KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa na 03 - 09 Agusta 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku Labaran wasannin BBC Hausa na 03 - 09 Agusta 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Arsenal na shirin ɗaukar kyaftin ɗin Newcastle

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal na shirin kammala yarjejeniyar ɗaukar kyaftin ɗin Newcastle United, Bruno Guimaraes, bayan dogon lokaci ana tattaunawa.

    A ranar 30 ga watan Yuli ne BBC Sport ta bayar da rahoton cewa ana sa ran Guimaraes zai koma ƙungiyar da ta lashe gasar Premier League bayan samun ci gaba a tattaunawar.

    Yanzu haka an kusa cimma cikakkiyar yarjejeniya, inda Guimaraes ke jiran izinin barin sansanin horaswa na Newcastle da ke La Manga a ƙasar Spain, domin kammala matakan ƙarshe na komawarsa filin wasa na Emirates.

    Arsenal na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da gwajin lafiyar ɗan wasan tsakiyar na Brazil a wannan makon.

    Babu tabbas kan kudin da za a biya, amma majiyoyi na nuni da cewa adadin na iya kai wa fam miliyan 80.

    Guimaraes, wanda ya koma Newcastle daga Lyon a shekarar 2022, ya bayyana ƙarara cewa yana son komawa Arsenal, kasancewar ɗan wasan mai shekaru 28 ya zama babban ɗan wasan tsakiya da Mikel Arteta ke matuƙar son ɗauka.

    Newcastle da Arsenal sun shafe wannan makon suna tattaunawa kan cikakkun sharuɗɗan yarjejeniyar, kuma yanzu ana ganin ana daf da cimma yarjejeniyar ta ƙarshe.

  2. An bai wa Vozinha izinin amfani da laƙabinsa a Colo-Colo

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Chile (ANFP) ta amince ta bai wa mai tsaron ragar Cape Verde, Vozinha, damar sanya sunan da aka fi saninsa da shi a bayan rigarsa ta ƙungiyar Colo Colo.

    Ɗan wasan mai shekaru 40 ya rattaba hannu kan kwantiragin watanni shida da Ƙungiyar ta Chile (Liga de Primera) a ranar Litinin, bayan ya samu yabo a duniya saboda rawar da ya taka a gasar cin kofin duniya.

    A bisa Ƙa'idojin gasar, ya kamata ya buga wasa da sunansa na asali, wato Josimar Jose Evora Dias, kasancewar dokokin ANFP sun tanadi cewa "ba a yarda a sanya sunayen laƘabi ko na barkwanci" a jikin rigunan wasa ba.

    Sai dai, Ƙungiyar Colo Colo ta samu izinin ya buga wasa da sunan da ya shahara da shi.

    Vozinha ya isa Santiago a ranar Lahadi inda magoya bayan ƙungiyar Colo Colo suka yi masa tarba ta musamman, sannan ya shiga atisaye tare da sababbin abokan wasansa bayan kwana biyu.

  3. Liverpool ta shirya ɗaukar Barcola kan farashin fam miliyan 100

    Barcola

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool ta riga ta biya fiye da fam miliyan 100 sau biyu domin sayen ƴan wasa - wato ɗan wasan tsakiya Florian Wirtz da ɗan wasan gaba Alexander Isak - kuma akwai yiwuwar za ta sake yin hakan.

    Ɗan wasan gefe na Paris St-Germain da tawagar Faransa, Bradley Barcola, ya zama babban ɗan wasan da Liverpool ke son ɗauka a wanbnan bazarar; ƙungiyar ta filin wasan Anfield ta shirya biyan kusan fam miliyan 100, yayin da PSG ta ƙaƙabawa ɗan wasan farashin fam miliyan 145.

    Liverpool, wadda ta zo ta biyar a gasar Premier a kakar wasan da ta gabata da tazarar maki 25 tsakaninta da zakarun gasar, Arsenal - na iya biyan Bayer Leverkusen jimillar kuɗin da ya kai fam miliyan 116 a kan Wirtz, bayan da ta riga ta karya tarihin kashe kudi a ƙungiyar ta hanyar biyan fam miliyan 125 domin ɗauko Isak daga Newcastle.

