Matasan arewacin Najeriya 10 da Tiktok ya ɗaukaka

Matasan da suka yi suna a Tiktok a a arewacin Najeriya

Asalin hoton, Tiktok

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Tun bayan da manhajar TikTok ta fara samun karɓuwa a Najeriya a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2025, ta zama wata babbar dama ga matasa da dama, inda wasu suka yi fice cikin ƙanƙanin lokaci.

Ta hanyar ƙirƙirar gajerun bidiyoyi na barkwanci, nishaɗi, wa'azi, ilimantarwa ko tattauna al'amuran yau da kullum, wasu sun tara miliyoyin mabiya, lamarin da ya buɗe musu ƙofofin samun kuɗi da damar tallata hajojinsu ko ayyukansu.

Sai dai shafin ya kuma kasance dandalin cece-ku-ce, domin ana yawan samun saɓani tsakanin fitattun masu amfani da shi.

A wasu lokutan hakan kan kai ga rufe shafukansu, amma abin da ke ɗaukar hankali shi ne yadda da yawa daga cikinsu ke sake buɗe sabon shafi su kuma dawo da ɗimbin mabiyansu cikin ɗan lokaci.

A Arewacin Najeriya, TikTok ya zama ɗaya daga cikin kafafen sada zumunta da matasa suka fi runguma.

Sai dai akwai masu suka da ke ganin wasu daga cikin masu amfani da dandalin na neman shahara ne ta hanyar amfani da kalamai marasa daɗi, zage-zage ko kuma abubuwan da suka saɓa wa al'ada domin jan hankalin masu kallo.

Ga wasu daga cikin matasan da TikTok ya zama silar ɗaukakarsu a Arewacin Najeriya.

Youngalajerh

Youngalajerh

Asalin hoton, Youngalajerh/TikTok

Ahmad Young Alajerh Dayyabu, wanda aka fi sani da Youngalajerh, na ɗaya daga cikin fitattun masu amfani da TikTok a Arewacin Najeriya, kuma shi ne wanda ya fi kowa yawan mabiya a dandalin daga yankin.

Ya yi fice ne ta hanyar wallafa bidiyoyin karatun Alƙur'ani mai girma da kuma saƙonnin wa'azi masu ratsa zuciya.

A halin yanzu yana da fiye da mabiya miliyan 12 a shafinsa na TikTok.

A yawancin bidiyoyinsa ya kan yi amfani da karatun Alƙur'ani, musamman na fitaccen alaramman ƙasar Yemen, Sheikh Muhammad Al Faqih, abin da ya ƙara jawo masa dimbin mabiya daga Najeriya da sauran ƙasashe.

G-Fresh Alameen

G-Fresh Alameen
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ainihin sunansa Alameen Ibrahim amma an fi saninsa da G-Fresh, ko kuma "Kano State Material", sunan da ya riƙa amfani da shi wajen gabatar da kansa a TikTok.

Ya yi fice ne ta hanyar bidiyoyin barkwanci, waƙoƙi da kuma hirarraki kai-tsaye, musamman waɗanda yake gudanarwa cikin dare tare da mabiyansa. Yana son yin turanci.

G-Fresh na ɗaya daga cikin fitattun masu amfani da TikTok a Arewa, inda asusunsa ke da miliyoyin mabiya. Yana yawan amfani da wasu kalaman da ake ganin ba su da ce, inda shi ma yake kiran kansa da "Shugaban ƴan kwalta na TikTok".

Ya kuma riƙa jan hankali sabooda auren da ya yi da wasu fitattun mata masu amfani da TikTok, daga haka su ma suke zama sanannu ko kuma dama can sanannu ne.

A yau, idan aka ambaci fitattun masu tasiri a TikTok a Arewacin Najeriya, G-Fresh na daga cikin sunayen da kan fara zuwa a zukatan mutane.

Hukumar Hisbah a Kano ta sha gayyatarsa domin yi masa nasiha kan wasu bidiyoyin da ake ganin ba su dace ya riƙa sakinsu ba.

