake tsare bayin cikin sasari da ɗauri sannan a yi cinikinsu, inda daga nan ake kai su zuwa wata sabuwar duniya, kuma mafi yawansu tafiyar ke nan domin ba su sake komawa ba.

    Kalli wannan bidiyon:

    Bayanan bidiyo, Mummuman tarihin cinikin bayi a Afrika da ba za a taɓa mantawa ba
  16. Tinubu ya yaba wa jami'an tsaron da suka ceto mutum 308 daga ƴanbindiga a Kwara da Neja

    Bola Ahmed Tinubu

    Asalin hoton, Bayo Onanuga

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa jami'an tsaro bayan nasarar da suka samu wajen ceto mutane 308 da ƴanbindiga suka sace a jihohin Kwara da Neja da ke arewa ta tsakiya.

    A cikin mutanen da aka ceto, 163 an sace su ne daga yankin Woro da ke ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara, yayin da 145 kuma aka sace su daga jihar Neja.

    A wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, an ce an ceto mutanen ne daga dajin Kainji Lake National Park da ke ƙaramar hukumar New Bussa a jihar Neja.

    Sanarwar ta ce an gudanar da aikin ne bisa sahihan bayanan sirri, tare da haɗin gwiwar Cibiyar Yaƙi da Ta'addanci ta Ƙasa (NCTC), Rundunar Sojin Najeriya, Hukumar DSS da kuma 'Yan Sandan Najeriya.

    "Wannan shi ne mafi girman aikin ceto mutane da aka taɓa gudanarwa cikin rana guda ta hannun jami'an tsaron haɗin gwiwa," a cewar shugaban ƙasa.

    Tinubu ya yaba da jarumtaka da haɗin kan jami'an tsaron, inda ya ce nasarar ta nuna yadda ayyukan tsaro da tattara bayanan sirri ke ƙara inganta.

    Mutanen da aka ceto na karɓar kulawar gaggawa a asibitin Wawa Cantonment, kafin daga bisani a miƙa su ga gwamnatocin jihohinsu domin ci gaba da kula da su da kuma haɗa su da iyalansu.

    Shugaban ya sake tabbatar wa 'yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kawar da matsalolin tsaro da dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar.

  17. Ba ma fuskantar ƙarancin makamai - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake nanata cewa ƙasarsa ba ta fuskantar ƙarancin makamai.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya soki rahotannin da ke cewa makaman Amurka sun ragu, yana mai cewa ƙasar na da "tarin makamai da harsasai", sai dai bai bayyana nau'o'in da yake magana a kansu ba.

    Ya ƙara da cewa kamfanonin tsaro na ƙasar na ci gaba da samar da makamai cikin sauri, tare da gina sabbin masana'antu da cibiyoyin kera makamai mafi yawa a tarihin Amurka.

    A cewarsa, za a ci gaba da tura makamai zuwa inda ake buƙatarsu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

    A baya dai jaridar Washington Post ta ruwaito cewa Trump ya tambayi Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, bayani kan rahotannin ƙarancin harsasai a wani taron majalisar ministoci da aka gudanar a Camp David a ranar Juma'ar da ta gabata.

    Jaridar, wadda ta ambato wasu majiyoyi biyu da ba ta bayyana sunayensu ba, ta ce Trump ya shaida wa Hegseth cewa yana tunanin an riga an warware matsalar ƙarancin makaman.

    Sai dai a saƙonsa na ranar Alhamis, Trump ya yi kakkausar suka ga waɗanda suka fitar da bayanan, yana mai cewa an fara gurfanar da su a gaban shari'a, kuma za su fuskanci hukuncin ɗaurin shekaru masu yawa a gidan yari.

  18. Rasha ta ce ta lalata jirage marasa matuƙa 605 da Ukraine ta harba cikin dare

    Russia Ukraine

    Asalin hoton, Telegram

    Ma'aikatar Tsaron Rasha ta ce dakarunta sun kakkabo jiragen marasa matuƙa 605 na Ukraine a hare-haren da ta kai cikin daren Laraba.

    A cewar ma'aikatar, an daƙile hare-haren ne a yankuna da dama, ciki har da Moscow da Yaroslavl, inda ɗaya daga cikin manyan matatun man Rasha, Slavneft-Yanos, take.

    Rahotanni sun ce an ga baƙin hayaƙi mai yawa na tashi sama a birnin Yaroslavl bayan harin da jiragen marasa matuƙa da Ukraine suka kai.

    Gwamnan yankin, Mikhail Evraev, ya ce wannan shi ne hari mafi girma da yankin ya taɓa fuskanta, kumaan lalata jirage marasa matuƙa 92 a yankin kaɗai.

    A gefe guda kuma, jami'an Ukraine sun ce hare-haren Rasha sun kashe mutum uku a birnin Balakliya, yayin da wasu 12 suka jikkata a yankin Sumy.

  19. Iraniyawa mutane ne masu taurin kai - Mataimakin Shugaban Amurka

    J.D. Vance

    Asalin hoton, Getty Images

    Mataimakin Shugaban Amurka, J.D. Vance, ya ce yana ganin Iraniyawa a matsayin wasu mutane masu taurin kai, inda ya ce hakan na daga cikin ƙalubalen da ake fuskanta wajen warware rikicin da ke tsakanin ƙasarsa da Iran.

    A wata hira da ya yi da tashar Fox News, Vance ya mayar da martani kan sukar da wasu Amurkawa ke yi game da yadda gwamnatin ƙasar ke tafiyar da yaƙin da Iran.

    Ya ce akwai rarrabuwar kawuna a cikin gwamnatin Iran, kuma wani ɓangare na shugabannin ƙasar na son a ci gaba da tattaunawa, yayin da wani ɓangaren masu tsattsauran ra'ayi ke son a ci gaba da yaƙi.

    Vance, wanda ya jagoranci tawagar Amurka a tattaunawar Islamabad, yana da yaƙinin cewa daga ƙarshe "komai zai ƙare ne ta hanyar da za ta amfani al'ummar Amurka."

    Sai dai ya bayyana cewa ana samun ci gaba da koma baya a rikicin da ake yi da Iran

    Wasu rahotanni sun ce shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, na iya kai ziyara Pakistan cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

    Sai dai gwamnatin Iran ba ta tabbatar ko musanta waɗannan rahotanni ba.

  20. Ukraine ta ce ta kai hari kan matatun mai biyu a Rasha

    Volodymyr Zelensky

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce dakarun ƙasarsa sun kai hare-hare kan matatun mai biyu da ke cikin Rasha.

    A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Zelensky ya ce sojojin Ukraine sun kai hari kan matatar mai ta Slavneft-Yanos da ke birnin Yaroslavl, da kuma matatar Bashneft-Novoil da ke yankin Bashkortostan.

    Tun da farko, rahotanni sun ce an ga baƙin hayaƙi na tashi daga yankin matatar mai ta Yaroslavl bayan hare-haren jiragen saman marasa matuƙa na Ukraine.

    Zelensky ya kuma ce dakarunsa sun kai hari kan kwale-kwalen sintiri guda biyu na sojojin Rasha da kuma wasu jiragen ruwan Rasha a Baharul Aswad.

    Har yanzu hukumomin Rasha ba su yi martani kan ikirarin Ukraine ba.