Wane ne Sheikh Musa Lukuwa kuma me ya sa yake taƙaddama da malaman Sokoto?

..

Asalin hoton, Sheikh Lukuwa/Facebook

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Wasu ƙungiyoyin Malaman addinin Musulunci da suka haɗa da na ƙungiyar sufaye ta Tijjaniya a Najeriya da zuri'ar Sheikh Usmanu Danfodiyo da sauran su, sun gabatar da koke ga gwamnatin Jihar Sakkwato da kuma Fadar Mai alfarmaSarkin Musulmi kan wasu kalamai da ake dangantawa da Sheikh Ayyuba Musa Lukuwa da ake zargi suna taɓa martaba da matsayin Annabi Muhammad (SAW).

Tawagar ta miƙa koken ga hukumomin da abin ya shafa, tana kira da a ɗauki matakin gaggawa.

Malam sun ce kalaman na iya tayar da fitina da kuma barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'ummar Muslumi.

Da me ake zargin Sheikh Lukuwa?

Shugaban Majalisar Sufaye a Najeriya, wadda ke wakiltar mabiya ɗarikun Tijjaniyya da Qadiriyya, Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal ya bayyana cewa kalaman da ake zargin an yi sun kasance abin ƙyama kuma ba za a amince da su ba.

"Yana cewa mahaifan annabi Muhammad suna cikin azaba kuma yana ta nanatawa kamar da gangan ake yi domin a tashi hankalin Musulmi," in ji Farfesa Yagawal.

Farfesa Abubakar ya kuma ƙara da cewa zarge-zargen sun hada da cin mutumcin Shehu Usmanu Danfodio da ma Fadar Sarkin Musulmi.

"Yana kuma zagin mutane masu mutumci. Yana zagin Sarkin Musulmi. Da kuma kiran a rushe hubbaren Shehu a mayar da shi filin ƙwallo. Da kwatanta kabarin Shehu da na Ojukwu duk ɗaya .

"Wannan cin zarafi da yake yi wa annabi Muhammad SAW wanda duk Musulmi mai imani ba zai ji daɗin hakan ba kuma ba zai kasa yin wani abu ba idan har yana iya yi. Ya daɗe yana cin zarafin annabi,"

Martanin Sheikh Lukuwa

To sai dai Sheikh Ayuba Musa Lukuwa ya ce an yi wa kalamansa bahaguwar fahimta, domin kuwa duk abubuwan da ya faɗa ya tsamo su ne daga hadisai da tarin hujjoji.

Ya kuma nemi a zauna tsakaninsa da malaman domin yin muƙabala kan batutuwan da suke zargin sa da su.

"Yau kwana shida da muka rubuta musu...ta neman muƙabala domin mu zauna da su mu yi karatu a kan waɗannan matsaloli...a dauki litattafan addini a yi karatu mu kuma nuna inda muka waɗannan abubuwan...shin ga manzon Allah na samo su ko kuma ni ne na ƙirƙiro su.

Mun kai wasiƙar ma'aikatar lamuran addinin sannan mun kai ta fadar Sarkin Musulmi kuma mun kai wa kwamishinan ƴansanda," in ji Sheikh Lukuwa.

Wane ne Sheikh Musa Lukuwa?

..

Asalin hoton, Sheikh Lukuwa/Facebook

Malam Musa Ayuba Lukuwa malamin addinin Musulunci ne a jihar Sokoto da ke bin fahimtar Ahlussunnah Wal Jama'a.

Yana daga cikin malamai masu yawan janyo taƙaddama musamman dangane da al'amura masu sarƙaƙiya.

Ya shahara wajen ra'ayoyi masu cin gashin kansu kan fikihun Musulunci da wasu ayyukan ibada.

Misali, game da tabbatar da ganin jinjirin wata na bukukuwan Musulunci irin su Idi, ya kasance yana jaddada muhimmancin dogaro da ganin watan a cikin gida ko yankin da ke kusa, kamar a Jamhuriyar Nijar maƙwabciya, maimakon jingina gaba ɗaya ga sanarwar da ta fito daga wurare masu nisa kamar Saudiyya.

A baya-bayan nan hotuna da bidiyo na kafar sada zumunta sun nuna malamin mai tarun shekaru ɗauke da bindiga biyo bayan barazanar da ya fuskanta bisa zargin taɓa ƙimar annabi Muhammad SAW.