    Yanzu kuma, ana iya ganin kungiyar ta kashe maƙudan kudade domin dauko Barcola mai shekaru 23, wanda ya kasance cikin tawagar Faransa a gasar cin kofin duniya.\

    Barcola ya koma PSG daga Lyon a shekarar 2023 kan kuɗin da aka bayyana cewa ya kai fam miliyan 38.5, kuma tun daga lokacin ya lashe kofunan Ligue 1 guda uku, da gasar French Cup sau biyu, tare da Kofin UEFA Super Cup da kuma Kofin FIFA Intercontinental Cup.

  4. An yi wa Salah tarbar gwarzo a Trabzonspor

    Salah

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Trabzonspor ta Turkiyya za ta tabbatar da siyan Mohamed Salah yayin da magoya bayanta suka yi masa tarba ta karamci a lokacin da ya isa Turkiyya.

    Ɗaruruwan magoya baya sun taru a wajen filin jirgin saman Ataturk da ke Istanbul ranar Laraba yayin da Salah ya fito sanye da kaya masu launukan Trabzonspor.

    Ɗan wasan gaban mai shekarA 34 ya bar Liverpool a Ƙarshen kakar wasa da ta gabata bayan shekara tara a Merseyside, inda ya zura ƙwallaye 257.

    Ba a tabbatar da albashin da Salah zai samu a Trabzonspor ba, amma tunda shi ɗan wasa ne mai zaman kansa, ƙungiyar Super Lig za ta iya ware wasu daga cikin kasafin kudinta don biyan albashinsa.

    Salah, wanda ya zura ƙwallaye 50 a gasar Champions League, zai buga gasar kwallon kafa na zakarun Turai da Trabzonspor a kakar wasa mai zuwa bayan ta ƙare a matsayi na uku, maki takwas a bayan zakarun Turkiyya Galatasaray.

  5. Kocin Cape Verde Bubista ya yi murabus yayin da Ivory Coast ta sake naɗa Renard

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bubista ya yi murabus daga muƙaminsa na babban kocin tawagar Cape Verde domin komawa kƙungiyar RS Berkane ta ƙasar Moroko, yayin da Ivory Coast ta ɗauki Herve Renard domin ya sake jagorantar tawagarta a karo na biyu.

    Bubista ya jagoranci ƙasar tsibirin zuwa matakin ƴan 32 na gasar cin kofin duniya a watan da ya gabata, inda tawagar ta 'Blue Sharks' ta sha kashi da ci 3-2 a hannun Argentina—wadda daga bisani ta zo ta biyu a gasar.

    Kocin mai shekara 56 ya kuma kai matakin daf da na kusa da na ƙarshe (quarter-final) a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2023 tare da Cape Verde, bayan ya fara jagorantar tawagar a watan Janairun 2020.

    Ya rattaba hannu kan kwantiragin shekara biyu da ƙungiyar RS Berkane, wadda ta zo ta biyu a gasar firimiya ta Moroko a kakar wasan da ta gabata; zai maye gurbin Moin Chaabani, wanda aka naɗa a matsayin sabon babban kocin Tunisia.

    Renard ya taba lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka (Afcon) sau biyu a matsayin koci, ciki har da nasarar da ya samu tare da Ivory Coast a shekarar 2015.

    A baya, ya jagoranci Zambia zuwa ga nasarar lashe kofin a shekarar 2012, abin da aka bayyana a matsayin wani gagarumin tarihi mai ban mamaki.

    Tun bayan barin Ivory Coast a watan Mayun 2015, Renard ya horas da tawagogin Moroko, da Saudiyya (sau biyu) da kuma tawagar mata ta Faransa, haka kuma ya jagoranci tawagar Tunisia a wasanni biyu a gasar cin kofin duniya ta bana.

  6. Mutane sun yi jerin gwano a titunan Milan domin jana'izar Franco Baresi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban mutane sun taru a titunan Milan ranar Talata don jana'izar fitaccen mai tsaron baya Franco Baresi.

    Ɗan wasan mai shekaru 66 ya rasu a makon da ya gabata bayan rashin lafiya.

    An ɗauke shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu tsaron baya da suka buga wasan, Baresi ya jagoranci Milan tsawon shekaru 15, inda ya buga wasanni 719 sannan ya zura ƙwallaye 33.

