Abincin Afirka 5 da kimiyya ta tabbatar da matuƙar amfaninsu ga lafiya
Daga zogale zuwa hatsin Acha, tare da kuka, dawa zuwa hatsin Teff akwai nau'o'in abinci da dama na Afirka da suka yi suna saboda yalwar sinadaransu masu inganta lafiya.
Wasu daga cikinsu ma ana ɗaukar su a matsayin abinci masu matuƙar amfani ga lafiya, sakamakon yawan sinadarai masu gina jiki da suke ɗauke da su da kuma fa'idoji masu yawa da suke bayarwa ga jiki.
Mu duba wasu daga cikinsu.
1- Zogale

Asalin hoton, Getty Images
Ana yawan yi wa zogale laƙabi da "itaciyar al'ajabi" saboda dimbin amfanin da ake dangantawa da ita ga lafiya. Zogale na daga cikin tsirran da suka fi yalwar sinadarai masu gina jiki.
Yana ɗauke da bitamin A da C, sinadarin gina jiki na protein, sindarin iron da kalmatako, sinadarin potassium, magnesium, mai, sinadaranan ƙarin kuzari da kuma harza, abin da ya sa yake da matuƙar amfani ta fuskar abinci mai gina jiki.
Asalinsa daga Afirka da Kudancin Asiya ne, kuma an san zogale da taimakawa wajen kare ƙwayoyin jiki daga lalacewa saboda sinadaransa masu yaƙi da Sinadarai masu haifar da lalacewar ƙwayoyin jiki.
Ko da yake ganyensa ne ya fi daraja saboda yawan sinadarai masu gina jiki da yake ɗauke da su, kuma ana iya cin danyensa ko a busar da shi, ko a niƙa shi, ana kuma amfani da sauran sassan itaciyar kamar ƙwayoyinsa, furanninsa, saiwoyinsa da kuma bawonsa.
Bugu da ƙari, waɗannan sinadarai masu yaƙi da abubuwan da ke lalata ƙwayoyin halitta da zogale ke ɗauke da su na taimakawa wajen inganta aikin ƙwaƙwalwa da tunani. Saboda haka, suna iya taka rawa wajen yaƙi da cututtukan da suka shafi mantuwa.
Binciken gwaje-gwaje ya nuna cewa wasu sinadarai da ake cirewa daga ganyen zogale, 'ya'yan itacensa ko saiwoyinsa na iya yin tasiri a kan hanyoyin da jiki ke bi wajen haifar da kumburi.
2- Accha

Asalin hoton, Getty Images
Acha na daga cikin tsofaffin nau'in hatsi da aka daɗe ana nomawa a Afirka ta Yamma, inda tarihinsa ya kai fiye da shekaru 5,000. Ana noma shi a kusan ƙasashe goma na yankin, ciki har da Guinea, Mali, Benin, Senegal, Burkina Faso, Togo da Nijar.
Saboda ƙwayoyinsa masu matuƙar ƙanƙanta da suke kama da yashi, wasu lokuta ana kiran Acha da suna "hatsin ƙananan ƙwayoyi". Duk da ƙanƙantarsa, ya shahara saboda yalwar sinadaransa masu gina jiki da kuma sauƙin narkewarsa a jiki.
Acha ba ya ɗauke da sinadarin gluten, kuma yana da wadataccen ƙarfe (iron), magnesium, zinc, calcium da kuma sinadarin da ke ƙara harza. Daga cikin amfaninsa akwai taimakawa wajen yaƙi da ƙarancin jini, rage damuwa da kuma ƙarfafa garkuwar jiki.
Masana harkar abinci da lafiya suna ba da shawarar a riƙa shan isasshen ruwa yayin cin Acha domin sauƙaƙa narkewarsa a jiki da kuma taimakawa wajen shanye sinadaransa masu amfani.
3 - Kuka

