Tupac Shakur: Yadda aka gano makasansa shekara 30 bayan kisa

Asalin hoton, Getty Images
Kusan shekaru talatin na ruɗani, jita-jita da hasashe iri-iri, da kuma tambayoyin da ba a samu amsarsu ba sun biyo bayan mutuwar ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan rap a tarihi, Tupac Shakur.
Harin bindiga daga cikin mota da ya kashe Tupac a watan Satumban 1996 a Las Vegas ya sauya alkiblar waƙar hip-hop gaba ɗaya, tare da mayar da shi daga fitaccen tauraron rap zuwa wata alama ta dindindin a al'adun zamani.
Mutuwarsa ta kasance ɗaya daga cikin manyan asirai a duniyar nishaɗi. Tsawon shekaru, an yi hasashe da ra'ayoyi da dama game da wanda ke da alhakin kisan sa, amma ba a kama ko gurfanar da kowa ba har sai a shekarar 2023, lokacin da aka tuhumi Duane "Keffe D" Davis, tsohon jagoran wata ƙungiyar 'yan daba da hannu a kisan.
Davis, wanda yanzu yake da shekaru 63, alkalai a Las Vegas sun same shi da laifin kisan kai a ranar 31 ga Agusta, 2026.

Asalin hoton, Getty Images
Alkalan kotun sun yanke hukuncin ne bayan tattaunawa da ba ta kai sa'o'i uku ba, lamarin da ya kawo ƙarshen ɗaya daga cikin shari'o'in da suka fi tsawo a tarihin kiɗe-kiɗe a Amurka.
Shari'ar ta sake tunatar da jama'a zamanin shekarun 1990, lokacin da aka yi mummunar takaddama tsakanin mawakan rap na Gabashin Amurka da na Yammacin Amurka .
Haka kuma ta fito da irin kusancin da ke tsakanin masana'antar rap da ƙungiyoyin 'yan daba na Bloods da Crips, rikicin da ya bayyana a waƙoƙi, kafafen yaɗa labarai da abubuwan da suka faru a wancan lokaci.
Masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa an aiwatar da kisan ne domin ɗaukar fansa bayan Tupac da abokansa sun kai wa Orlando "Baby Lane" Anderson, ɗan ɗan'uwan Davis, hari sa'o'i kaɗan kafin aukuwar harbin.
Duk da cewa ba a tuhumi Davis da harbin kai tsaye ba, kotu ta amince da hujjar masu gabatar da ƙara cewa yana cikin waɗanda suka shirya wannan kisan.
A ƙarshe, bayan kusan shekaru 30 da mutuwar Tupac Shakur, hukuncin da aka yanke wa Davis ya buɗe sabon babi a tarihin ɗaya daga cikin kisan da ya fi girgiza duniyar kiɗa da al'adun zamani.
Wane ne Tupac Shakur?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tupac Shakur ya kasance, kuma mutane da dama sun yi imanin har yanzu yana nan a matsayin ɗaya daga cikin mutane masu tasiri a tarihin kiɗan hip-hop.
An haife shi a birnin New York a shekarar 1971, kuma an sanya masa suna ne bisa sunan jagoran tawaye na Kudancin Amurka, Tupac Amaru II.
Ya fitar da kundin waƙoƙinsa na farko a shekarar 1991. Har yanzu yana daga cikin mawakan da suka fi sayar da waƙoƙi a tarihin kiɗa, inda aka sayar da sama da miliyan 75 na kundin waƙoƙinsa a faɗin duniya.
Daga cikin fitattun ayyukansa akwai waƙar "Ghetto Gospel", wadda aka fitar bayan rasuwarsa a shekarar 2004.
A shekarar 2017, sunan Tupac ya shiga kundin tarihi na Rock and Roll Hall of Fame, wata babbar karramawa da ake yi wa fitattun mawaka da suka taka muhimmiyar rawa a tarihin kiɗa.
Baya ga waƙa, ya kuma yi fice a harkar fim. Ya fito a fina-finai kamar "Juice", "Poetic Justice", "Above the Rim", "Gridlock'd", da "Gang Related."
Mahaifiyarsa, Afeni Shakur, ita ce ta raine shi. Afeni ta kasance mai fafutukar kare haƙƙin baƙar fata kuma mamba a ƙungiyar Black Panther Party, wadda ta yi suna wajen gwagwarmayar neman daidaito da adalci ga baƙar fata a Amurka.
Tupac da kansa ya kasance mai bayyana ra'ayoyinsa a sarari ta hanyar waƙoƙinsa da jawabansa game da matsalolin zamantakewa kamar wariyar launin fata, talauci, da cin zarafin da 'yan sanda ke yi.
Tasirinsa a duniyar hip-hop ya samu yabo daga mawaƙa da dama. Daya daga cikin waɗanda suka fi bayyana hakan shi ne Kendrick Lamar, wanda ya sha cewa Tupac na daga cikin mutanen da suka yi tasiri a kansa.
Shahararren mawakin rap 50 Cent ma ya taɓa yin yabo ga Tupac.
"Duk wani mawaƙin rap da ya taso a shekarun 1990 yana bin Tupac wani bashi na gudunmawa da tasiri."
Yadda aka kashe Tupac