    Ɗan wasan na baya ya lashe kofuna 18 tare da Rossoneri da suka haɗa da gasar Serie A guda shida, da Champions League uku, da ItalianSuper Cup guda huɗu, kofunan Uefa Super Cup guda uku da kuma Club World Cup guda biyu.

    Ya buga wasanni 81 a Italiya kuma yana cikin tawagar da ta lashe gasar cin kofin duniya ta 1982.

    Ya buga kuma ya kasance kyaftin a wasan ƙarshe na 1994, wanda Italiya ta sha kashi a hannun Brazil.

    An naɗa Baresi shugaba na musamman na Milan a shekarar 2020, kuma an yi ratayar da rigarsa mai lamba shida lokacin da ya yi ritaya daga buga wasa.

  7. Norgaard na shirin raba gari da Arsenal

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An cire Christian Norgaard daga cikin tawagar Arsenal da za ta buga wasan sada zumunta da Real Betis a birnin Dublin, yayin da yake shirin komawa ƙungiyar Everton.

    Rahotanni sun nuna cewa Norgaard na shirin komawa Everton kan kuɗi kimanin fam miliyan bakwai.

    Ɗan wasan mai shekaru 32 ya kasance a cikin tawagar Arsenal a lokacin da suka doke Girona da ci 4-1 a makon da ya gabata, amma bai buga wasan ba, kuma yanzu yana shirin zuwa gwajin lafiya a Everton.

    Norgaard ya koma Arsenal ne a bazaran bara kan kudi fam miliyan 10, tare da yiwuwar karin fam miliyan 5 idan aka cika wasu sharuɗɗa.

    Sai dai ya sha wahalar samun damar buga wasa, inda ya buga wasanni bakwai kacal a gasar lig yayin da Arsenal ta lashe kofin.

    Wasan farko daya tilo da ya fara a gasar lig shi ne na ranar ƙarshe ta kakar wasan da ta gabata.

  8. An naɗa Taylor a matsayin shugaban alƙalan wasa a Turkiyya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An naɗa tsohon alƙalin wasa Anthony Taylor a matsayin darektan kula da manyan alƙalan wasa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Turkiyya (TFF).

    Taylor shekara 47 ya bayyana cewa yana "matuƙar farin ciki" da karɓar wannan muƙami.

    "Ina matuƙar farin cikin shiga hukumar ƙwallon ƙafa ta Turkiyya kuma ina fatan ganin abin da makomar wannan aiki za ta kawo," in ji shi.

    An yi wannan naɗin ne wata 10 bayan kammala bincike na tsawon shekara biyar, wanda ya gano cewa 371 daga cikin jami'an wasa 571 a Turkiyya suna da asusun yin caca.

    A lokacin, shugaban hukumar TFF, Ibrahim Haciosmanoglu, ya ce: "Idan muna son kai ƙwallon ƙafar Turkiyya matsayin da ya dace da ita, dole ne mu kawar da duk wani gurɓataccen abu da ke cikinta."

    A watan da ya gabata, Taylor ya sanar da yin ritaya daga aikin lafari bayan ya shafe shekaru 20 yana gudanar da wasanni; ya yi hakan ne bayan ya jagoranci wasan da Spain ta doke Portugal da ci 1-0 a zagayen ƴan 16 na gasar cin kofin duniya a ranar 6 ga watan Yuli.

    Ya jagoranci wasannin cikin gida na ƙwararru guda 668, tare da yin alƙalanci a gasar Euro ta 2020 da kuma gasar cin kofin duniya ta shekarun 2022 da 2026.

  9. Como ta cimma yarjejeniyar ɗaukar Chalobah daga Chelsea

    ...

    Asalin hoton, getty

    Ƙungiyar Como ta cimma yarjejeniyar da ta haura fam miliyan 30 don Ɗaukar Ɗan wasan baya na Chelsea, Trevoh Chalobah.

    Ana sa ran ɗan wasan mai shekara 27 zai rattaba hannu kan kwantiragin dogon lokaci tare da zama shugaba a bangaren yan wasan ƙungiyar a ƙarƙashin koci Cesc Fabregas a ƙungiyar ta Italiya, wadda ta samu tikitin shiga gasar Champions League bayan ta zo ta huɗu a gasar Serie A a kakar wasan da ta gabata.

