Me ya sa garkuwa da mutane ke ƙaruwa a Kano?

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Asabar, 29 ga watan Agusta ne rundunar ƴansandan Jihar Kano ta ce ta daƙile wani yunƙurin garkuwa da mutane tare da ceto Sarkin Noman Kano, Alhaji Yusif Nadabo, a Garun Mallam da ke Kano.
A cewar Kakakin Rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wasu da ake zargin ƴanbindiga ne sun mamaye garin da misalin ƙarfe 11:30 na dare, inda suka rika harbe-harbe a iska tare da yin garkuwa da Sarkin Noman Kano.
A yayin harin, an harbi mutane uku — Yusif Nasiru mai shekara 20 da Salisu Garba mai shekara 20 da Ibrahim Hassan mai shekara 20 — waɗanda dukkansu mazauna Garun Mallam ne.
Haka kuma akwai wani rahoton daban da ya nuna wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe Alhaji Garba Buba, shugaban jam'iyyar APC na mazaɓar Rantan da ke ƙaramar hukumar Bebeji a jihar ta Kano.
Sai dai kakakin rundunar ƴansandan jihar, Haruna Abdullahi Kiyawa ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a makon cewa rundunar ta kama mutum 244 da laifuka daban-daban.
Ya ce sun kama masu garkuwa da mutume 8, da ƴan fashi 28 da ɓarayin motoci 7 da dilolin ƙwaya 19 da ƴan daba 117.
Sai dai ba yanzu ba ne aka fara samun rahotannin garkuwa da mutane ba a Kano, domin lamarin ya daɗe yana ci wa mutane tuwo ƙwarya, musamman mazauna gefen jihar da ke maƙwabtaka da jihohi da suke fama da matsalolin tsaro.
Yadda lamarin ya yi ƙamari
A watan Oktoban shekarar 2025 ne wata ƙungiyar mazauna yankin ƙaramar hukumar Shanono da ke jihar Kano suka koka game da yadda ƴanbindiga ke kai musu hare-hare tare da sace mutane da dabbobinsu.
Yayin taron manema labarai, shugaban al'ummar Farin-Ruwa Alhaji Yahaya Bagobiri ya nemi gwamnatin tarayya da ta jihar su kawo musu ɗauki.
Bagobiri ya ce wasu hare-hare da ƴanfashin suka kai musu ranar Talata da Laraba sun yi sanadiyyar raunata mutane da kuma sace shanu da dama.
Haka kuma yankin Lakwaya da ke ƙaramar hukumar Gwarzo a Jihar ta Kano ta sha fama a baya, inda aka riƙa samun hare-hare da kashe mutane.
Yahaya Bagobiri ya ce garuruwan da ƴanfashin suka fi kai wa hari sun haɗa da Farin-Ruwa da Kuraku da Gorantuse da Saure da kuma Shadu.
Shanono da ke arewa maso yammacin jihar Kano, na da nisan kilomita 85 daga ƙwaryar birnin Kano, kuma ta yi maƙwabtaka da ƙananan hukumomin Kankiya da Musawa da Danja na jihar Katsina waɗanda ke fama da hare-haren ƴanfashin daji na tsawon lokaci.
Me ya janyo matsalar tsaro a Kano?

