Yadda hukunce-hukuncen kotun ƙoli suka jefa ƴan'adawar Najeriya cikin garari

Atiku Obi Kwankwaso

Asalin hoton, Multiple/X

Bayanan hoto, '
    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • Lokacin karatu: Minti 6

A cikin watannin da suka gabata, dunƙulewar da ƴan adawar Najeriya suka yi a jam'iyya ɗaya ta sanya ana hasashen cewa siyasar ƙasar ta fara ɗaukan saiti gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsofaffin ƴan takarar shugaban ƙasa Peter Obi da Rabiu Kwankwaso da ma sauran waɗanda ake ganin za su iya yin tasiri a ɓangare adawa sun dunƙule a wuri ɗaya.

Ya kai ga cewa hatta wani ɓangare na jam'iyyar PDP da ke fama da rikicin shugabanci sun amince su yi jingina da jam'iyyar ADC ta haɗaka domin fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya.

Sai dai cikin ƙanƙanin lokaci wannan wannan fata ta kau.

Hukuncin da kotun ƙolin Najeriya ta yanke a makon da ya gabata, ya sa lamura sun dagule.

Jam'iyyun sun yi ta jiran hukuncin kotun ƙoli kan rikice-rikicen shugabanci da dukkansu su ke fama da su, amma sai ga shi lamurran da suka biyo bayan hukunce-hukuncen sun zama tamkar sun ƙara dagula lamurra.

A ɓangaren jam'iyyar APC, kotun ƙoli ta buƙace ɓangarorin biyu su koma babbar kotun tarayya domin sauraron ƙarar da aka shigar ta farko.

Game da jam'iyar PDP kuwa, kotun ƙolin ta rushe shugabancinta ɓangaren Tanimu Turaki da taron da suka gabatar na zaɓen shugabanni a birnin Ibadan a ƙarshen shekarar 2025.

Hukunce-hukuncen da kotun ƙoli ta yanke

PDP ADC

Asalin hoton, BBC PIDGIN

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ɓangaren Tanimu Turaki na jam'iyyar PDP ya shigar ƙarar ne a kotun inda yake neman kotun ta fayyace dangane da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke wanda ya ruguza babban taron da ɓangaren ya yi a birnin Ibadan na jihar Oyo a watan Nuwamban 2025.

Shi ma ɓangaren Abdulrahman Mohammed na PDP ɗin ya shigar da ƙara na a amince da shugabancinsa da Samuel Anyanwu da Nyesom Wike ke goyon bayansu.

Haka zalika, ɓangaren sanata David Mark na jam'iyyar ADC ya shigar da ƙara ne dangane da cire sunansa da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (Inec) ta yi daga shugabanci a watan Maris.

  • Hukunci kan David Mark da ADC

A hukuncin da kotun ƙloin Najeriya ta yanke ƙarƙashin mai shari'a Mohammed Lawal Garba, ta ce masu ƙarar su koma babbar kotun tarayya domin ci gaba da shari'ar da ake yi.

Sai dai kotun ta soke matsayar kotun ɗaukaka ƙara da ya ce a tsaya a matakin da ake, lamarin da ya kai da cewa Inec ta cire suna David Mark daga shugabanci.

  • Hukuncin kotu kan PDP ɓangaren Tanimu Turaki

Kotun ƙolin ta yanke hukunci dangane da shari'ar inda kuma ta kori ƙarar da shugabancin PDP tsagin Tanimu Turaki ya shigar.

Yayin da yake sanar da matsayar alƙalan, mai shari'a Stepehen Adah ya bayyana cewa taron da suka gudanar a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamban 2025 a Ibadan rashin ɗa'a ne ga hukuncin babbar kotun tarayya da mai shari'a James Omotosho ya yanke inda ya dakatar da su daga gudanar da babban taron jam'iyyar.

PDP

Asalin hoton, OfficialPDPng/X

Bayanan hoto, Tanimu Turaki

Kotun ƙolin ta kuma soki ɓangaren Turaki game da zuwa kotun da ba ta da hurumi, a madadin zuwa kotun ɗaukaka ƙara.

Saboda haka, kotun ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar da ta yanke na haramta taron PDPn a jihar Oyo.

Me hukunce-hukunce suka janyo?

Duk da yake jam'iyar ADC na ganin ta samu abin da ta ke so - INEC ta mayar da sunan shugabanninta ɓangaren David Mark - ana ganin wani ɓangare na hukuncin kotun ƙolin da ya buƙaci su koma babbar kotun tarayya domin ci gaba da shari'ar da su ke yi da Nafiu Bala Gombe, kamar wani shigo-shigo ba zurfi ne.