    Chelsea za ta karɓi fam miliyan 25.7 a tashin farko, tare da ƙarin fam miliyan 5.1 da za a iya samu bayan an cimma wasu sharuɗɗa.

    Wannan yarjejeniya ta yi daidai da kudin da Chelsea ke buƙata kan ɗan wasan, wato fam miliyan 30 da karin fam miliyan 5, bayan an samu tayi da dama tun farkon watan Yuni, tare da sha'awar da ƙungiyar Inter Milan ta nuna.

    Fabregas, tsohon ɗan wasan tsakiya na Chelsea da Arsenal, ya nuna matuƙar sha'awar ɗaukar Chalobah kuma ya daɗe yana zawarcinsa na tsawon sama da watanni shida.

    Ɗan wasan na Ingila zai bar ƙungiyar da ya taso a cikinta bayan kusan shekaru 20, kasancewar ya koma Chelsea ne tun yana yaro.

  10. Mudryk na iya dawowa ranar Laraba bayan dakatarwar da aka yi masa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana sa ran Mykhailo Mudryk zai koma filin wasa a ranar Laraba bayan ya shafe watanni 20 ba ya buga wasa, sakamakon sanya sunansa a cikin tawagar Chelsea da za ta kara da Juventus a wasan sada zumunta a Hong Kong.

    Ɗan wasan na Ukraine mai shekara 25 bai buga wani muhimmin wasa ba tun watan Nuwamban 2024, bayan an dakatar da shi na wucin-gadi saboda samun sakamakon gwaji mai nuna kasancewar haramtaccen sinadarin 'meldonium' a jikinsa.

    Sai dai an ba shi damar komawa buga wasa a makon da ya gabata bayan ya sasanta batunsa da Hukumar Kwallon Kafa.

    Sabon kociyan Chelsea, Xabi Alonso, ya ce: "Eh, zai iya buga wasa. Watakila ba zai iya buga minti 90, amma ana iya zaɓarsa. An zaɓe shi, don haka zai iya buga wasa.

    "Ya yi atisaye jiya, inda ya zo kai tsaye daga filin jirgin sama zuwa otal. Don haka, abin da aka fi mayar da hankali a kai jiya shi ne yanayin sake haɗuwa da sauran ƴan wasa domin tantance yanayin lafiyar jikinsa."

  11. Arsenal na tattaunawa kan ɗaukar Guimaraes daga Newcastle

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal na tattaunawa kai tsaye da Newcastle United domin ɗaukar kyaftin din ƙungiyar, Bruno Guimaraes.

    An fahimci cewa ƙungiyoyin biyu na gudanar da tattaunawa ta kai-tsaye game da ɗan wasan tsakiyar, bayan da aka yi tattaunawar farko ta hanyar masu shiga tsakani.

    Guimaraes, mai shekara 28, na son komawa ƙungiyar da ta lashe gasar Premier League a kakar da ta gabata.

    Ana jiran a ga ko za a cimma yarjejeniya, amma waɗanda ke da hannu a lamarin suna ganin cewa ana samun ci gaba wajen cimma matsaya kan batun sauya sheƙar tasa.

    A baya dai BBC Sport ta rawaito cewa Arsenal za ta buƙaci ƙari kan tayin da ta yi na fam miliyan 70 ta hanyar masu shiga tsakani a watan da ya gabata.

    Wata majiya a Newcastle ta bayyana cewa ƙungiyar ta yi watsi da tayin da Arsenal ta yi na farko.

    Duk da cewa tayin da Arsenal ta yi bai yi nasara ba - kuma babu ɓangaren da ya bayyana adadin kuɗin - ana sa ran za su sake dawowa da wani tayi mai tsoka.

  12. Fulham ta ɗauki Garcia da Palacios daga Real Madrid

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Fulham ta ɗauki Gonzalo Garcia da Cesar Palacios daga Real Madrid kan kwantiragin shekaru biyar.

    Garcia, mai shekaru 22, ya buga wa babbar ƙungiyar ta ƙasar Spain wasanni 39 a kakar wasan da ta gabata, inda ya zura ƙwallaye takwas a dukkan gasa da suka fafata.