Murja Kunya

Murja Kunya

Asalin hoton, fb/Murja Kunya

Murja Ibrahim Kunya na daga cikin waɗanda dole a kira ta a ta biyu cikin fitattun mutane a TikTok saboda yadda yi ƙaurin suna a shafin da tarin mabiyanta.

A shekarun baya, hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta taɓa gurfanar da ita kan zargin wallafa bidiyoyin da ta ce sun saɓa wa tarbiyya da ƙa'idodin zamantakewa.

A shekarun baya, hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta taɓa gurfanar da ita kan zargin wallafa bidiyoyin da ta ce sun saɓa wa tarbiyya da ƙa'idodin zamantakewa.

Haka kuma, ta taɓa shiga hannun Hukumar EFCC bayan wani bidiyo da ya nuna tana wulaƙanta takardun kuɗin Najeriya (Naira), tare da yanke mata hukuncin ɗaurin wata shida ko zaɓin tara.

Duk da cewa an sha rufe wasu daga cikin shafukanta na TikTok, Murja kan sake buɗe sabbin shafuka, kuma cikin ɗan lokaci ta kan sake tara dimbin mabiya.

Aminu J Town

Aminu J Town

Asalin hoton, Aminu J Town/FB

Aminu J Town na ɗaya daga cikin fitattun ƴan TikTok daga Arewacin Najeriya.

Yana yawan yin sharhi kan lamuran da suka shafi arewaacin Najeriya, musamman kan tsaro da kuma wasu abubuwan da suka shafi al'umma.

Ya yi suna saboda yadda wasu ke ganin yana yawan tsage gaskiya komai ɗacinta.

Sadiya Haruna

Sadiya Haruna

Asalin hoton, Sadiya Haruna/TikTok

Sayyada Sadiya Haruna aka fi saninta da shi. Ita ce matar da G Fresh ya fara aure daga haduwar TikTok.

Ko da yake ta shahara sosai kafin aurensu da shi, amma kuma suna yawan ɓatawa su shirya. Aurensu ya mutu kafin kowannensu ya sake wani auren, inda daga baya suka sake haɗewa bayan sake mutuwar aurensu.

Sadiya tana yawan hawa waƙoƙin bege, amma kuma wasu na yawan cece-ku-ce kan yanayin abubuwan da take yi a TikTok.

Tana daga cikin waɗanda suka samu ɗaukaka sosai daga shafin TikTok.

Kotu ta taɓa yanke wa Sadiya Haruna hukuncin ɗaurin-talala na wata shida, inda aka yi umarni ta riƙa zuwa makarantar Islamiyya domin koyon "tarbiyya" da kuma "sanin yadda za ta riƙa mu'amala a matsayinta na Musulma".

Maryam Nicki Minaj

Maryam Nicki Minaj

Asalin hoton, Maryam Nicki Minaj/TikTok

Maryam, wadda aka fi sani a TikTok da "Nicki Minaj", ta fara samun ɗaukaka ne bayan aurenta da G-Fresh.

Tun bayan aurensu, G-Fresh ya riƙa kiran ta da sunan Nicki Minaj, wanda daga baya ya zama sunan da mutane suka fi amfani da shi wajen kiranta a kafafen sada zumunta.

Maryam ƴar jihar Adamawa ce, kuma duk da cewa tana da nata mabiya a TikTok tun kafin aurensu, dangantakarta da G-Fresh ta ƙara mata farin jini, inda mutane da dama suka fara bibiyar abubuwan da take wallafawa.

Sai dai bayan kusan shekaru biyu suka rabu. Bayan rabuwar, Maryam ta ci gaba da amfani da TikTok sosai.

Hassan MakeUp

Hassan Makeup

Asalin hoton, Hassan Makeup/Tiktok

Duk da yake cewa Hassan Make Up ɗan asalin Jamhuriyar Nijar ne, amma kuma yawancin bidiyoyinsa suna ɗaukar hankali ne a arewacin Najeriya.

Yana yawan zama Najeriya kasancewar yawancin abokansa da abokan hulɗarsa na kasuwanci suna zaune a ƙasar. Hakan ya sa bidiyoyinsa suka fi samun karɓuwa a tsakanin masu amfani da TikTok a Arewa.

