Shin ƙarin albashi ga sojoji zai iya magance matsalar tsaron Najeriya?

Dakarun Rundunar Operation Hadin Kai mai fada da mayakan Boko Haram

Asalin hoton, @HQNigerianArmy

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Masana sun fara tsokaci game da ƙarin albashi da gwamnatin Tinubu ta sanar da yi wa sojojin ƙásar daga kashi 30 zuwa 80 cikin dari.

Shugaban Najeriya Bola Ahemd Tinubu ya amince da ƙarin albashi da ya kai kashi 30 zuwa 80 ga dakarun sojojin Najeriya.

Karin albashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Satumbar 2026, kamar yadda wata sanarwar daga fadar shugaban ƙasar ta bayyana a ranar Talata.

Sanarwar ta ce sojojin Najeriya aƙalla 250,000 ne ake tsammanin za su amfana da wannan sabon ƙarin albashi.

Masana harkokin tsaro sun ce duk da ƙarin albashi mataki ne mai kyau, amma matsalar tsaro da ta addabi Najeriya ta wuce batun albashi kaɗai.

Dr Kabiru Adamu masanin harkokin tsaro ya shaida wa BBC cewa babu shakka inganta walwala da yanayin aiki da albashi na jami'an tsaro na cikin abubuwan da ke taimakawa wajen ƙarfafa masu guiwa da ba su kuzari wajen gudanar da ayyukansu.

Masanin ya ce Idan aka yi la'akari da hatsarin da aikinsu ke saka su ciki na tsaron ƙasa ya kamata albashinsu ya fi na sauran ma'aikata da aƙalla kashi saba'in da biyar cikin ɗari.

A cewar sa, ya kamata akwai tsarin da za a riƙa waiwaye ta yadda albashin zai riƙa ƙaruwa.

Dr Kabir Adamu ya ce bayan batun albashin abu mai mahimmanci shi ne ɓangaren kayan aiki.

"Wani abu da yake tayar man da hankali shi ne yadda za a ce akwai dakaru a filin yaƙi amman suna cikin motocin da ba na sulke ba, hakan kuskure ne kuma hatsari ne sosai," in ji masanin.

Ya kara da cewa duk da kayan aikin su da suka haɗa da makamai da kayan da suke sakawa na kariya da yawan su da juye da ya kamata a ce ana masu da ba da taimakon gaggawa na rashin lafiya da ƙara masu muƙami duk abubuwa ne da za su taimaka wa jami'an tsaro wajen yin aikinsu.

Ƙarƙashin sabuwar sanarwar, jami'an da suke daga matsayin kanar zuwa birgediya janar da manjo janar da laftanar janar da janar duka za su samu ƙarin kashi 30 ne cikin 100.

Tun daga matsayi na ɗaya da ake kira laftanar na biyu da laftanar da manjo da zuwa laftanar kanar za su samu ƙarin kashi 80 cikin 100 na ƙarin albashin.

Yanzu ƙunshin albashin sojojin na shekara zai tashi daga naira biliyan 660 zuwa naira biliyan 924.

Shugaba Tinubu ya ce an ɗauki matakin ne saboda cika alƙawarin gwamnatinsa na "kyautata rayuwar sojoji da suke yaƙi da matsalolin Najeriya irin su ɓarayin daji, da masu satar mutane domin neman kuɗin fansa da 'yanta'adda da suka addabi ƙasar"

Me Najeriya ta fi buƙata?

Dr Kabiru Adamu ya ce dangane da abin da aka fi buƙata tsakanin abubuwan guda biyu, a iya cewa kayan aiki da fasahohin zamani ne gaba sai kuma yawan sojoji.

''Duk da cewa ana buƙatar yawan sojojin da su yi aiki da waɗannan sabbin fasahohin amma dai kayan aikin da kuma sabbin makaman su ne kan gaba'', a cewar sa.

'Yanzu idan ka duba yaƙin Rasha da Ukraine lokacin da aka fara shi, kowa ya yi tsammanin yaki ne irn wanda aka saba gani a baya za a yi, amma daga baya kowa ya ga yadda ake yin yaƙin ta hanyar amfani da sabbin fasahohin makamai na zamani'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Abu huɗu ne ke tantance ƙarfin soji

Masanin tsaron ya ce akwai abubuwa guda huɗu mafiya muhimmanci ga kowace ƙasa game da rundunar sojinta, kamar haka:

  • Yawan sojoji da ingancinsu

Wannan ya shafi horon da tsarin shugabanci da kulawa da rundunar sojin ke samu na abin da ya shafi haɗin gwiwa.

''Wannan shi ne abu na farko dangane da ingancin rundunar soji a kowace ƙasa'', in ji shi

  • Kimiyya da fasaha

Wannan ya shafi irin sabbin fasahohin zamani da rundunar sojin ke amfani da iuta wajen aiwatar da ayyukanta.

''Wannan ya ƙunshi fasahohin tattara bayanan sirri ta tantance su, da yadda ake rarraba wa sojojin kayan aikin da suke bukata'', a cewar Dr Kabiru Adamu.

  • Yanayin siyasar Kasar

Wannan ya shafi yadda ƙasa ta fahimci tsaro ta kuma ɗauke shi da muhimmanci, da sanya idanu a ɓangaren tsaron ba tare da yin katsalandan ga buƙatar jami'an tsaron.

"Hakan zai taimaka matuƙa wajen ƙarfin soji da tsaron kowace ƙasa'', in ji shi.