    Ɗan wasan gaban, wanda ya fara buga wa tawagar kasar Spain wasa a watan Yuni, zai sake haɗuwa da sabon kocin Fulham Alvaro Arbeloa—wanda suka taɓa aiki tare a filin wasa na Bernabeu—kan kuɗin da aka kiyasta ya kai fam miliyan 34.

    Ɗan wasan gaban wanda ya fi kowa zura ƙwallaye a gasar cin kofin duniya ta Club World Cup a bazarar da ta gabata, zai haɗe da tsohon abokin wasansa na Real, Palacios a Craven Cottage.

    Ɗan wasan tsakiya mai shekaru 21, shi ma ya isa Fulham ne kan kwantiragin da zai kai bazarar 2031, kodayake kulob ɗin yana da zaɓin tsawaita kwantiragin ƴan wasan biyu da wata 12.

    Palacios ya buga wasanni biyar a babbar ƙungiyar Real - duk daga benci - kuma ya buga wa Spain wasa a matakin ƴan ƙasa da shekara 20.

  13. Real za ta ci gaba da tattaunawa da Vinicius Jnr

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Vinicius Jr zai ci gaba da tattaunawa kan kwantiragi da Real Madrid a wannan makon yayin da zakarun gasar Premier Arsenal ke ci gaba da nuna sha'awa kan ɗan wasan gaba.

    Ƙungiyar ta arewacin Landan ta bayyana ɗan wasan na Brazil a matsayin wanda ta ke sanya wa ido idan har aka kasa warware matsalar kwantiraginsa.

    Amma, yayin da ake sa ran ɗaya daga cikin ƴan wasan gaba masu hazaƙa a duniya zai koma arewacin Landan, akwai rashin tabbas game da ko ɗan wasan zai tafiya a wannan bazarar.

    Wannan rashin tabbas ya faru ne saboda wakilan Real Madrid da Vinicius Jr sun kwashe wata 18 asuna ta tattaunawa kan sabuwar kwantiragi.

    Kwantiraginsa na yanzu dai zai ƙare ne a 2027.

  14. Dan wasan tsakiyar Ingila Henderson ya koma Chelsea

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan tsakiya na Ingila, Jordan Henderson, ya koma ƙungiyar Chelsea kan kwantiragin shekara biyu bayan an amince a soke kwantiraginsa da Brentford.

    Henderson, mai shekara 36, shi ne ya jagoranci Liverpool a matsayin kyaftin har suka lashe gasar Premier League a kakar 2019-20, sannan ya kuma lashe gasar Champions League da FA Cup, da League Cup (sau biyu) da UEFA Super Cup da kuma FIFA Club World Cup a lokacin da yake ƙungiyar ta Anfield.

    A shekarar 2023, ya koma ƙungiyar Al-Ettifaq ta Saudiyya, kafin daga bisani ya koma Ajax ta Netherlands a watan Janairun 2024; daga nan kuma ya dawo gasar Premier League tare da Brentford a lokacin bazara na bara, inda ya buga wasanni 32 a babban matakin gasar a kakar 2025-26.

    Chelsea ta kammala kakar wasan da ta gabata a matsayi na 10 a gasar Premier League—kuma ta gaza samun tikitin shiga gasar ƙwallon ƙafa ta zakarun Turai.

    Sabon koci Xabi Alonso ya kasance mai himma a kasuwar musayar ƴan wasa, inda Henderson ya zama dan wasa na 10 da ya koma ƙungiyar ta Blues a wannan lokacin na bazara.

  15. Pochettino ya amince da tsawaita kwantiraginsa a matsayin kocin Amurka

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Mauricio Pochettino ya cimma yarjejeniyar ci gaba da zama kociyan tawagar ƙwallon ƙafa ta maza ta Amurka har zuwa shekarar 2030.

    Tsohon kociyan kungiyoyin Tottenham da Chelsea, wanda ya fara riƙe muƙamin a watan Satumbar 2024, ya jagoranci Amurka — ɗaya daga cikin ƙasashen da za su ka karɓi baƙuncin gasar cin kofin duniya — ​​zuwa matakin ƙungiyoyi 16 na gasar, kafin daga bisani Belgium ta doke su.