Waɗannan hukunce-hukunce sun ƙara tarwatsa kawunansu, inda ta kai ga har an fara ficewa daga jam'iyyun saboda rashin isasshen lokacin kammala tsare-tsaren da suka dace domin shiga zaɓen 2027.

Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 kuma jigo a jam'iyar ADC, Peter Obi ya fice daga jam'iyar a ranar Lahadin nan, inda ya kafa hujja da rikicin da ba su da tabbacin za a iya warware shi kafin ƙarewar wa'adin kammala duk wasu shirye-shiryen da INEC ta gindaya na shiga zaɓen.

A cikin sanarwar da ya fitar, Peter Obi ya ce "Gwamnatin Najeriya da ƴan korenta waɗanda suka haifar da rikice-rikice a jam'iyyar LP, abin da ya tursasa ni barin ta, a yanzu da alama sun sun shiga jam'iyyar ADC, inda ake fama da ƙararraki a kotu da rikicin cikin gida a maimakon mayar da hankali kan manyan matsalolin ƙasa..."

Haka nan shi ma Rabiu Kwankwaso, a sanarwar da ya fitar a daren ranar Asabar ya ce "Mun bar jam'iyyar NNPP sanadiyyar ƙararraki a kotu waɗanda suka sa zaman mu (a jam'iyyar) ba zai yiwu ba.

"Yanzu ita ma ADC an jefa ta cikin irin wannan hali," a cewar sanarwar.

A ranar Lahadi, manyan ƴan adawar biyu suka tattara kayansu suka koma jam'iyyar NDC.

Gwamnan jihar Bauchi, wanda shi ne shugaban gwamnonin jam'iyar PDP kuma ɗaya daga cikin ƙashin bayanta shi ma ya bar PDP inda ya koma jam'iyyar APM.

Jam'iyyun adawar sun daɗe suna zargin cewa gwamnatin tarayyar ƙasa da jam'iyar APC mai mulki da kitsa rigingimun cikin gida domin ganin ba su fuskanci wani ƙalubale a sake lashe zaɓen 2027 ba.

Jam'iyar APC mai mulki ta sha musanta hannu a rikice-rikicen.

Abin da aka yi hasashe?

Masana siyasa a Najeriya na ganin cewa halin da manyan jam'iyyun adawar suka samu kansu a ciki ba ya rasa nasaba da ƙudurin da dukkanin jiga-jigansu ke da shi na yin takarar shugaban ƙasa, kuma "babu wanda ya ke da niyyar haƙura don mara wa wani baya idan aka yi zaɓen fitar da gwani".

Farfesa Abubakar Umar Kari, wanda malami ne a Jami'ar Abuja kuma masanin harkokin siyasar Najeriya ya ce dama tun farko an hango alamun za su samu rabuwar kai, sai dai ba a yi tunanin da wuri haka lamarin zai faru ba.

"Dama an yi ta hasashen cewa abin da ya ke faruwa ɗin zai iya faruwa. Akwai alamar tambaya dama anya da irin wannan burin nasu za su iya zama lema ɗaya?" in ji Farfesan.

Ya ƙara da cewa jiga-jigan adawar suna kallon hukuncin kotun a matsayin wata barazanar kuma da alama suna neman dalili ne domin kare manufarsu ta fita jam'iyyar domin cimma burinsu na yin takara.

Wace dabara ta rage musu?

Masanin siyasar ya ce idan har ƴan adawar na son kayar da Bola Tinubu dole su tattara ƙarfinsu waje ɗaya, saɓanin haka kuma ba lallai su kai labari ba.

Farfesa Kari na ganin tunkarar zaɓe tare da yin nasara kan jam'iyar APC da ke da gogaggun ƴan siyasa irin su shugaba Bola Ahmed Tinubu ba abu ne da ƴan adawar za su iya yi cikin sauƙi ba tare da sun dunƙule wuri guda ba.

"Dabara tana wajensu, amma dole su rabu dama, tun da kowa ya dage kan ƙudurinshi. Amma in da za su haɗa kansu waje guda, su mara wa juna baya mai yiwuwa irin ƙalubalen da za su ba APC mai mulki zai fi," in ji shi.

Farfesa Kari ya ce idan har ba su yi hakan ba, to sun bayar da wata dama da za ta share wa APC hanya domin lashe zaɓe cikin ruwan sanyi ta hanyar rarraba ƙuri'unsu.

Ya ce: "Kayar da shi sai an yi gayya, a tattara duk wani ƙarfi waje guda. In dai suka raba kansu, kamar sun shimfiɗa musu hanya ce cikin ruwan sanyi [Tinubu] ya samu nasara".