Masu riƙe da muƙamai 5 da aka taɓa yin garkuwa da su a arewacin Najeriya

Asalin hoton, Facebook/Multiple
Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce tana ci gaba da ƙoƙarin ceto Alƙalin Babbar Kotu a jihar Kebbi mai shari'a Faruku Hassan Bunza da ƴanbindiga suka sace.
A ranar Asabar ne da daddare ne wasu ƴanbindiga ɗauke da makamai suka auka gidan alƙalin tare da sace shi.
Bayanai sun ce alƙalin ya koma gidansa daga bulaguron da ya yi zuwa jihar Sokoto kafin faruwar lamarin.
Kwamishinan ƴansandan jihar CP Umar Muhammad Haɗejia ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Asabar.
Tuni dai iyalansa suka yi kira da jami'an tsaro da hukumomi su tsananta ƙoƙari domin ceto shi.
Sace alƙalin na zuwa ne kwana guda bayan da wasu ƴanbindiga suka sace shugaban ƙaramar hukumar Bungudu da ke jihar Zamfara mai maƙwabtaka.
Ba wannan ne karon farko da ƴanbindiga a arewacin ƙasar ke sace masu riƙe da muƙamai ba.
A wannan muƙala mun duba wasu fitattun masu riƙe da muƙamai da ƴanbindigar suka taɓa sacewa a arewacin ƙasar.
Shugaban ƙaramar hukumar Bungudu

Asalin hoton, Facebook/ Jameel Bungudu
A ranar Juma'a a daddare ne wasu ƴanbindiga suka ƙaddamar da hari a garin Bunguɗu a jihar Zamfara, inda suka yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Nura Umar Bungudu da kuma wasu daga cikin makusantansa.
Rahotanni sun ce ƴanbindigar sun kutsa garin tare da tafiya kai-tsaye zuwa gidan shugaban ƙaramar hukumar da ke unguwar Zango.
Bayan shugaban ƙaramar hukumar, maharan sun yi garkuwa da wani ma'aikacin asibitin tarayya da ke Gusau da wani mai sana'ar cire ta kuɗi ta POS a yankin.
Haka kuma rahotannin sun ƙara da cewa harin ya yi sanadiyar mutuwar jami'an tsaro, ciki har da ƴansanda da ƴan sa-kai.
Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta ce jami'anta na bibiya tare da yunƙurin ceto shi.
Sarkin Gobir
Sarkin Gobir na garin Gatawa, Marigayi Alhaji Isa Bawa na ɗaya daga cikin fitattun masu riƙe da mukamai daga faɗa hannun ƴanbindiga a arewacin Najeriya, wanda kuma har ya mutu a hannunsu.
Wani ɗan sarkin na ya ce an kama mahaifin nasa ne a wani kwanton-ɓauna a yankin Kwanar Maharba yayin da yake komawa gida daga wani taro da ya halarta.
Marigayin ya shafe makonni masu yawa a hannun masu garkuwar waɗanda suka riƙa yi masa bidiyon cin zarafi.
Hon Sani Bello, ɗanmajalisar wakilai
A ranar 2 ga watan Agustan 2016 ƴanbindiga suka sace Hon. Sani Bello ɗan majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar Mashi/Dutsi a jihar Katsina a gonarsa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Bayanai sun ce ƴanbindigar sun saki bayan kwanaki uku a hannu, bayan biyan kuɗin fansa.
Daga bisani ƴansandan sun ce sun samu nasarar kama maharan a wani yanki na jihar Katsina, waɗanda kuma suka tabbatar da cewa su ne suka maka Hon. Bello.
Shugaban UBEC
Shi ma tsohon shugaban hukumar ilimin bai ɗaya ta Najeriya, UBEC, DR Mahmood Abubakar ya taɓa faɗa wa komar ƴanbindiga a lokacin da yake kan muƙaminsa.
A lokacin bayanai sun ce ƴanbindigar sun sace shi a kan babban titin Abuja zuwa Kaduna tare da ɗaya daga cikin ƴaƴansa.
A lokacin faruwar lamarin ƴanbindigar sun harbe direbansa, wanda ya mutu nan take.
Daga baya jami'an tsaro sun samu nasarar kuɓutar da su daga hannun masu garkuwar, tare da kama wasu daga ciin masu garkuwar.











