Alƙawurra 3 da ƴan takarar gwamnan ADC suka yi wa ƴan arewacin Najeriya

Yan takawarar gwamna na jam'iyyar ADC

Asalin hoton, Facebook/Multiple

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Laraba ne ƴan takarar gwamnoni na ADC daga jihohin Arewa maso yammacin Najeriya suka bayyana manufofinsu, yayin da aka fara buɗe kafar fara yaƙin neman zaben gwamnoni na 2027.

Ƴan takarar sun ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ne a wajen wani taro a Abuja babban birnin Najeriya, wanda ya tattara ƴan takarar gwamna da mataimakansu na jam'iyyar adawa ta ADC, masu takara a jihohi bakwai na Arewa maso yamma da suka haɗa da Kaduna da Kano da Jigawa da Katsina da Zamfara da Sokoto da kuma Kebbi.

Sun ce sun haɗa kai ne domin tsara dabarun bai ɗaya da za su yi amfani da su a matsayin jaddawalin kawo canji mai ma'ana a jihohin bakwai, idan suka yi nasara a zaɓe mai zuwa.

Tsohon ministan shari'a na Najeriya kuma ɗan takarar gwamna a jihar Kebbi, Abubakar Malami, wanda ya jagoranci taron ya shaidawa BBC tsare-tsaren nasu da kuma yadda za su aiwatar da su, domin kyautata rayuwar al'ummar yankin.

Ya zayyano tsare-tsaren nasu kamar haka:

Dawo da tallafin mai

Ƴan takarar gwamnan na jam'iyyar ADC da mataimakan su sun sha alwashin goyon bayan ɗan takarar su na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar domin ganin ya cika alƙawarin da ya yi na dawo da tallafin mai a Najeriya.

Dangane da wannan batu, Abubakar Malami ya ce ''idan an ɗauki mataki wanda ya zama ya cutar da walwalar al'umma, wajibi ne a juya shi.''

Ya ƙara da cewa ''cire tallafin mai da aka yi me ya amfanawa ƴan Najeriya in bayan matsi da talauci? shiyasa dole duk wani tsari da za mu bi ta hanyar doka sai mun kawar da duk wani abu da ya jefa jama'a a cikin rashin walwala da talauci.''

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƴan takarar gwamnan na jam'iyyar ADC sun ce fatan su shi ne ganin sun samar da tallafi mai domin amfanin talaka, ta yadda za a koma sayar da man a tsakanin naira 300 zuwa 500.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne ya janye tallafin da gwamnatin ƙasar ke bayar wa a ɓangaren man fetir, tun a jawabin sa na farko bayan shan rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga watan Mayun 2023, lamarin da ya janyo tashin farashin man da kuma tsadar rayuwa tsakanin al'umma.

Amma ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar ya yi alƙawarin cewa zai mayar da tallafin man fetur a ƙasar idan ya samu nasara a zaɓen.

A tattaunawa da ya yi da kafafen yaɗa labarai a ranar Laraba, 19 ga watan Ogusta, Atiku Abubakar ya ce cire tallafin bai yi amfani ba kasancewar "ba a ga abin da aka yi da kuɗin ba".

"Ina kuɗin suke? Ya kamata a ce an yi amfani da su wajen maganin talauci da rashin zuwa makaranta, da sauran su".

A lokacin da aka tambaye shi ko zai mayar da tallafin man fetur ɗin idan ya ci zaɓe a 2027, sai ya ce: "Zan mayar, kuma duk wani wanda ya saci kudin zai dawo da su".

Da matakin da ƴan takarar gwamna na jam'iyyar ADC daga Arewa maso yamma suka sanar, alamu na nuna cewa batun dawo da tallafin zai zamo ɗaya daga cikin manyan manufofin da ADC za ta yi yaƙin neman zaɓe da su.

Ƙarin albashin ma'aikata - N110,000

Yan takarar gwamnan a jihohin Arewa maso yammacin Najeriyan sun kuma yi alƙawarin tsayar da tsarin albashin ma'aikatan gwamnati a jihohin ya zamo mafi ƙanƙanta naira 110,000, kamar yadda Abubakar Malami ya tabbatar wa BBC.

''Mun daidaitu cewa albashin da za mu biya ma'aikata ba zai kasa naira 110,000 a dukkan jihohinmu.

Za mu sha banban da yadda aka saba, shiyasa za mu ɗauki matai da ya saɓawa al'ada domin ganin hakan ta tabbata da yardar Allah.''

A bisa tsarin ake kai yanzu, mafi ƙanƙantar albashi a Najeriya shi ne wanda ke ɗaukar naira 70,000 bayan ƙarin da aka yi a 2024, inda kafin nan ma'aikatan gwamnatin tarayya ke ɗaukar 30,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi.

A ɗan tsakanin nan dai an ga yadda ƙungiyoyin ƙwadago ke sake tayar da batun gyaran tsarin albashin domin tafiya daidai da yadda rayuwa ta ke a yanzu.

Tsaro

Yan takarar sun kuma ce za su samar da wani tsarin tsaro na yanki wanda zai fitar da aikin haɗin gwiwa a tsakainin su domin magance matsalar tsaro da ta addabi yankin su.

Abubakar Malami ya ce tsarin mulkin Najeriya ya zayyana muhimman abubuwan da gwamnati ke samarwa jama'arta kuma a cikin su, akwai mafi girma guda biyu ''walwalar al'ummma da kuma ba su kariya ta fuskar tsaro.'' Saboda haka ya ce za su yi aiki tare domin ɓullo da dabaru na zamani da amfani da fasaha wajen tarra bayana sirri da kuma samar da tsaro a jihohin su idan suka yi nasara a zaɓen mai zuwa.

Sun yi alƙawarin kafa tsarin kai ɗauki da kariya ga al'ummomi a faɗin shiyyar ƴan majalisar dattawa 21 na Arewa maso Yamma domin kawar da ƙalubalen tsaron yankin.

Yanzu haka dai yankin Arewa maso yammacin Najeriya na fama da matsananciyar matsalar tsaro da ta haɗa da ta ƴan fashin daji masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da ta ƴanbindiga masu kai hari da kashe mutane a sassan yankin. Wannan matsala ta shafe shekaru tana damun yankin, duk da ƙoƙari da gwamnatoci ke cewa suna yi domin magance ta.