Belgium na tambayar Fifa kan dalilin da aka bar Balogun ya yi wasa duk da jan kati, Folarin Balogun

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Kwallon Ƙafa ta Belgium ta ce har yanzu tana son samun amsoshi kan dalilin da ya sa aka bar Folarin Balogun ya fuskance su a gasar cin kofin duniya, kuma ta nemi a saka batun cikin ajandar taron Majalisar FIFA na gaba.
A cikin ɗaya daga cikin batutuwan da suka fi jawo ce-ce-ku-ce a gasar cin kofin duniya da aka yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico, an bai wa Balogun damar buga wa Amurka wasan zagayen ‘yan 16 da Belgium, bayan da FIFA ta dage hukuncin dakatar da shi wasa ɗaya na tsawon shekara guda, bayan jan kati kai tsaye da ya samu a wasansa na baya.
Wannan mataki ya kasance ba kasafai ake ganin irin sa ba, kuma ya fuskanci suka daga wurare da dama, musamman bayan da aka bayyana cewa shugaban Amurka Donald Trump da wasu jami’an Fadar White House sun matsa wa FIFA lamba kan batun.

