BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Me ya sa garkuwa da mutane ke ƙaruwa a Kano?
Wani masanin tsaro ya ce duka ƙauyukan da ke da iyaka da jihohin Katsina da Kaduna na cikin barazanar hare-haren ƴanbindiga.
Chelsea na bibiyar Wijnaldum, Newcastle da Aston Villa na zawarcin Kofane
Chelsea ta tuntuɓi tsohon ɗanwasan tsakiyar Liverpool Georginio Wijnaldum, Arsenal na bibiyar ɗanwasan gaban Bournemouth Eli Junior Kroupi yayin da Everton ta ce ba ta da niyyar sayen ƙarin ƴanwasa a yanzu.
Mene ne bambancin falalar Umarar Ramadan da ta Mauludi?
Akwai lokutan da ake samun tururuwar masu zuwa aikin Umara daga sassa daban-daban na faɗin duniya akwai kuma lokutan da ba a fiye cika ba
'Yadda na tafi Najeriya daga Spain don neman masoyin da ya yaudari mahaifiyata'
'Yahoo Boys' na Najeriya samari ne da ke amfani da wayoyinsu da basirarsu don damfara wasu waɗanda abin ya shafa su miƙa dubban daloli.
Iran ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a Bahrain da UAE
Wannans ahfi na kawo muhimman al'amuran da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar 02/09/2026
Dalilai 8 da ke sa matasa sauya addini
A farkon makon nan ne wani matashi ya fito a wani bidiyo yana cewa ya fice daga addinin Musulunci ya koma Kirista, lamarin da ya ɗauki zafi tare da haifar da zazzafar muhawara.
Ministan Indiya mabiyin addinin Hindu da ya yabi Musulunci ya tayar da ƙura
Sa'ilin da yake jawabi a wani taro ranar Lahadi a jihar Karnataka ta ƙasar Indiya, ministan ilimi mai zurfi na ƙasar Roy Reddy ya yaba wa Musulunci, inda ya bayyana shi a matsayin "addini mai kyau."
Manyan tarihi 7 da aka kafa a kasuwar ƴan ƙwallon Turai ta 2026
Yayin da aka rufe kasuwar daren da ya gabata, ƙungiyoyi da dama sun yi sayi fitattun ƴan wasa, tare da karya wasu tsofaffin tarihin cinikayya da kuma yin wasu sayayyar da suka ɗauki hankalin masu bibiyar harkokin wasanni a duniya.
Ko kun san fa'idar sanƙo da maza ke fama da shi?
Ana kallon masu sanƙo a matsayin mutanen da suka fi basira, kuma manyan mutane da suke da ƙima, kuma irin yadda kan su ke ƙyalli zai iya taimakon wajen jan ra'ayin mata ko kuma su ceto rayuwa.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Hantsi, 06:30, 3 Satumba 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 3 Satumba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 2 Satumba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 2 Satumba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Ƴanwasan da Liverpool ta ɗauka da waɗanda suka bar ƙungiyar
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 31 ga watan Agusta zuwa 6 ga watan Satumba 2026.
Liverpool ta so Gusto, Arsenal ta ƙi sallama Zubimendi
Liverpool ta nemi aron Malo Gusto, Chelsea ta so ɗaukar Alex Scott da kuma Martin Zubimendi, yayin da ɗanwasan Manchester United Chido Obi ke son tafiya aro.
Wasu muhimman lokuta 13 da suka fi ɗaukar hankali a rayuwar Messi
Yayin da Lionel Messi ke sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasarsa ƙwallon bayan rasuwar mahaifinsa, ɓangaren wasanni na BBC ya yi waiwaye kan wasu daga cikin muhimman lokutan da suka fi daukar hankali a rayuwar ɗanwasan na Argentina a fagen tamola.
Arsenal na shawara kan Fofana, kuma ba ta cire tsammani ba kan Alvarez
Arsena na shawara kan Malick Fofana, haka kuma Gunners har yanzu tana son Julian Alvarez, Liverpool ta yi watsi da tayin fam miliyan 30 na Nottingham Forest kan Trey Nyoni.
Messi ya yi ritaya daga buga wa Argentina wasa
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Messi ya ce ya bayar da dukkan ƙarfinsa ga tawagar ƙasar, amma yanzu "ba shi da sauran abin da zai bayar".