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wata shahararriyar itaciya ta nahiyar Afirka ita ce kuka. Ba wai 'ya'yanta kaɗai ake amfani da su ba, har da ganyenta.
Ana matuƙar amfani da 'ya'yan kuka wajen yin abin sha. Domin haɗa shi, ana jika ɓangaren cikin 'ya'yan a ruwa, sannan a tace. Wasu kuma kan ƙara madara ko wasu sinadarai kafin a sha.
Mutane da dama na son abin shan saboda ɗanɗanonsa, amma kuma saboda ƙimarsa ta fuskar gina jiki. 'Ya'yan kuka na ɗauke da sinadarai masu yaƙi da abubuwan da ke lalata ƙwayoyin halitta da kuma harza a yalwace.
Haka kuma suna da sinadarin potassium da bitamin C masu yawa, waɗanda ke taimakawa wajen sa mutum jin ƙoshi na tsawon lokaci, tare da taimakawa wajen kula da nauyin jiki.
A gefe guda kuma, ana amfani da ganyen kuka a girki a ƙasashe da dama na Afirka ta Yamma, musamman a Benin, Togo da Ghana. Ana sarrafa su wajen yin miyar kuka, wadda take da ɗan ɗanko kuma take da matuƙar karɓuwa a tsakanin al'umma.
An kuma san ganyen kuka da yalwar sinadarai kamar calcium, potassium, ƙarfe da protein, da kuma bitamin B da C, tare da provitamin A. Waɗannan sinadarai na taimakawa wajen yaƙi da ƙarancin jini da ƙarfafa garkuwar jiki, da kuma taimakawa wajen kare jiki daga kamuwa da cututtuka.
4 - Dawa

Asalin hoton, Getty Images
Dawa na daga cikin muhimman hatsi da aka daɗe ana nomawa a Afirka, musamman a yankunan Sahel da sauran wuraren da ake fama da ƙarancin ruwan sama. Ta shahara saboda juriyarta ga fari da kuma ƙimarta ta fuskar gina jiki.
Dawa na da wadatacciyar harza, protein, da kuma muhimman abubuwa kamar ƙarfe , magnesium, phosphorus da potassium. Haka kuma tana ɗauke da sinadarai masu yaƙi da abubuwan da ke lalata ƙwayoyin halitta waɗanda ke taimakawa wajen kare ƙwayoyin jiki daga lalacewa.
Saboda yawan fiber da take ɗauke da shi, dawa na taimakawa wajen inganta narkewar abinci da lafiyar hanji. Haka kuma tana taimakawa wajen daidaita adadin sukari a jini, wanda ya sa ake kallonta a matsayin abinci mai amfani ga masu son rage haɗarin kamuwa da ciwon sukari.
Masana lafiya kuma sun nuna cewa cin dawa na iya taimakawa wajen inganta lafiyar zuciya, rage yawan kitsen jijiyoyi da kuma samar da kuzari mai ɗorewa saboda yadda take sakin kuzari a hankali a jiki.
Bugu da ƙari, dawa ba ta ɗauke da sinadarin gluten, abin da ya sa ta dace da mutanen da ke da matsalar rashin jituwa da wannan sinadari. A sassa da dama na Afirka, ana amfani da ita wajen yin tuwo, kunu, burodi da sauran nau'ikan abinci na gargajiya da na zamani.
5 - Hatsin Teff

Asalin hoton, Getty Images
Teff wani tsohon hatsi ne da aka fi nomawa a Habasha. Ya shahara saboda irin dimbin sinadarai masu gina jiki da yake ɗauke da su.
Da farko, teff na da yawan sinadarin calcium idan aka kwatanta da sauran nau'ikan hatsi. Bugu da ƙari, ba ya ɗauke da sinadarin gluten, kuma yana da yalwar ƙarfe da harza, protein, ma'adanai masu muhimmanci ga jiki da kuma magnesium.
Saboda waɗannan sinadarai, teff na taimakawa wajen:
- Gina da ƙarfafa ƙasusuwa da haƙora.
- Yaƙi da matsalar ƙarancin jini.
- Inganta narkewar abinci da lafiyar hanji.
- Samar da kuzari mai ɗorewa ga jiki.
- Ƙarfafa tsokoki da lafiya gaba ɗaya.
Saboda kyawawan siffofinsa na gina jiki, teff na daga cikin abincin da masana harkar lafiya ke yaba wa, kuma 'yan wasa da dama suna amfani da shi a matsayin wani ɓangare na tsarin abincinsu.