Asalin hoton, @KanoPoliceNG
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wata tattaunawa da ya yi da BBC, Dokta Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Security and Consulting Limited mai nazarin tsaro a ƙasashen yankin Sahel ya ce matsalar tsaro a jihar Kano ta fara girman da ya kamata gwamnati ta mayar da hankali domin magance ta.
Masanin tsaron ya ce duka ƙauyukan da ke da iyaka da jihohin Katsina da Kaduna na cikin barazanar hare-haren ƴanbindiga.
Dokta Kabiru Adamu ya ce akwai abubuwa kamar guda uku da suka haddasa samun matsalar ɓullar ƴanbindiga a jihar Kano.
Matsin lambar jami'an tsaro a maƙwabtan jihohi
Masanin tsaron ya ce ɗaya daga cikin matsalolin da suka haifar da matsalar tsaro a jihar Kano shi ne yadda jami'an tsaro suka matsa wa ƴanbindigar da hare-hare musamman a jihar Katsina mai makwabtaka.
''Akwai matakan tsaro masu yawa da jami'an tsaro ke ɗauka a jihar Katsina, wanda kuma babu irin hakan a jihar Kano, saboda ƙarancin matsalar a jihar, wannan ya sa ƴanbindigar suka karkata zuwa Kano, inda babu irin waɗancan matakan sosai'', in ji shi.
Sulhu da ƴanbindiga a Katsina
Wani abu da ya ƙara janyo samun hare-haren ƴanbindiga a jihar Kano shi ne yadda wasu al'umomin Katsina mai makwabtaka ke yin sulhu da ƴanbindigar domin samun zaman lafiya, a cewar Shugaban Kamfanin na Beacon Security.
Al'umomi a ƙananan jhukumomi da dama a jihar Katsina sun yi sulhu da ƴanbindiga, lamarin da ya sa ƴanbindigar suka dakatar da hare-hare a yankunan da aka yi sulhun.
"A iya ƙididdigar da muka yi akwai ƙananan hukumomi 17 a jihar Katsina da suka yi sulhu da ƴanbindiga da ke addabarsu da hare-hare'', in ji Kabiru Adamu.
''To ka ga kenan wuraren da suka kai wa hare-hare sun ragu matuƙa, kuma tun da suna riƙe da makamai, dole su nemi wasu wurare da za su riƙa kai hare-hare, tun da sulhun bai tanadi karɓe makamansu ko sauya musu tunani ba'', in ji shi.
Dama dai masana tsaro sun sha yin gargaɗi game da illolin yin sulhu da ƴanbindiga ba tare da karbe makaman da suke amfani da su ba.
Sauƙin kai hari
Kabiru Adamu ya ce a ilimin kimiyyar tsaro, akwai abubuwa guda uku da ke sa ƴanbindiga su ƙaddamar da hare-hare a wuri, na farko shi ne mai aikata laifin yana kan bakarsa na ci gaba da aikatawa, na biyu zai duba ribarsa idan ya kai, sai kuma sauƙin ƙaddamar da harin.
''To idan ka duba duka waɗannan abubuwa sun haɗe a Kano, ga ƙauyuka nan babu jami'an tsaro, sannan ga shi kuma za su samu riba idan suka kai'', in ji matsanin tsaron.
Me ya kamata hukumomi su yi?
Shugaban kamfanin mai nazarin tsaro ya ce galibi jihohin Najeriya suna da sakaci wajen ɗaukar ingantattun matakan tsaro na zamani.
''Yana da kyau gwamnati ta ɓullo da wasu hanyoyi da mazauna ƙauyuka za su samu damar sanar da jami'an tsaro idan suna cikin barazana, su kuma jami'an tsaro su gaggauta kai ɗauki'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa yana da kyau gwamnatin jihar Kano ta tashi tsaye wajen inganta harkokin tsaron jihar, ta hanyoyin zamani.
''Kano na da ƙananan hukukomi 44 da dubban ƙauyuka, to ya kamata gwamnatin jihar ta samu wani ƙauye mai nisa ta yi gwajin hanyoyin zamani na isar da saƙo, a kuma ga minti nawa zai ɗauki jami'an tsaro kafin su kai ga ƙauyen domin bayar da agaji,'' in ji shi.
An tura ƴansanda 250 bakin iyakokin Kano

Asalin hoton, Abdullahi Haruna Kiyawa
Rundunar ƴansandan Jihar Kano ta kammala horar da jami'ai 250 kan dabarun yaƙi da sarrafa makamai, inda za a tura su ƙananan hukumomin da ke kan iyakar jihar domin ƙarfafa tsaro da gaggauta kai ɗauki.
A cewar Kakakin Rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, jami'an sun shafe wata guda suna samun horo a sansanonin 9 PMF Hotoro da 52 PMF Challawa.
Kwamishinan ƴansandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce horon ya ƙunshi sarrafa makamai, dabarun yaƙi, ƴancin ɗan'Adam, amfani da ƙarfi, tattara bayanan sirri da gano abubuwan fashewa.
Ya ce: "Jami'ai 250 da suka kammala karatun a yau za a tura su zuwa ƙananan hukumomin da ke kan iyakar Jihar Kano domin ƙarfafa tsaron iyaka da inganta saurin kai ɗauki."
Kwamishinan ya kuma umarci jami'an da su kasance masu ƙwarewa da adalci, tare da mutunta haƙƙin jama'a, yana jaddada cewa "ƙarfin bindiga dole ne a kodayaushe ya kasance ƙarƙashin jagorancin doka da mutuncin ɗan ƙasa."











