Sojojin Yemen sun kai wa Houthi hari tare da lalata jiragen ruwansu marasa matuƙi

Asalin hoton, Getty Images
Sojojin Yemen sun ce sun kai hare-haren jiragen sama marasa matuƙa kan sansanonin mayaƙan Houthi a yankuna da dama, tare da kai farmaki kan maɓoyarsu da ke yankin Baqim a arewacin lardin Saada.
A lokaci guda kuma, rundunar ruwan Yemen ta sanar da cewa ta lalata kwale-kwale huɗu marasa matuƙa na ƴan Houthi kusa da tsibiran Hanish da Dhaqr da ke Tekun Bahar Maliya.
















