Mene ne hijabi, kuma mene ne asalinsa a Musulunci?

Asalin hoton, Getty Images
A watan Yulin da ya gabata ne kotun ɗaukaka ƙara da ke Ibadan a kudancin Najeriya, ta soke hukuncin da wata kotun jihar Oyo, da ke kudu maso yammacin ƙasar, da ta bai wa ɗalibai mata musulmi na makarantar International School (ISI) damar sanya hijabi tare da kayan makaranta.
A ranar 22 ga Mayun 2024 ne kotun jihar Oyo ta yanke hukuncin farkon bayan ɗalibai mata Musulmai 11 sun shigar da ƙara, inda suka zargi makarantar da tauye musu ƴancin su na hana su sanya hijabi a matsayin kayan makaranta.
Mai shari'a Biobele Georgewill, tare da goyon bayan mai shari'a K.I. Amadi, sun ce makarantar ISI ta Ibadan makaranta ce mai zaman kanta, ba ta cikin jerin makarantun gwamnati da hukuncin kotun koli kan sanya hijabi ya shafa.
Bayan wannan an samu wani lokaci da aka nuna wata ɗaliba tana sanye da hijabi ta je rubuta jarabawar JAMB, inda rahotanni suna nuna cewa an hana ta shiga, lamarin da ya tayar da ƙura.
An dai sha ganin yadda batun saka hijabi ke tayar da ƙura, lamarin da ya sa wasu ke tambayar matsayinsa da asalinsa, musamman ganin akwai na'uka daban-daban na hijabin.
Wannan ya sa BBC ta zanta da malamai domin sanin haƙiƙanin mene ne hijabin, da asalinsa da ma siffarsa.
Hijabi a mahangar Sunni
BBC ta zanta da Sheikh Abubakar Abdussalam Muhammad wanda aka fi sani da Baban Gwale, wanda ya ce Hijabi kalma ce ta Larabci wadda ke nufin sanya shamaki ko katanga tsakanin mutum da wani abu, kamar yadda Allah ya bayyana a cikin Alƙur'ani.
Sheikh Baban Gwale ya ce a mahangar Shari'a hijabi shi ne matakan da mace take ɗauka domin namijin da bai halatta ya ganta ba, kada ya gan ta ko ya kalli jikinta.
Malamin ya ƙara da cewa hijabin yana da fannoni daban-daban.
"Na farko, mace ta nisanci wuraren da mazan da ba muharramanta ba suke yawan kasancewa.
"Na biyu kuma idan wata larura ta sa dole sai ta fita, sai ta sanya tufafin da suka dace da Shari'a, ta yadda ba za a fito da surar jikinta ko abubuwan da za su jawo hankalin maza ba," in ji shi.
Asalin hijabi
Sheikh Baban Gwale ya hijabi na da asali mai tsawo, inda ya bayyana cewa tun a zamanin Sayyida Maryam (AS) mahaifiyar Annabi Isa, idan tana son yin wani abu na biyan buƙatarta, tana nisantar idon mutane. W
Shehin malamai ya ƙara da cewa da zuwan Annabi Muhammad (SAW), sai ya gindaya wasu ƙa'idoji da suka tsara yadda mace za ta kasance a cikin al'umma.
Daga cikin waɗannan ƙa'idoji akwai umarnin Allah ga matan Annabi (SAW) da su zauna a gidajensu, kuma kada su rika fita suna nuna kawunansu kamar yadda ake yi a zamanin Jahiliyya.
Malamin ya ƙara da cewa Allah ya umarci Annabi (SAW) da ya faɗa wa matansa da ƴaƴansa mata da matan muminai su sanya 'jilbab' ɗinsu a kansu.
Shehin malamai ya ce sanya hijabi wajibi ne ga mace musulma baliga.
Sharuɗɗan hijabi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sheikh Baban Gwale ya ce hijabi na Shari'a yana da wasu muhimman sharuɗɗa waɗanda ya lissafa:
Ya rufe jikin mace
Tufafin ya kamata ya rufe jikin mace baki ɗaya, ba tare da barin wani ɓangaren ba.
Sai dai malamai sun yi saɓani kan fuska da tafukan hannu, inda babban malamin addini musuluncin, inda ya ƙara da cewa wasu malamai sun ce ba dole ba ne mace ta rufe fuska da tafukan hannunta, bisa wasu ruwayoyi da aka danganta da Nana A'isha (RA) game da Asma'u 'yar Abu Bakr (RA), amma ya ce wasu sun ce dole ne.
Tufafin ya kasance mai faɗi
Kada tufafin ya manne da jikin mace ko ya nuna surar jikinta. Ya kamata ya kasance mai faɗi da yalwa domin kada a iya gane yanayin jikinta.
Tufafin ya kasance mai kauri
Kada tufafin ya kasance sirara ko shara-shara har za a iya ganin launin fatar mace ko tufafin da take sawa a ƙarƙashinsa.
Sheikh Baban Gwale ya ce, "Waɗannan abubuwa uku sune manyan ginshiƙan hijabi," in ji shi.
Kada tufafin ya kasance mai ɗaukar hankali
Bai kamata tufafin ya kasance da irin kayan ado mai ɗauke da zane-zane ko launuka masu tsananin jan hankali da za su sa mutane su kalli mace ba.
