Yadda ƴanbindiga suka sace shugaban ƙaramar hukuma a Zamfara

Dauda Lawal

Asalin hoton, Dauda Lawal/FB

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Ƴanbindiga sun ƙaddamar da wani hari a garin Bunguɗu a jihar Zamfara, inda suka yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar, Nura Umar Bungudu da kuma wasu daga cikin na kusa da shi.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya auku ne da daren ranar Juma’a, inda suka kutsa garin tare da tafiya kai-tsaye zuwa gidan shugaban ƙaramar hukumar da ke unguwar Zango.

Jihar Zamfara na cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da matsalar tsaro ta ɗaɗe tana ci wa mutanenta tuwo a ƙwarya, lamarin da ya yi ajalin mutane da dama, sannan ya jefa da dama cikin ƙuncin rayuwa.

Rahotanni daga jihar sun nuna cewa bayan shugaban, maharan sun yi garkuwa da wani ma'aikacin asibitin tarayya da ke Gusau da wani mai sana'ar cire ta kuɗi ta POS a yankin.

Haka kuma rahotannin sun ƙara da cewa harin ya yi sanadiyar mutuwar jami'an tsaro, ciki har da ƴansanda da ƴan sa-kai.

Haka kuma harin ya jikkata wasu mutane da dama, waɗanda a yanzu haka suke kwance suna jinya a asibiti.

Gwamnatin jihar ba ce komai ba game da harin a hukumance, kuma duk yunƙurin BBC na magana da su bai kai ga gaci ba.

Haka kuma kakakin rundunar ƴansandan jihar, Yazid Abubakar bai ɗauki waya ba.

Amma wani hadimin Gwamna jihar Zamfara a ɓangaren sadarwa mai suna Mugira Yusuf ya wallafa a shafinsa na Facebook yana addu'ar Allah ya kuɓutar da shugaban ƙaramar hukumar da sauran mutanen.

Ya rubuta, "Allah ubangiji ka yi wa Shugaban Ƙaramar Hukumar Mulkin Bungudu, Hon. Nura Umar Abdullahi (NU), da sauran ɗaruruwan bayin Allah da ke hannun azzaluman ƴanbindiga mafita. Allah ka tsare su, ka kuɓutar da su cikin aminci da ƙoshin lafiya," kamar yadda ya rubuta.

Yadda abin ya faru

Bunguɗu

Asalin hoton, Jameel Umar Bungudu/FB

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A wani faifan bidiyo da tashar Maifata TV ta fitar, wani mazaunin gidan shugaban ƙaramar hukumar ya ce sun kashe ƴansanda biyu a gidan.

A bidiyon wani mai suna Abdussalam, wanda ya ce shugaban ƙaramar hukumar mijin yayarsa ne, wanda yake gidan a lokacin da abin ya faru ya ce da daddare suka shiga gidan.

"Suna shigowa suka kashe jami'an tsaron da ke gidan. Sai suka shigo suka tashe mu suka tambaye mu ‘ina maigidan?’ Muka ce ba ya nan. Sai suka fara buga min bindiga. Sai suka ce mana an faɗa musu mu huɗu ne muka dawo gidan. Kuma haka ne. Ka ga ke nan faɗa musu aka yi," in ji shi.

Ya ce bayan maharan sun ɗaure su ne sai suka kai su bayan gida, inda daga baya suna can ne suka ga an fito da matar mai gidan, sannan shi ma aka fito da shi.

"Shi ne sai suka tattara mu, suka shiga da mu daji. Ana cikin tafiya ne sai mai gidan ya ce mu ƴaƴansa ne, su sake mu, shi su tafi da shi.”

Ya ce shi dai yana da masaniyar an kashe mutum huɗu, sannan an kwashi wasu mutane bayan su.

Muna ƙoƙarin ceto shi - Sojoji

Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta ce jami'anta na bibiya tare da yunƙurin ceto shugaban ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara, Nura Umar Abdullahi, bayan wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da shi daga gidansa, sannan ta ƙara da cewa an ceto wasu daga cikin iyalansa.

