Khamenei ya aika wa ƙasashen Gulf saƙo: Abin da muka sani game da lafiyarsa

Asalin hoton, EPA/Shutterstock
Jagoran Addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya yi kira ga shugabannin kasashen Musulmi, musamman na Gabas ta Tsakiya da yankin Tekun Fasha, da su haɗa kai domin tunkarar Amurka da Isra'ila. Wannan kira na kunshe ne a cikin wani sako da kamfanin dillancin labarai na Iran, IRNA, ya wallafa.
Sakon ya zo ne watanni shida bayan hare-haren Amurka da Isra'ila, da suka yi ajalin mahaifinsa, tsohon Jagoran Addinin Iran Ali Khamenei, tare da ji wa Mojtaba munanan raunuka, kamar yadda wasu majiyoyi na kusa da muƙarrabansa suka shaida wa Reuters.
A cikin sakon da aka gabatar yayin taron Makon Hadin Kan Musulunci, Khamenei ya ce shugabannin kasashen yankin dole ne su "gano hakikanin makiyansu, su fahimci shirye-shiryensa, sannan su fahimci manufofinsa," yana nufin Amurka da Isra'ila, kamar yadda IRNA ta ruwaito.
Ya kara da cewa Washington da Isra'ila ba makiyan Iran da abin da ya kira "gungun masu adawa" kawai ba ne, makiyan sauran dukkan kasashen Musulmi na yankin Yammacin Asiya da Arewacin Afirka ne, har da waɗanda ke haɗa gwiwa da su.
Wannan shi ne sako na biyu da ya fitar sako a baya-bayan nan yana jaddada muhimmancin hadin kai a cikin gida. A wani sako da aka wallafa ranar 28 ga watan Agusta, ya yi gargadi kan kalamai da za su iya haifar da rarrabuwar kawuna a cikin al'umma, kamar yadda kafafen yada labaran gwamnatin Iran suka bayyana.
Sai dai duka sanarwar da ake fitarwa da sunan Khamenei tun bayan hawansa karagar mulki an fitar da su ne a rubuce kawai. Bai fito bainar jama'a ba, sannan hukumomin Iran ba su fitar da hotunansa, sautin murya ko bidiyonsa ba tun bayan da aka naɗa shi Jagoran Addini. Wannan ya haifar da tambayoyi game da lafiyarsa da kuma irin ikon da yake da shi a zahiri wajen tafiyar da harkokin kasar.
Ko halayyarsa ga ƙasashen yankin Gulf sun sauya?
Saƙon Khamenei na zuwa ne watanni bayan ƙarin zaman ɗarɗar tsakanin Iran da wasu ƙasashen yankin na Gulf, bayan harin da Tehran ta kai wa sansanin sojin Amurka da wasu wurare a yankin lokacin da suke yaƙi.
Gabanin fara yaƙin, ƙasahsen Saudiyya da Qatar da kuma Oman sun so matsa wa Washington lamba na kada ta kai wa Iran hari. Yarima Mai Jiran Gadon Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya tabbatar wa Shugaban Iran Masoud Pezeshkian cewa ƙasarsa ba za ta bari a yi amfani da wani yankinta ko sararin samaniyarta wajen duk wani matakin soja kan Tehran ba, a cewar Reuters.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai Iran ta mayar da martani ga hare-haren Amurka da Isra'ila ta hanyar harba makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa kan ƙasashe shida mambobin Majalisar Haɗin Kan Ƙasashen Gulf, kamar yadda wani binciken Reuters ya bankaɗo.
Hare-haren ba su tsaya kan sansanonin Amurka kawai ba, har ma sun shafi filayen jiragen sama, kayan more rayuwa da cibiyoyin man fetur da kuma yankunan fararen hula.
Takunkuman da aka ƙaƙaba wa Iran sun haifar da raguwar zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin Hormuz, lamarin da ya haddasa cikas ga jigilar makamashi da kasuwanci a yankin.
Hare-haren sun jawo fushin al'uma a yankin Gulf. Firaministan Qatar ya bayyana hare-haren Iran a matsayin "cin amana", yana mai cewa hakan ya faru ne duk da tabbacin da ƙasashen Gulf suka bayar na cewa za su kasance 'yan ba-ruwana. Ministan harkokin wajen Saudiyya kuma ya ce amincewar da suke da ita ga Tehran ta "rushe", yana mai cewa ƙasarsa tana da damar ɗaukar matakin soja kan Iran.
Zaman ɗarɗar ya sake ƙaruwa ne a watan Agusta lokacin da Iran ta yi barazanar kai hari kan cibiyoyin makamashin ƙasashen Gulf idan Amurka ta sake kai mata hari.
Bayan gano wasu makamai biyu masu linzami da Abu Dhabi ta ce an harbo su daga Iran, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta dakatar da duk wata hulɗar kasuwanci da Tehran har sai baba ta gani.
