Mene ne bambancin falalar Umarar Ramadan da ta Mauludi?

Asalin hoton, Getty Images
Yadda ake samun tururuwar al'umar Musulmi domin gudanar da ayyukan Umara a watan Mauludu a baya-bayan nan ya sa ana tambayoyin cewar shin Umarar lokacin Mauludu Ko Ramadan wacce tafi?
Alƙaluma daga masu harkokin jigilar maniyyata sun nuna cewa a 2026 a watan Mauludu an samu ƙarin mutanen da suka halarci Umarar ta bana.
Alhajji Abdu'aziz Sabitu Muhammad Arfa Air Servie shaida wa BBC cewa ba su taba samun yawan masu zuwa aikin Umarar Mauludi ba irin ta bana, inda kamfaninsu ya buga bizar mutum akalla mutum 300 a watan Mauludi kawai, saɓanin mutum ƙasa da 100 da suka samu a watan Mauludin bara.
"Mukan yi bizar mutum 2,000 da azumi jimillar kamfanoni biyar ko shida. A baya mun ta fuskantar matsalar rashin samun biza daga hukumomin Saudiyya, amma yanzu ana samu sosai".
Ma'ida Abubakar ita ce shugabar kamfanin White Birds Travel Agency, ta ce a watan Agustan da ya yi daidai da farkon watan Rabi'il Awwal ta yi wa mutum sama da 200 biza.
"Sai da ya kai duk wanda bai sayi tikitinsa a watan Yuni ba, bai samu tafiya ba a watan Agusta.
"Jirage sun yi ƙaranci a watan Agusta daga Kano zuwa Legas zuwa Abuja da sauran wurare da jiragen da suke tafiya Saudiyya suke tashi. Abun ƙaruwa yake kullum".
Falalar Umara
Umara na daga cikin ibadun addinin musulunci da aka yarda musulmi ya yi idan yana da hali.
Ba kamar aikin Hajji ba da yake ɗaya daga cikin manyan shika-shikan addinin Musulunci biyar, Umara kawai tana zaman abin da aka so ne mutum ya yi kuma ko da sau ɗaya ne a rayuwarsa.
Amma ba ya zama laifi idan mai hali ya yi ta da yawa a rayuwarsa, hakan kan zama ƙarin falalar ubangiji da yake yi wa mawadata daga cikin bayinsa.
Umara ba ta da wani tsayayyen lokacin da aka ce a cikinsa ake yinta, misali, kamar aikin hajji da ake yi a wata na 12 cikin watannin addinin Musulunci Zul Hajj.
Ayyukan da ake yi a lokacin ibadar Umara ma sun sha banban da na ibadar aikin Hajji, akwai kuma inda suka haɗu, wani wajen a samu ƙari wani kuma a samu ragi.
Umarar Ramadana

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An samu haɗuwar bakunan da ra'ayoyin malamai kan falalar Umara a lokacin watan Ramadana, babu wani saɓani kan darajarta da falalarta.
Sheikh Halliru Maraya ɗaya ne daga fitattun malaman addinin Musulumci a Najeriya, ya kuma ce "Ya tabbata a ɗaya daga cikin hadisan da aka rawaito na aikin Hajji da Umara, cewa Shugaba Annabi Muhammad SAW ya ce "Yin Umara a cikin watan Ramadana tana daidai da yin Hajji ko kuma yin Hajji tare da ni".
Ya ƙara da cewa "duk da cewa an samu shakku daga wanda ya rawaito Hadisin kan "daidai take da Hajji kawai, ko kuma Hajji tare da Annabi Muhammad", koma dai wanne ne daga ciki malaman Musulunci sun haɗu a kan cewa yin Umarar Ramadana falalarta daidai take da ta aikin Hajji.
Amma wannan baya nufin idan mutum bai taɓa aikin Hajji na farilla ba sai ya yi Umarar Azumun Ramadana a ce ya yi daidai da wanda ya yi aikin Hajjin farilla, ko kuma shikenan ba sai ya yi aikin Hajji ba da aka ware masa lokaci a addini.
Malamin ya ce ana nufin girman ladanta da falalarta ne ya yi daidai da wacce aka yi da Annabi Muhammad, "amma ba ta sauke farali".
A cewar Sheikh Halliru Maraya shari'a ce ta bayyana lada da falalar aikin Umarar Ramadana.
Umarar Maulud
Game da falalar Umarar Mauludi da ake yi malamin ya ƙara da cewa babu wani nassi a ƙur'ani ko hadisi da ya tabbatar da falalar Umara a cikin Rabi'il Awwal.
"Ba a fayyace banbancin lada ko falalar yin Umara ba a cikin watan Mauludi, falalarta da ladanta daidai yake da ka yi Umara a cikin watan Sha'aban ko kuma Jimada Thani".
Sai dai Malamin ya ce ba laifi ba ne idan mutum ya tashi ya tafi ya yi Umarar da Mauludi domin shi ne watan da aka haifi Fiyayyen halita ka je masa ziyara ka kai wa sahabbansa.
"Amma hujja da za ta tabbatar da yin haka babu ita a addini".