Kada ya kasance irin tufafin maza ko tufafin da suka keɓanta da waɗanda ba musulmi ba
Bai kamata mace ta sanya tufafin da suka kebanta da maza ba. Annabi (SAW) ya yi gargadi mai tsanani game da maza masu kwaikwayon mata da mata masu kwaikwayon maza.
Kada ta sanya turare idan za ta fita
Daga cikin abubuwan da Shari'a ta hana mace yayin fita waje shi ne sanya turare mai ƙamshi da maza za su iya ji. Annabi (SAW) ya yi gargadi kan mace da ta sanya turare sannan ta wuce cikin jama'ar maza domin su ji ƙamshinsa.
Mahangar Shi'a
A nasa jawabin, Dokta Shu'aibu Muhammad Abdullahi, shugaban cibiyar nazarin kimiyyar addinin Musulunci ta Khatamul Anbiya Institute of Islamic Sciences da ke Kano shi ma ya ce kalmar hijabi ta samo asali ne daga Larabci, kuma tana nufin shamaki ko rufe wani abu ta yadda ba za a iya ganinsa ba.
A shari'a, "musamman dangane da mace, akwai hijabi na zahiri da na baɗini. Hijabi na zahiri shi ne mace ta sanya abin da zai suturta jikinta daga waɗanda ba muharramanta ba, yayin da hijabi na baɗini ya shafi kamala da tsare mutuncin mace."
Malamin ya ce a wasu lokuta ana iya samun mace mai hijabi na zahiri, amma ba ta cika wasu abubuwan da suka shafi hijabin baɗini ba.
A game da hukuncin hijabi ga mace, Sheikh Shuaibu ya ce wajibi ne, "kuma barinsa saɓon Allah ne"
Abin da hijabi ya kamata ya rufe
A game da inda ya kamata hijabin ya rufe, Sheikh Shu'aib ya ce mafi yawan malamai suna yi ammanar cewa dukkan jikin mace al'aura ne ban da fuska da tafukan hannu biyu.
Sai dai ya ce ba wai fuska da tafukan hannu kaɗai ake magana a kai ba, inda ya ce akwai batun ado.
"Bai kamata mace ta bayyana adonta a gaban waɗanda ba muharramanta ba, ko da kuwa adon yana fuska ko hannu ne," in ji shi.
Ya yi misali a cewa idan mace ta sanya hijabi ta rufe jikinta gaba ɗaya ban da fuska da tafukan hannu, "to bai kamata ta bayyana adon da ke hannunta ba, kamar zanen lalle."
A game da siffofin hijabi, shehin malamin ya zayyano siffofi kamar waɗanda suke sama.
Sai dai malamin ya ƙara da cewa shari'a ba ta ƙayyade wani takamaiman launi ko irin yadin da dole mace ta yi amfani da shi wajen hijabi ba.
Ya ce, "Muhimmin abu shi ne ya cika sharuɗɗan sutura da shari'a ta tanada, kuma ya rufe wuraren da ya kamata a rufe."
Ya ce idan mace na iya amfani da launi daban-daban, "matuƙar launin ko irin kayan bai zama abin da zai jawo hankali ko ya sa tufafin su koma kayan ado ba. Wasu al'ummomi na iya fifita baƙi, wasu fari, wasu kuma wasu launuka, gwargwadon al'adunsu.
Ya ƙara da cewa batun launi da yanayin tufafi yana da muhimmanci, domin abin da ake ɗauka a matsayin ado yana iya bambanta daga al'umma zuwa al'umma.
"Idan a wani yanki doguwar riga tana jan hankali, a wajen wata al'ummar ba ta jan hankali, a wurin da take jan hankali ba ta zama hijabi ba."
A mahangar Tijjaniya
Sheikh Halliru Maraya, malamin addini daga ɓangaren ɗariƙar Tijjaniyya, ya ce sanya hijabi wajibi ne ga mata, bisa umarnin Alƙur'ani da ya zo ga matan muminai kan su rufe jikinsu.
Ya ce wannan aya ce ta Alƙur'ani da ta sanya hijabi ya zama wajibi ga mata.
Ya bayyana cewa matsayin al'aura ya bambanta tsakanin mace yantacciya da bayi. A cewarsa, al'aurar bayi tana tsakanin cibiya da gwiwa, kamar yadda yake ga namiji.
Amma mace yantacciya, in ji shi, dukkan jikinta al'aura ne ban da fuska da tafukan hannu.
Ya ce hijabi kuwa shi ne duk wata sutura da mace za ta sanya domin rufe wuraren da Shari'a ta wajabta ta rufe.
Sheikh Halliru ya ce Ɗariƙar Tijjaniyya hanya ce ta neman kusanci da Allah ta hanyar gudanar da zikiri da wasu ibadu na musamman.
Ya ce ɗariƙar tana da manyan ka'idoji guda bakwai, kuma na farko shi ne riƙo da Littafin Allah a magana da aiki.
A cewarsa, wannan na nufin ɗan ɗariƙar ya kasance yana aiki da koyarwar Alƙur'ani a cikin maganganunsa da ayyukansa.
Saboda haka, ya ce mata mabiya Ɗariƙar Tijjaniyya ya kamata su sanya tufafi masu kauri waɗanda ba sa bayyana jiki, tare da rufe kawunansu, bayansu da ƙirjinsu.
Ya ce wannan yana daga cikin yadda mace za ta cika abin da ake nufi da hijabi a Shari'a.