Duk da haka, hanyoyin sadarwa tsakanin ɓangarorin ba su katse ba, bayan da Oman da Qatar suka ci gaba da ƙoƙarin shiga tsakanin Iran da Amurka, musamman a tattaunawar da ke da nufin kawo ƙarshen yaƙin da sake buɗe mashigin Hormuz.
Ba kamar barazanar da Iran ta yi a baya ba, sakon Khamenei ya fi karkata ga amfani da harshen haɗin kai ga ƙasashen Gulf, inda ya buƙaci shugabanninsu su mara wa Tehran baya wajen fuskantar Amurka da Isra'ila.
Sai dai sakon bai taɓo batun hare-haren da Iran ke kai wa ƙasashen Gulf ba, kuma magana kan yadda za a sake farfaɗo da dangantaka tsakaninsu. Haka kuma ya ƙunshi suka a fakaice kan ci gaba da haɗin gwiwar da wasu ƙasashen yankin ke yi da Washington.
Ta yaya Mojtaba Khamenei ya zama Jagoran Addini?
Mojtaba Khamenei ya karbi jagorancin Iran ne bayan kashe mahaifinsa a hare-haren Amurka da Isra'ila da suka fara kaiwa a ranar 28 ga wata Fabrairu.
Mojtaba ya samu raunuka a hare-haren da suka kai ɗin. Mutane uku da ke kusa da shi sun shaida wa Reuters cewa ya ji raunuka a fuska da ƙafafunsa, kuma an lalata masa fuskarsa sosai. Ko da yake kamfanin dillancin labaran ya ce ba shi da tabbas kan tabbacin wannan labari.
Hukumomin Iran ba su fitar da wani cikakken bayani game da irin raunukan da ya samu ba.
An zaɓi Mojtaba Khamenei a matsayin Jagoran Addinin Iran ne a ranar 8 ga Maris, kwanaki takwas bayan fara yaƙin, a lokacin da Iran ke fuskantar ɗaya daga cikin manyan rikice-rikicen siyasa da yaƙin soja mafi muni tun bayan juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979.
Gabanin yaƙin, Mojtaba yana aiki ne a ɓoye a matsayin babban mai taimaka wa mahaifinsa, kuma ba a cika ganinsa a bainar jama'a ba.
Sai dai ɓacewar da ya yi daga idanun al'umma tun bayan hawa mafi girman mukami a ƙasar ya haifar da ruɗani, ganin cewa Jagoran Addinin ne mai yanke hukuncin ƙarshe kan manyan batutuwan siyasa da na soji a ƙasar Iran.
Me ya sa har yanzu ba ya fitowa bainar jama'a?
Jami'an Iran sun danganta rashin bayyanar Khamenei da ci gaba da murmurewarsa daga raunin da ya samu, tare da fargabar cewa Amurka ko Isra'ila na iya sake yunƙurin kai masa hari.
Wani babban jami'in Iran ya shaida wa Reuters cewa kaɗan daga cikin jami'an gwamnati ke iya haɗuwa da shi, kuma hukumomi ba sa fitar da bayanai game da shi saboda fargabar hakan ka iya ba da haske kan mafakarsa da za su taimaka wa Amurka gano inda yake.
Reuters ta ambato wani mutum na kusa da shi yana cewa yana ƙara samun lafiya sosai, kuma har yanzu yana cikin masu yanke hukunci kan batutuwan da suka shafi ƙasar.
Sai dai hukumomin Iran ba su fitar da wani bayani a hukumance game da halin lafiyarsa ba. Haka kuma, tun bayan naɗa shi a matsayin Jagoran Addini ba a fitar da wasu sabbin hotunansa, sautin murya ko bidiyo da ke nuna shi ba, kamar yadda AFP da Reuters suka ruwaito.
Khamenei ma bai halarci jana'izar mahaifinsa ba, kuma ya kasance yana tuntuɓar al'ummar Iran ne kawai ta hanyar rubutattun saƙonni da kafafen yaɗa labarai na gwamnati ke karantawa, a cewar Reuters.
Anya kuwa shi yake mulkin Iran?
Wasu jami'an Iran da majiyoyi sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa Khamenei ne ke yanke hukunci kan manyan batutuwa, kuma yana gudanar da tarurruka akai-akai da manyan jami'an gwamnati tare da karɓar bayanai kan harkokin soja, tattalin arziki da manufofin ƙasashen waje.
Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce a ranar 10 ga Agusta ya yi wata ganawa da Khamenei ta tsawon sa'o'i bakwai, kamar yadda Reuters ta ruwaito.
Reuters ta kuma ambato wani jami'in Iran yana cewa ci gaba da aiki yadda ya kamata na cibiyoyin gwamnati da kuma daidaiton matsayinsu kan manufofin ƙasashen waje na nuna cewa Jagoran Koli har yanzu yana jagorantar ƙasar.
