Ta yaya tarwatsewar ƴan adawa zai shafi zaɓen 2027?

Asalin hoton, Peter Obi/Facebook
A daidai lokacin da ake babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027 ke ƙara ƙaratowa, masu bibiyar al'amuran siyasa na ganin salon na siyasar na ɗaukar salo daban-daban, musamman a ɓangaren ƴan hamayya.
Tuni tsoffin ƴantakarar shugaban Najeriya biyu a zaɓen 2023 wato Rabiu Musa Kwankwaso da ya tsaya takara a NNPP a zaɓen 2023 da takwaransa na LP, Peter Obi suka dunƙule a sabuwar jam'iyyar NDC domin fafatawa da Bola Tinubu.
Ƴantakarar biyu na cikin manyan jiga-jigan da a baya suka haɗu a jam'iyyar ADC da ake wa laƙabi da ta haɗaka, sabuwar haɗuwar manyan ƴan hamayya a cikinta domin fuskantar zaɓen 2027 a matsayin tsintsiya maɗaurinki ɗaya.
A baya dai jam'iyyun hamayyar ƙasar sun gudanar da wani taron a birnin Badun na jihar Oyo domin samar da matsaya kan yadda za su fuskanci zaɓen, taron da ya samu halartar jiga-jigan PDP da ADC da Labour da NNPP.
A taron ne suka bayyana cewa zai yi wahalar gaske a iya kayar da shugaba Tinubu idan ba sun haɗa ƙarfi da ƙarfe ba domin yi masa taron dangi su fuskance shi, sannan a ƙarshe suka amince su yi aiki.
Tarwatsewar hamayya?
A taron na Ibadan, an kusan duk wani jigon hamayya a ƙasar, kamar tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Anambra Peter Obi da tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon gwamnan Rivers Rotimi Amaechi da Aminu Waziri Tambuwal.
Sai kuma mai masaukin baƙi, Gwamna Seyi Makinde da shugaban wani tsagi na PDP, Tanimu Kabiru Turaki da wasu jiga-jigan jam'iyyu daban-daban da sauran masu ruwa da tsaki.
Wannan ya sa aka yi tunanin ƴan hamayya sun samu maslaha a tsakaninsu, kuma aka ruwaito cewa sun amince su fitar da ɗan takara ɗaya.
Jim kaɗan ne wasu ƴan majalisar wakilai da sanatoci suka koma jam'iyyar ADC, inda jam'iyyar ta ƙara tagomashi.
Daga cikin tikitin da aka riƙa ruwaito a jam'iyyar ADC akwai:
- Atiku da Obi
- Obi da Kwankwaso
- Atiku da Amaechi
- Atiku da Makinde
Sai dai yanzu za a iya cewa haɗakar ta samu tangarɗa domin bayan ficewar Obi da Kwankwaso, tuni ƴan majalisar wakilai 17 sun fice daga cikinta, inda 16 suka koma jam'iyyar NDC, ɗaya kuma ya koma APC.
Obi da Kwankwaso sun bayyana cewa rikice-rikice da shari'o'in da ADCn ke fama da su da rashin tabbas ne suka tilasta musu ficewa daga jam'iyyar domin samun tabbacin shiga zaɓen na 2027.
Me hakan ke nufi?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An daɗe ana bayyana cewa ƴan hamayya a ƙasar na buƙatar haɗin kai domin fuskantar zaɓen 2027 idan har suna so su nuna ƙwanji.
Duk da cewa sauye-saueyen jam'iyya ba sabon abu ba ne a siyasar Najeriya, ana kallon faruwar hakan a yanzu a matsayin mafi tasiri saboda yadda kusan manyan jam'iyyun adawar suka aminta suna buƙatar dunƙulewar.
A wata tattaunawa da BBC ta yi da Farfesa Abubakar Kari masanin kimiyyar siyasa ne a Jami'ar Abuja, ya ce nan gaba idan ba a yi taka tsan-tsan ba Najeriya za ta iya komawa ƙasa mai jam'iyya ɗaya.
Farfesa Kari ya ce ya kamata ya yi jam'iyyun hamayya su riƙa haɗuwa suna gangami domin ƙwace mulki daga jam'iyya mai muki, "amma saboda rashin haɗin kai na ƴan'adawa, sai ya zama akasin haka ne ke faruwa," in ji shi, inda yake nuni watsewa da suke yi.
A game da abin da ya kamata a yi, Farfesa Kari ya ce: "Ƴan'adawa su yi gagarumin yunƙuri domin ganin hakan bai ci gaba da faruwa ba, kuma suma su fara zawarcin manyan ƴansiyasa daga APC ganin cewa ita ma jam'iyyar mai mulki tana fuskantar ƙorafe-ƙorafe da rashin gamsuwa da yadda abubuwa ke wakana a cikinta."
Shi ma Farfesa Abubakar Mu'azu na Jami'ar Maiduguri kuma darakta a cibiyar diflomasiyya da cigaban ƙasa ya bayyana a wata tattaunawarsa da BBC, cewa ya yi ita ma APC haɗaka ce aka yi domin kayar da PDP.
"Kamata ya yi jam'iyyun hamayya su tsara gidansu ta yadda za su ja hankalin masu zaɓe. Ai da ba APC ba ce take mulki, daga baya ne wasu suka haɗe suka kayar da PDP.
"Ya kamata su yi la'akari da cewa duk wanda yake kan mulki yana so ya ci gaba, ya rage nasu su san dabarar da za su yi domin ƙwace mulki."
Ƙalubalen da ke gaban ƴan hamayya
A watan Afrilun 2025 ne wasu jiga-jigan ƴansiyasa a Najeriya suka amince da African Democratic Congress (ADC) a matsayin jama'iyyar da za su ƙulla ƙawancen haɗaka a cikinta.
Ƴansiyasar sun ce sun amince da ADC ne da nufin haɗa ƙarfi da ƙarfe a cikinta da nufin kawar da jam'iyyar APC daga mulkin Najeriya a zaɓen 2027.
An cimma ƙawancen ne a taron haɗakar da aka gudanar ranar Laraba 2 ga watan Yulin bara a babban ɗakin taro na Ƴar'adua Centre da ke birnin Abuja.
Sabuwar haɗakar ta ADC ta zaɓi Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan ƙasar David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar, wadda suka amince da ita a matsayin jam'iyyar haɗaka.
Sai dai shari'a ta hana jam'iyyar rawar gaban hantsi, inda rikicin cikin gida tsakanin David Mark da Nafiu ya tsayar da ita, lamarin da aka kai har Kotun Ƙolin ƙasar kafin aka samu wata ƴar mafita.
Sai dai bayan hukuncin kotun ne kuma masana shari'a irin su Audu Bulama Bukarti suka bayyana cewa baya tiya akwai wata cacar, inda ya bayyana wa BBC cewa asalin shari'ar jam'iyyar ta ADC ba a ma fara ba.
Ita ma PDP har yanzu akwai sauran rina a kaba, domin a daidai lokacin da ake tunanin Kotun Ƙoli ta warware rikicin, sai ya kasance har yanzu ɓangarorin na cigaba da takun-saƙa.
A daidai lokacin da kwamitin amintattun jam'iyyar ya ce ya naɗa Tanimu Turaki shugabancin riƙo, tsagin Wike na nanata cewa hukuncin kotun soke tsagin Turaki ya yi, don haka su ne suka samu nasara a kotu.