Ya yi suna ne ta hanyar bidiyoyin kwalliya, nishaɗi da kuma salon rayuwarsa. Wasu na sukar salon shigarsa da irin tufafin da yake sanyawa a bidiyoyinsa, inda wasu ke ganin ya saɓa da abin da suka saba gani.

Yana yawan kace-nace da masu amfani da shafukan, lamarin da ke kai wa har ga a yi zage-zage.

Mai Wushirya

Idris Mai Wushirya

Asalin hoton, Mai Wushirya/Tiktok

Idris Mai Wushirya na daga cikin matasan da TikTok ya yi silar ɗaukakar su a Arewacin Najeriya ta hanyar bidiyoyin barkwanci da nishaɗi.

Sai dai abin da ya fi ƙara masa shahara shi ne cece-ku-cen da suka biyo bayan kama shi da Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab'i ta Jihar Kano a shekarar 2025, bisa zargin wallafa bidiyoyin da aka ce sun saɓa wa al'ada da tarbiyya.

Daga baya kuma ya sake ɗaukar hankalin jama'a lokacin da wata kotun majistare a Kano ta umarce shi da ya auri fitacciyar mai amfani da TikTok, Basira Yar Guda, bayan sun bayyana cewa suna soyayya a shafin.

Sai dai daga bisani batun auren bai tabbata ba, bayan bincike da kuma bayanan da suka fito game da yadda lamarin ya kasance.

Rahama Saidu

Rahama Saidu

Asalin hoton, Rahama Saidu/IG

Rahama ƴar kasuwa ce da ta shahara a TikTok tun bayan da aka sallame te daga makarantar koyon aikin jinya da Ungonzoma ta jihar Kebbi saboda bidiyoyin da take wallafawa a shafinta na Tiktok.

Makarantar ta kafa hujja da cewa bidiyoyin da take yi sun saɓa da al'ada da tarbiyyar makaranta.

Amma za a iya cewa hakan ya zame mata gobarar titi, domin a cewarta tun bayan sallamarta daga makaranta ta samu damar maida hankali a kasuwancinta kuma ta buɗe shaguna da dama.

Hakan ya jawo mata ɗaukaka sosai a TikTok.

Aminu Warkal

..

Asalin hoton, Warkal/Facebook

Aminu Abdullahi da aka fi sani da Warkal, ɗan siyasa ne kuma yana yawan wallafa bidiyoyin sharhi kan lamuran siyasa musamman a jihar Kano da Kwankwasiyya.

Wasu bidiyoyin nasa sun haifar da cece-ku-ce da kuma janyo masa farin jini ga masu bibiyar siyasa.

Sauran waɗanda ke kan ganiyarsu

Akwai wasu ƙarin mutanen kuma da suka shahara a TikTok amma za a iya cewa a yanzu ne suka cin ga niyarsu ko kuma sun yi suna a baya ta fannoni daban-daban kuma suna daga cikin waɗanda wasu ke kallo a matsayin abin koyi.

Daga cikin waɗanda ke kan sharafinsu a yanzu akwai;

  • Baddoo: Ɗan TikTok ne da ya karkata kan harkokin nishadi da barkwanci, inda ya fara ja zarensa a shafin kuma ya tara ɗimbin mabiya.
  • Londonbe - Ƴar siyasa: Shafa'atu Ahmedfitacciyar ƴar siyasa ce da ke amfani da TikTok, kuma tsohuwar shugabar mata a ƙungiyar Kwankwasiyya a Jihar Kano.
  • Sharfadden Bature: Sharfaddeen na daga cikin matasa masu fufutuka a siyasa da ƙoƙarin kawo sauyi. Yana yawan yin tsokaci kan harkokin ci gaban matasa a shafukan sada zumunta, kuma TikTok na ɗaya daga cikin manhajojin da suka sa ya yi suna.
  • Hausa Guy: Dan jarida ne da ke wallafa bidiyo a kafafen zamani kuma yaa da ƙwarewa a harkokin hulɗa da jama'a.
  • Abba MD
  • Alpha Charles Borno - Nishaɗi
  • Babiana (Queen of Update) - Nishaɗi
  • Khadija Mai bakin Kiss - Nishadi
  • Abdul D One