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Ana musayar wuta tsakanin Iran da Amurka
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 01 ga watan Satumbar 2026.
Alamomin cutar mashaƙo da ake fama da ita a Kano da Katsina
A Najeriya musamman wasu jihohin arewacin ƙasar ana samun ɓarkewar cutar mashaƙo wadda ke kama yara waɗanda suka kai shekara biyar da kuma manya da suka haura shekara 60.
Jiragen yaƙi 5 na zamani da ƙasashen gabashin Afirka suka mallaka
Ƙasashe daban-daban na yankin na kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayen jiragen yaƙi da horas da matuƙa jirage da inganta tsarin sa ido da leƙen asiri da kuma bunƙasa fasahohin yaƙi domin kare kansu tare da ƙarfafa yadda za su iya tinkarar barazanar tsaro.
Khamenei ya aika wa ƙasashen Gulf saƙo: Abin da muka sani game da lafiyarsa
Jagoran Addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya yi kira ga shugabannin kasashen Musulmi, musamman na Gabas ta Tsakiya da yankin Tekun Fasha, da su haɗa kai domin tunkarar Amurka da Isra'ila.
Abubuwa biyu da za su iya tantance wanda zai lashen zaɓen Najeriya na 2027
Tsadar rayuwa, rashin tsaro, rashin aikin yi, rashin lantarki, kiwon lafiya da ilimi na cikin abubuwan da ke addabar ƴan Najeriya, amma waɗanne abubuwa ne za su fi jan hankalin masu kada ƙuri'a a zaɓen 2027?
Tupac Shakur: Yadda aka gano makasansa shekara 30 bayan kisa
Kusan shekaru talatin na ruɗani, jita-jita da hasashe iri-iri, da kuma tambayoyin da ba a samu amsarsu ba sun biyo bayan mutuwar ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan rap a tarihi, Tupac Shakur.
Dalilai huɗu da suka haifar da tashin farashin man fetur a Najeriya
A ƴan kwanakin nan, farashin man fetur ya sake tashi a sassa daban-daban na Najeriya, inda a wasu gidajen mai a Abuja, babban birnin ƙasar ake sayar da litar fetur kan naira 1,400.
Ina aka samo kalmar Takutaha kuma me ya sa ake biki a ranar?
Ana gudanar da bikin Takutaha ne a ranar bakwai daga ranar Maulidi, wato ranar da Hausawa a al'ada suke yin bikin sunan wanda aka haifa.
Wane ne ke jagorantar Najeriya idan Tinubu da Shettima ba sa nan?
Masu sukar shugaban ƙasar na cewa domin martaba sashe na 145 na kundin tsarin mulki ya kamata shugaban ƙasa idan zai je hutu ya miƙa riƙon mulki a hukumance ga mataimakinsa.
Gaske ne Opay zai dakatar da aiki a watan Satumba?
A ranar 30 zuwa 31 ga Agustan 2026, wani saƙo na bogi ya yaɗu a kafafen sada zumunta yana cewa OPay zai dakatar da harkokinsa daga ranar 1 ga watan Satumban 2026, kuma ya buƙaci kwastomomi su cire kuɗaɗensu.
Me ya sa Tinubu ba ya son a fitar da sakamakon binciken da Amurka ta yi a kansa?
A ƴan kwanakin nan ne Shugaba Tinubu ya nemi wata kotu ta hana Ma'aikatar Shari'ar Amurka (DOJ) da hukumomin FBI da DEA fitar da wasu takardunsa da ake dangantawa da zargin safarar miyagun ƙwayoyi da aka taɓa yi masa, a cewar lauyoyinsa.
Yadda Rasha ta taimaka wajen murƙushe boren sojoji a Nijar
Jakadan Rasha Viktor Voropayev ya ce gwamnatin Nijar ce ta buƙaci ɗaukin sojojin Africa Corp domin "murƙushe boren", wanda hakan ya kawo ƙarshen rade-radin da ake yi kan cewa sojojin na Rasha za su tsaya a tsakiya.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