Sai dai babu wata hujja mai zaman kanta da aka bayyana a bainar jama'a da ke tabbatar da halartar Khamenei a waɗannan tarurruka ko kuma irin rawar da yake takawa wajen yanke shawara.
Rashin fitowarsa fili ya haddasa yawaitar jita-jita tsakanin Iraniyawa, ciki har da wasu magoya bayan gwamnati. Reuters ta ambato wani ɗan ƙungiyar Basij yana cewa jin muryar Jagoran Koli ko ganin wata shaida ta kasancewarsa zai ƙara wa mutane ƙwarin gwiwa da amincewa da shugabancin ƙasar.
Haka kuma ta nakalto wani ɗan kasuwar Iran mai goyon bayan sauye-sauye yana nuna shakku kan bayanan gwamnati, yana cewa babu wata shaida da ke nuna cewa Khamenei yana raye ko kuma yana da hannu a yanke shawarar da ake yi a ƙasar.
Ta yaya ake tafiyar da Iran duk da ba a ganin jagora?
Kamfanin dillancin labarai na Reuters, da ya dogara da majiyoyin Iran, ya ce Khamenei ya bai wa wasu manyan jami'ai iko mai faɗi na kula da harkokin yau da kullum na gwamnati, yayin da yake ci gaba da riƙe ikon ƙarshe kan manyan shawarwari na dabarun ƙasa.
A cewar majiyoyin da suka yi magana da Reuters, ƙungiyar manyan shugabannin da ke tafiyar da harkokin ƙasar ta ƙunshi manyan kwamandojin Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), da kuma Shugaba Masoud Pezeshkian, Kakakin Majalisar Dokoki Mohammad Baqer Qalibaf, da jami'an Majalisar Tsaron Ƙasa ta Koli.
Reuters ta ce tasirin Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ya ƙaru tun bayan fara yaƙin, inda ta samu babbar rawa a tsarin yanke shawara na gwamnati, wanda aka sake tsara shi domin ya fi karkata ga Majalisar Tsaron Ƙasa ta Koli.
Wannan ya yi daidai da hasashen da cibiyoyin bincike suka wallafa, ciki har da Carnegie Endowment for International Peace da Gulf International Forum, waɗanda suka nuna cewa tsarin mulkin ƙasar ya ƙara zama mai haɗin kai, tare da ƙarin tasirin Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci wajen yanke manyan shawarwari na dabarun ƙasa.
A cikin wani sharhin bincike da Cibiyar Carnegie ta wallafa, mai bincike Mohammad Ayatollahi Tabar ya rubuta cewa ba za a iya danganta jagoranci a Iran ga mutum guda ko ƙaramin rukuni kawai ba. Ya ce ana yanke shawarwari ne ta hanyar wata babbar hanyar haɗin gwiwa tsakanin cibiyoyi da shugabanni daban-daban, kuma wasu daga cikin waɗannan shawarwari suna nuna matsaya ɗaya tsakanin Jagoran Koli da manyan kwamandojin Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci.
Alex Vatanka, masanin Cibiyar Nazarin Gabas ta Tsakiya (Middle East Institute) da ke Washington, ya yi imanin cewa dogon rashin bayyanar Khamenei a fili na iya bai wa mabanbantan cibiyoyin iko a cikin tsarin mulkin Iran damar ikirarin cewa matsayinsu shi ne yake wakiltar ra'ayin Jagoran Koli.
Waɗanne ƙalubale ne ke gabansa?
Sakon Khamenei ya zo ne a lokacin da Iran ke fuskantar tasirin watanni shida na yaƙi, takunkumin Amurka, da ƙuntatawa kan fitar da man fetur ɗinta zuwa ƙasashen waje.
A wannan lokaci, tsarin siyasar ƙasar ya ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai duk da kisan tsohon Jagoran Koli da kuma wasu manyan kwamandojin soja.
Har yanzu Iran na da ikon kawo cikas ga samar da makamashi da kuma kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da na ƙawayen Washington a yankin.
Sai dai tattalin arzikin Iran na fuskantar matsin lamba mai tsanani sakamakon kuɗaɗen da yaƙi ya janyo, takunkuman tattalin arziki, da raguwar fitar da man fetur. Wannan yanayi ya haifar da faɗuwar darajar kuɗin ƙasar tare da ƙara fargabar yiwuwar sake barkewar zanga-zangar cikin gida.
A cewar majiyoyin da suka yi magana da Reuters, shugabancin Iran ya sake tsara abubuwan da ya fi mayar da hankali a kai, inda manufar ta zama kare tsarin mulki, dawo da ƙarfin hana maƙiya kai hare-hare, da kuma hana matsalolin tattalin arziki haddasa rashin zaman lafiya a cikin ƙasar.
Fatanka ya ce cimma yarjejeniya ta hakika da Washington, ko kuma yanke shawarar ci gaba da yaƙi mai tsawo da tsada, na buƙatar cikakkiyar amincewa da sahihin izini daga Khamenei ba tare da wata shakka ba.