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Amurka (US Soccer) ta bayyana cewa, sabuwar yarjejeniyar ta ƙunshi faɗaɗa ayyukan Pochettino da tawagarsa ta masu horaswa, inda za su rika bayar da shawara da tallafi ga hukumar kan batutuwan da suka shafi ci gaban tsarin tawagar ƙasa baki ɗaya.

  16. Chelsea ta ɗauki ɗan wasan tsakiya, Barco daga Strasbourg

    ...

    Asalin hoton, getty

    Chelsea ta kammala ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Strasbourg, Valentin Barco, kan kwantiragin shekara bakwai.

    Matashin mai shekara 21 ya zama ɗan wasa na shida da Chelsea ta ɗauka a wannan bazarar, bayan zuwan Morgan Rogers da Danny Welbeck da Emmanuel Emegha da Maxence Lacroix da kuma Marco Palestra.

    Ɗan wasan tsakiyar zai haɗe da sauran tawagar Chelsea a rangadin shirye-shiryen tunkarar kakar wasa mai zuwa, inda za su kara da ƙungiyar Juventus ta Italiya a Hong Kong a ranar 5 ga watan Agusta.

    Chelsea ba ta bayyana kuɗin da aka kashe wajen ɗaukar ɗan wasan ba.

    Barco ya buga wa Argentina wasa ɗaya a gasar cin kofin duniya ta 2026, inda suka zo na biyu bayan Spain - kuma Jude Bellingham ya mare shi bayan nasarar da suka samu kan Ingila a wasan kusa da na ƙarshe.

    Barco, wanda ya fito daga makarantar horar da matasa ta Boca Juniors, ya koma Brighton a shekarar 2024 kan kuɗi £7.9m.

    Sai dai ya shafe shekara ɗaya ne kawai a yankin kudancin ƙasar, sannan ya koma Strasbourg a lokacin bazara mai zuwa bayan ya kammala wa'adin zaman aro a ƙungiyar.

  17. Newcastle ta sayi golan Braga Hornicek kan fam miliyan 25.7

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Newcastle United ta Ɗauki mai tsaron raga Lukas Hornicek daga Sporting Braga kan kuɗi £25.7m.

    Duk da cewa tuni Newcastle ta dauki Ewen Jaouen, mai shekaru 20, daga ƙungiyar Reims a wannan bazara, ƙungiyar ta kuma kasance tana neman mai tsaron raga na farko wanda ya riga ya ƙware sosai a fagen.

    Hornicek, mai shekara 24, ya tafi sansanin horar da ƴan wasa na Newcastle da ke ƙasar Spain a ƙarshen mako domin kammala yarjejeniyar komawarsa da kuma sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyar, bayan da ƙungiyar ta biya kuɗin da aka ƙayyade na sakin ɗan wasan daga tsohuwar ƙungiyarsa.

  18. Hukumar ƙwallon kafar Ingila za ta janye goyon bayanta ga shugaban FIFA

    Infantino

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila za ta rubuta wa shugaban Fifa Gianni Infantino takardar janye goyon bayan da take ba shi a daidai lokacin da ya samu koma baya a shirinsa na sayar da hannun jari a gasannin Fifa ga masu zuba jari masu zaman kansu.

    Wannan ya zo ne yayin da UEFA ke barazanar ɗaukar matakin shari'a kan shawarwarin kuma hukumar ƙwallon ƙafar Wales ta janye goyon bayanta a bainar jama'a ga yunƙurin Infantino na ci gaba da shugabancin Fifa.

    A watan Maris mai zuwa, Infantino zai tsaya takara a karo na huɗu kuma na ƙarshe a matsayin shugaban FIFA kuma zai buƙaci ƙuri'u 106 daga mambobin Fifa 211 domin ya yi nasara.

    Majiyoyi sun shaida wa BBC cewa matsayin hukumar FA na Scotland kan makomar Infantino ya ci gaba da kasancewa daidai da na rashin kwarin gwiwar UEFA a kansa.

    Hukumomin ƙwallon ƙafa na Turai, da na Arewacin Amurka da Tsakiyar Amurka da Caribbean sun riga sun ƙalunblanci shugabancin Infantino a bainar jama'a, inda Uefa da Concacaf suka fitar da kalamai suna sukar shirye-shiryen.