A cewar rundunar, maharan sun yi nasarar yin awon gaba da shugaban karamar hukumar bayan sun yi galaba a kan jami'an ƴansanda da masu sintiri da ke ba shi kariya.

Sanarwar ta ce bayan sojoji sun ji harbe-harbe ne suka garzaya wurin tare da bin sawun maharan, inda suka yi musayar wuta.

Rundunar ta ce matsin lambar da dakarunta suka yi ya sa maharan ne ya sa suka bar mutum biyar daga cikin iyalan shugaban ƙaramar hukumar, waɗanda suka haɗa da 'ya'yansa biyu da mahaifiyarsa da matarsa da wani ɗan'uwansa, kafin su tsere da shi cikin daji.

Rundunar ta tabbatar da mutuwar jami'an tsaronsa uku, ciki har da ƴansanda biyu da dan sintiri guda daya. Haka kuma wani ɗan babu ruwan ya rasu, sannan wani Alhaji Bello Umar, ya ji raunuka.

Rundunar ta ce ta ƙaddamar da aikin haɗin gwiwa tare da ƴansanda da DSS da ƴan sa-kai domin gano inda maharan suke tare da kuɓutar da shugaban ƙaramar hukumar cikin ƙoshin lafiya.

Matsalar tsaro a Zamfara

A watan Fabrairun 2017 ne Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da shiga yarjejeniyar zaman lafiya da Buharin Daji, wanda a lokacin shi ne jagoran ƴanbindiga a jihar da ma maƙwabta.

Yarjejeniyar ta zo bayan lokaci da aka ɗauka ana kashe mutane tare da sace wasu domin kuɗin fansa.

Sai a watan Maris na 2018 Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da kashe Buharin Daji, lamarin da ya sa aka riƙa farin ciki da murnar tunanin cewa an kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar.

Asali rikici ne da za a iya alaƙanta da ƴan sa-kai da ɓarayin shanu kafin ya rikiɗe zuwa satar mutane da kashe su, a lokaci da dama kuma ramakon gayya ke ƙara ta'azzara matsalar.

Ko a zamani mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bai wa ƴan bindigar da ke jihar Zamfara wa'adin wata biyu su miƙa wuya, sannan aka sanar da tura ƙarin sojoji jihar.

Sai dai duk da irin waɗannan matakai da aka ɗauka a baya, har yanzu matsalar tsaro ra zama babban kalubalen da ke addabar jihar ta Zamfara da ma yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Duk da cewa gwamnati ta sha nanata cewa tana daukar matakan magance lamarin, amma abin ya ci tura.

A watan Maris na wannan shekarar ta 2026 ne Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana sauya sheƙarsa daga PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC, inda a lokacin, kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa ficewar gwamnan zuwa APC ta zama dole saboda muradun al'ummar Zamfara.

Daga cikin hujjojin da aka ambata a cikin muradun ƴan jihar akwai ƙoƙarin haɗa ƙarfi da ƙarfe da gwamnatin tarayya wajen magance matsalar ta tsaro.

Me ya kamata a yi?

A cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC, Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacom Security and Intelligence kuma masani kan lamuran tsaro a yankin Sahel, ya zayyana wasu matakai da ya ce yake tunanin idan an bi za a iya samun zaman lafiya, kamar haka:

  • Gwamnatin Tarayya ta ƙara haɗa kai da jihohi domin fitar da tsari na magance wasu matsaloli, kamar talauci da sauyin yanayi da sauransu
  • Daƙile ɗaukar makamai a hannun waɗanda bai kamata ba
  • Tsaro na iyaka domin kula da shiga da fitar mutane da kayayyaki
  • Hukunta mai laifi saboda zargin da Fulani ke yi cewa shari'a na zalintar su

"Idan ba a yi haka ba, kashe shugabannin ba zai yi wani tasiri ba," in ji shi.