Asalin hoton, Getty Images
Tupac yana da shekara 25 kacal lokacin da aka harbe shi har sau huɗu a wani titi a Las Vegas a ranar 7 ga Satumba, 1996.
'Yan sanda sun ce kafin harbin, ya shiga wata arangama a wani gidan caca.
Bisa ga rahotannin 'yan sanda, Tupac yana cikin mota ƙirar BMW lokacin da lamarin ya faru.
A daidai wannan lokacin ne wata farar motar Cadillac ta ƙaraso kusa da motar, sannan wani daga ciki ya buɗe wuta.
An garzaya da Tupac asibiti inda aka saka shi a sashen kula da marasa lafiya masu matsanancin hali, amma ya rasu bayan kwanaki shida.
Binciken kisan Tupac ya shafe shekaru da dama yana gudana. Watakila mafi muhimmancin shaidan da har yanzu yake raye a wannan shari'a shi ne Marion "Suge" Knight, wani shugaban kamfanin kiɗa wanda yake tare da Tupac a cikin motar lokacin da aka harbe shi.
Sai dai bai taɓa ba da cikakken haɗin kai ga masu bincike game da abin da ya gani a wannan dare ba.

Asalin hoton, Getty Images
A watan Satumban 2023, 'yan sandan Las Vegas sun tuhumi Duane Davis da hannu a kisan mawaƙin.
'Yan sanda sun bayyana Davis a matsayin "jagora kuma babban mai yanke shawara" na ƙungiyar 'yan daba ta Southside Compton Crips.
Davis ya sha faɗa, har cikin tarihin rayuwarsa da ya rubuta, cewa yana cikin motar da aka harbi Tupac daga cikinta.
Masu gabatar da ƙara sun ce Orlando Anderson, marigayi ɗan ɗan'uwan Davis, ya yi faɗa da Tupac a gidan caca kafin harbin, kuma yana cikin wannan motar ƙirar Cadillac lokacin da aka kai harin.
Tun daga lokacin, Anderson da sauran mutum biyu da suke cikin motar, Terrence Brown da DeAndre Smith, duk sun rasu.
Masu gabatar da ƙara sun yi iƙirarin a shari'ar, wadda ake sa ran za ta ɗauki makonni da dama, cewa Davis ne ya bayar da umarnin aiwatar da kisan.
Idan aka same shi da laifi, zai iya fuskantar hukuncin ɗaurin rai da rai ba tare da damar neman afuwa ko sakin sharadi ba.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai tun bayan kama shi a shekarar 2023, Davis ya janye wasu daga cikin maganganunsa na baya, kuma ya musanta cewa yana da hannu a mutuwar Tupac.
"Ba ni da laifi. Ban kashe kowa ba. Ban taɓa kashe kowa ba. Ba su da wata hujja a kaina," in ji shi a wata hira da ya yi daga kurkuku da ABC News a watan Maris na 2025.
Ba kasafai ake sa ran kotu a Las Vegas za ta iya tabbatar da wanda ya harbi Tupac kai tsaye ba.
Sai dai wani masanin shari'a, Sean Kent, ya shaida wa BBC cewa masu gabatar da ƙara za su yi ƙoƙarin gabatar da tsohon jagoran ƙungiyar 'yan daba a matsayin wanda ya tsara kisan daga baya.
"Masu gabatar da ƙara za su kafa hujjar cewa ko da Davis bai ja kunamar bindigar da kansa ba, har yanzu yana da alhakin kisan, domin da ba don sa hannunsa a lamarin ba, da harbin bai faru ba," in ji Sean Kent.
Wannan shi ne ginshiƙin hujjar masu gabatar da ƙara, wato cewa Davis ne ya shirya ko ya jagoranci aiwatar da kisan, ko da kuwa ba shi ne mutum wanda ya harbi Tupac kai tsaye ba.
A ƙarƙashin dokokin jihar Nevada, mutum na iya fuskantar hukuncin kisan kai idan ya taka muhimmiyar rawa wajen tsarawa, umarta ko taimakawa wajen aikata laifin.











