Hukunce-hukuncen da kotun ƙoli ta yanke kan PDP da ADC

..

Asalin hoton, BBC pidgin

Lokacin karatu: Minti 3

Kotun ƙoli ta yanke hukunce-hukunce guda biyu dangane da shari'o'in da ɓangarorin jam'iyyun hamayya na PDP da ADC suka shigar.

Ɓangaren Tanimu Turaki na jam'iyyar PDP ya shigar ƙarar ne a kotun inda yake neman kotun ta fayyace dangane da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke wanda ya ruguza babban taron da ɓangaren ya yi a birnin Ibadan na jihar Oyo a watan Nuwamban 2025.

Haka zalika, ɓangaren sanata David Mark na jam'iyyar ADC ya shigar da ƙara ne dangane da cire sunansa daga na'urar hukumar zaɓen Najeriya da Inec ɗin ta yi a watan Maris.

Jam'iyyar hamayyar ta ADC ta fara neman a gaggauta yanke hukunci kan saɓanin da take ciki kan sahihancin shugabancinta, domin fayyace makomar jam'iyyar musamman hamayyar shugabanci tsakanin bangaren Sanata David Mark da kuma bangaren Nafiu Bala Gombe.

Kotun Ƙoli ta tabbatar da shugabancin David Mark na ADC

..

Asalin hoton, Muhammeed M Abdulhameed/FB

Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da shugabancin jam'iyyar ADC ɓangaren Sanata David Mark.

A hukuncin da kotun ta yanke ƙarƙashin mai shari'a Mohammed Lawal Garba, ta ce masu ƙarar su koma babbar kotun tarayya domin ci gaba da shari'ar da ake yi.

Alƙalan sun kuma yi watsi da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na cewa a tsaya inda ake da cire sunan shugabancin ADC ɓangaren David Mark daga shafin INEC.

Tun da farko dai tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa mai kula da yankin arewacin ƙasar, Nafi'u Bala Gombe ne ya shigar da tsagin David Mark ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, yana zargin su da ƙwace shugabancin jam'iyyar.

Lamarin da ya sa tsagin na David Mark - ya garzaya gaban kotun ɗaukaka ƙara, inda ya buƙaci kotun ta hana babbar kotun tarayya sauraron batun rikicin shugabancin nata.

Ɓangaren na David Mark ya ce babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron ƙarar da ta shafi rikicin shugabancin jam'iyya.

Kotu ta kori ƙarar PDP ɓangaren Tanimu Turaki

..

Asalin hoton, PDP/TURAKI

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kotun ƙolin ta yanke hukunci dangane da shari'ar jam'iyyar PDP inda kuma ta kori ƙarar da shugabancin PDP tsagin Tanimu Turaki ya shigar.

Kabiru Turaki dai ya shigar da ƙarar ne yana ƙalubalantar matakin rushe taron zaɓen shugabanninsu da aka yi a Ibadan da kotun ƙolin ƙasar ta yi a baya.

Yayin da yake sanar da matsayar alƙalan, mai shari'a Stepehen Adah ya bayyana cewa taron da suka gudanar a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamban 2025 a Ibadan rashin ɗa'a ne ga hukuncin babbar kotun tarayya da mai shari'a James Omotosho ya yanke inda ya dakatar da su daga gudanar da babban taron jam'iyyar.

Kotun ƙolin ta kuma soki ɓangaren Turaki game da zuwa kotun da ba ta da hurumi, a madadin zuwa kotun ɗaukaka ƙara.

Saboda haka, kotun ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar da ta yanke na haramta taron PDPn a jihar Oyo.

Uku daga cikin alƙalai biyar ɗin sun amince da wannan hukuncin, yayin da biyu daga cikinsu suka ce kotun ɗaukaka ƙarar tana da hurumi.

Me hukuncin ke nufi ga jam'iyyar PDP?

Hukuncin kotun ƙolin ya nuna cewa shugabancin Abdulrahman Mohammed da Samuel Anyanwu a matsayin shugaban jam'iyyar PDP da sakatare waɗanda aka za ba a watan Maris 2026 shi ne halastacce.

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike shi ne ke goyon bayan shugabancin na Abdulrahman Mohammed.

A watan na Maris ne dai wakilai daga faɗin Najeriya fiye da 2,000 suka zaɓi Abdulrahman da Anyanwu da ƙarin wasu mambobi 19.

To sai dai a wata shari'ar ta daban kuma kotun ta ƙi amincewa da ƙarar da Samuel Anyanwu ya shigar na a amince da shugabancinsu amma kuma kotun ta yi watsi da buƙatar.

Wannan na nufin a yanzu haka babu wani tsayayyen shugabanci a jam'iyyar PDP.